Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana cewa mayakan Boko Haram suna kashe jama’ar jihar a duk lokacin da suka nuna wa sojojin Nijeriya inda suke.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne ta hanyar kakakin sa, Malam Isa Gusau, martani dangane da zarge-zargen da wasu ke yi cewa sojoji ba su samun hadin kan jama’ar jihar wajen ba su cikakken bayanan sirri kan mayakan Boko Haram.
A wani bayanin da ya tura a shafin sa na ‘Tweeter’, Isa Gusau ya yi nuni da yadda Boko Haram suka bayar da dalilin da yasa suka kashe manoma a Zabarmari saboda bayanan sirrin su da mutanen garin ke bai wa sojoji.
“Wannan daya ne daga cikin sakamakon da ke biyo bayan hadin kan jama’ar jihar Borno ke bai wa jami’an tsaro tsawon lokaci. Mutane da dama ne suka rasa rayukan su, a duk lokacin da suka tsegunta wa sojoji bayanan sirrin mayakan, kuma har yanzu ba su dena ba. Kuma wasu da dama su kan yi kokarin taimakon sojoji zuwa fagen fama kuma a kashe, kuma duk da hakan basu bari ba. Yanzu kuma sai mu kara jin wani maras ta ido ya bude baki ya zargi jama’ar Borno.”
A ranar Asabar da ta gabata Boko Haram su ka yi wa manoman shinkafa da dama kisan gilla a kauyen Zabarmari, da ke karamar hukumar Jere a jihar.
Da ya ke daukar nauyin wannan aika-aikar kisan gillar, kwamandan mayakan, Abubakar Shekau ya ce sun aiwatar da kai harin ga manoman sakamakon yadda suka kama daya mamban su tare da mika shi ga sojojin Nijeriya.