Za A Yi Musanye Tsakanin Ronaldo Da De Gea

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tanason yin musanye da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United inda takeson ta bada dan wasanta Ronaldo ta karbi mai tsaron ragar Manchester United, Dabid De Gea.

Real Madrid dai ta dade tana zawarcin mai tsaron ragar inda a shekarar 2015 ta kusa siyan dan wasan kafin kuma a samu matsala wajen tura takardun mai tsaron ragar zuwa hukumar kwallon kafa ta duniya akan lokaci inda a karshe cinikin ya rushe.

Sakamakon garanbawul da kungiyar take shirinyi a kakar wasa mai zuwa kungiyar ta shirya siyan sababbin yan wasa kuma kwararru yayinda kuma har ila yau ta shirya rabuwa da wasu daga cikin yan wasan da take dasu a yanzu.

Sai dai babu lallai kungiyar Manchester United ta amince da wannan bukata ta Real Madrid domin a makon daya gabata mai koyar da yan wasan kungiyar, Jose Mourinho ya bayyana mai tsaron ragar kungiyar a matsayin wanda babu kamarsa kuma yace baya tunanin kungiyar zata sake siyan Ronaldo.

Cristiano Ronaldo dai ya zura kwallaye 426 cikin wasanni 420 daya buga a kungiyar a dukkanin wasannin tun daga shekara ta 2009 daya koma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United lokacin tsohon mai koyarwa Sir Aled Ferguson akan kudi fam miliyan 80 daidai.

Ronaldo da Dabid De Gea dai suna amfani da wakili daya ne wato Jorge Mendes sai dai a wannan makon De Gea yake bayyana cewa yana cikin farin ciki a kungiyarsa.

Exit mobile version