Khalid Idris Doya" />

Za Mu Yi Zaben Maye Gurbi Ne Idan Majalisar Dokoki Ta Bukaci Hakan, Inji INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta gudanar da zaben maye gurbin da ake da su a majisar Wakilai da na Dattawa ne kadai indan suka samu umurni daga majalisar dokoki kan bukatar hakan a rubuce.
Shugaban hukumar INEC ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu shi ne ya shaida wa ‘yan jarida hakan a lokacin da ke tattaunawa da su a Legas.
Farfesa Yakubu ya ce, hukumar za ta gudanar da zaben cikewa ko maye gurbin kujeru har guda biyar, amma har yanzu tana jiran majalisar dokokin kasa kan bukatar hakan.
Shugaban INEC ya ce dokan kasa ta bai wa hukumarsu damar gudanar da zabe amma dole ne sai majalisar dokokin ta tarayyar da na jahohi sun sanar musu da bayanin yin zaben maye gurbin wadanda suke bukatar mayewa.
Da yake bayani dangane da zaben jihar Ekiti kuma, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce hukumar tana kan aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar zaben.
Babban kotun tarayya da ke da matsuguni a Jabi a cikin babban birni tarayyar kasa (FCT), ta yanke wa wani ma’aikacin a ofishin Auditor-General na kasa (AuGF), James Ayodele Lebi, daurin shekaru biyu a gidan wakafi a sakamakon kamasa da laifin yin amfani da takardar bogi na cibiyar Akantoci ta Nijeriya (ICAN) domin samun karin girma a wajen aikinsu.
Alkalin kotun, mai shari’a Justice Y. Halilu ya kuma ce mai laifin zai bayar da naira N100,000 kana zai shafe wa’adin da aka yanke masan ne a gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa.
Hukuncin na zuwa ne a sakamakon gurfanar da shi kan wannan zargin da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa hade da dangogin da suka shafi wannan laifuka wato (ICPC) suka shigar da ma’aikacin a gaban kotun.
Tun da fari ICPC ta shaida wa kotun cewar wanda suke zargin ‘James Ayodele Lebi’ ya je ofishin Daraktan gudanarwa na ofishin AuGF, dauke da takardar bogi na ICAN inda ya bukacesa da ya daukaka masa dajarar mukaminsa zuwa babban jami’in a ofishin bin dididdigi da binciken ta kasa.
Hukumar ta ICPC ta shaida wa kotun cewar aikata wannan laifin ya saba wa sashi na 25 (1) da ke cikin kundin laifuka da hukucninsa na hukumar yaki da cin hanci da rashawa hade da dangogin hakan na Act, 2000.
Alkalin kotun Justice Y. Halilu a cikin hukuncinsa ya bayyana cewar mai laifin ya cancanci hukuncin da aka yake masa domin hakan ya zama hukunci a gareshi, hade da zama izina ga masu aikata irin wannan dabi’ar.
Alkalin ya kuma shawarci gwamnatin tarayya ta kara sanya ido domin tabbatar da wadanda suke gabatar da takardun bogi an dakile shirinsu.

Exit mobile version