Za A Yi Wa Ɗan Majalisar Ƙaramar Hukumar Tarauni Kiranye

Daga Rabi’u Muhammad Abu Hidaya

Al’ummar ƙaramar hukumar Tarauni cikin jihar Kano sun shirya tsaf domin yi wa ɗan majalisa mai wakiltarsu a garin Abuja, Honarabul Nasiru Baballe Ila kiranye.A tattaunawarmu da wasu daga ciki dattawa da matasan ƙaramar hukumar sun ce babu wani abin a zo a gani da wakilin nasu ya tsinana tun ɗarewarsa wannan kujera tsawon shekaru shida(6), idan aka yi la’akari da takwarorinsa na wasu ƙananan hukumomin jihar masu wakilci a Abuja, don haka ba su ga dacewarsa a wannan kujera ba.

Wasu daga cikin al’ummar wannan yanki sun nuna cewa sun yi maraba da wannan kiranye da za a yi wa wakilin nasu domin hakan kawai shi ne abin da zai sa sabon wakilin da za su aika ya yi musu aikin da ake buƙata, da suke bayyana dalilansu na yin wannan kiranye sun ce,“akwai ayyuka da ƙudirori da dama da yakamata a ce wakilin namu ya kai tun ɗarewarsa wannan kujera, amma bai yi ba, hasalima akwai guraben aiki na ma’aikatun da suke ƙaramar hukumar wanda yakamata a ce ‘yan asalin ƙaramar hukumar Taraunin ne suka samu aiki a ciki, a maimaikon haka ma sai wasu ‘yan ƙaramar hukumar ne suka samu tagomashin cin moriyar aiki a waɗannan wurare, saboda halin ko-in-kulan da  yake da shi ga al’ummarsa, a maimaikon farilla sai ya  ɓ uge da nafila.

Binciken mu ya gano yanzu haka mutane kimanin dubu shida sun sanya hannu a takarda da kwamitin kiranyen suka raba, mun kuma tattauna da wasu ɗaiɗaiku a cikin jama’ar ƙaramar hukumar waɗanda suka sanya hannu a wannan takarda me yasa suke son dawo da wakilin nasu ga abin da suka ce.

“Ya gaza game da hakkin da muka ɗora masa ya kuma sanya hijabi a tsakaninmu da shi, baya zuwa wurinmu tun lokacin da muka zabe shi ba mu kara sanya shi a idanunmu ba, ga shi kuma kullum matsaloli suna kara yi wa yankin namu yawa kwanakin baya mu da iyalanmu mun fama da zazzabin cizon sauro da wasu cututtuka waɗanda muke buƙatar ɗaukinsa na rabon magunguna, amma babu wanda yake saurara sai wasu mutane ƙalilan waɗanda da ba sa tare damu”.

Lamarin ‘yan siyasar kasar nan dai kullum sake ta ɓ arbarewa yake, hukumar za ɓ e ta ƙasa ce dai ta bayyana wannan ƙudiri na kiranye a kwanakin baya don dawo da wakilan da su ka gaza ayyukansu a yayin wakilcinsu a majalisa, kuma ga dukkan alamu lamarin zai samu tagomashi a cikin al’umma don bayan wannan ɗan majalisa na ƙaramar hukumar Tarauni Honarabul Nasiru Baballe Ila akwai wasu wakilan da ake yunƙurin yi musu wannan kiranye.

Wakilinmu ya yi ƙoarin jin ta bakin ɗan majalisar kan wannan lamari abun ya ci tura.

 

 

 

Exit mobile version