Abdullahi Muhammad Sheka" />

Zabar Abba Kabir Yusuf Shi Ne Tabbatar Dimokradiyya Ta Kankama A Jihar Kano -Falaki

An bayyana zaben da Kanawa suka yiwa Injiniya Abba Kabiru Yusif da cewa shi ne ya tabbatar da Dimokradiyya ta zauna da gindinta a Jihar Kano, wannan Bayani ya fito daga Bakin shugaban Muryar Malaman Kwankwasiyya na Kasa Sheikh Musa Falaki Tsakuwa alokacin da yake zantawa da Jaridar Leadership ta wayar salula jinm kadan da fitowar sa daga Shabbakin ma’aiki a Madina. Sheikh Musa Falaki Tsakuwa ya bayyana cewa zabar Abba Kabir Yusfi shi ne zai dawo da cigaban ayyukan da jagoranmu ya dora Jihar Kano akai duk da wasu makiya cigaban Jihar Kano sun yiwa ire iren wadancan ayyukan rikon sakainar kashi.
Sheikh Musa Falaki wanda shi ne shugaban muryar malaman Kwankwasiyya na kasa ya ci gaba da cewa an kusa shan al’ummar Kano basulla da sun yi gangacin sake zabar wadancan da suka kware da daure al’umma igiyar igiyar zato, kuma ai ko ba komai irin abin kuyar da aka jefa Kanawa a ciki kan wani faifan bidoyo da ya fita bakaramar rage darajar Kanawa wa ya yi ba kwarai da gaske. Don haka sai Musa Falaki ya jinjinawa Kanawa bisa wannan kyakkyawar dabara, sannan kuma ya bukaci al’umma a ci gaba da addu’a kar a tsaya har sai mun ga abin da muka zaba ya tabbata.
Da aka tambayeshi ko me yake ganin kan sakamakon zaben wanda Hukumar zabe tace bai kammla ba, Sheikh Musa Falaki cewa ya yi ai Allah ke bada mulki ga wanda yaso a lokacin da yaso, kuma tarihin jihar Kano ai maimaita kansa yake ba’ kwacen zabe a Kano ba, a shekara ta 2003 Gwamna Kwankwaso awannan lokacin shi ya fara taya Shekarau murna, sannan kuma shima Shekara ta 2011 haka ya hakura ya sake mikawa Kwankwaso mulki, kuma shi na yanzu a zatonsa dawwama zai yi, ya hakura ya karbi kaddara Allah Abba Kabir ya baiwa a wannan karon.
Hakazalika muna tabbatarwa da jama’a cewar ko sau nawa za’a sake zabe da yardar Allah Abba Kabir Yusif shi ne zai lashe, ya kamata jama’a su hankalta duk irin taron dangin da aka yiwa Kwankwaso kuma gashi ba shida mulki a hannun sa amma sai Allah ya shiga cikin al’amarinsa ya rangade wancan taron tsintsya ba sharar, sabaoda haka jama’a su kwantar da hankali Allah ya kaimu ranar 23 ga watan da muke ciki ai rana bata karya sai dai uwar diyya ta ji kunya, inji Musa Falaki.

Exit mobile version