Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya amince zai bayyana a gaban majalisar kasa domin yi wa ‘yan Nijeriya jawabi kan karuwar matsalar tsaro a fadin kasar, musamman ma mummunan harin kisan kiyashin da a ka yi wa wasu manoma a garin Zabarmari da ke Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno ranar Asabar da ta gabata.
Wannan bayanin ya fito ne ta bakin shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, wanda ya jagoranci tawagar majalisar domin ganawa da Shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja jiya Laraba.
Da ya ke ganawa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya tabbatar da cewar, Buharin zai zo gaban majalisar, domin amsa gayyatar da majalisar ta ma sa kan matsalolin tsaro da suke kara kamari a fadin kasar, domin yi wa ‘yan Nijariya bayani dalla-dalla.
Sai dai ya ce, har zuwa yanzu dai ba a ware wata rana takamaimai da Buharin zai bayyana a gaban majalisar ba, illa dai ya shaida cewar ya amince zai amsa sammacin, amma bai bayyana rana ba, illa dai ya ce nan kusa kadan zai zo.
Mista Femi ya kuma shaida cewar zai sanar da ‘yan jarida duk ranar da a ka ware domin bayyanar Buharin, Hon. Gbajabiamila ya kara da cewa: “Shi kwararre ne kan demokradiyya, masaninta ne. don haka zai zo domin yi wa majalisa bayani nan gaa kadan,”
Shugaban majalisar ya nuna cewa tabbas Buhari ya damu matuka da halin da kasar nan take ciki, inda ya ce yana sauraron koke-koken jama’a.
Kana, ya kuma bada tabbacin cewa Buhari ya maida hankali da himmatuwa wajen kare rayuka da dukiyar jama’an Nijeriya.
Shugaban majalisar na dattawan ya bayyana cewar dalilinsu na sammacin Buhari da ya gurfana a gabansu shine don ya zo ya yi magana da al’umman kasa kai tsaye wadanda suka zabeshi kan wannan kujerar domin ganin yadda za a yi a shawo kan matsalar tsaro da ya addabi kasar.