Idris Aliyu Daudawa" />

Zabe: Abin Da Ya Sa Osinbajo Ya Fadi A Mazabarsa —Mai Bashi Shawara

Mai ba mataimakin Shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya bayyana cewar mnataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fadia a mazabar shi wadda b a Bictoria Garden City, Legas, saboda ya kasance ya taka laifin wasu ne, ga kuma shi al’amarin hadin kai saboda a kaskanta wani, da kuma kabilanci.
Bayan ma ya ci zabe a rumfar da shi mataimakin Shugaban kasa yake jefa kuri’a, baya ga shi dantakarar Shugaban kasa a jam’yyar PDP Atiku Abubakar ya ci a rumfar shi Osinbanjo, bugu da kari kuma ya samu nasara gaba daya a karamar Hukumar Eti Osa inda unguwar BGC ta ke.
Ojud shine wanda ya raka Osinbajo a yawancin yakin neman zaben da yakan je,wanda kuma ya hada da ‘TraderMoni’ wajen rarraba su kudade, ya bayyana cewar a wata kasida mai suna “Yakin da Osinbanjo ya kasa yin nasara”.
Ya dai rubuta kamar haka, “Cikin watanni biyu ya ziyarcin BGC fiye da goma sha biyar .
“ Taron unguwa nan ga na cikin dakin hutawa, kai har ma idan yana tafiya a kasa, ya gana da kwararru, da kuma wasu kungiyoyi, kamar ma dai yadda yake taron mutane masu bin addinin kirista.
“Amma kuma sai ga shi zabe ya zo sun juya ma shi baya wannan bai dace ba ai, saboda ya kasa rumfar mazabar shi.
“Na samu kiraye- kirayen jama’a masu yawa da kuma sakonni ana tambayar ko minene ya faru? wannan amsa ba wata mai wuya bace, saboda kuwa wani aiki ne na, an samu wani al’amarine wanda ya shafi kabilanci da kuma wasu manyan mutane wadanda, suke ganin wasu tsare -tsaren gwamnatin su basu yi masu dadi ba, ga shi kuma yana zama cikin irin mutanen da basu jin dadin mulkin su.
“ Kamar lokacin da muike wadannan tarurrukan, na fara tunanin irin abin da ya faru, zai iya kasancewa, nai kuma yi ma abokai ne magana, cewar shi al’amarin zuwa BGC wani bata lokaci ne, duk kuwa da yake an yi magana akan zabe ne, saboda na ga shi al’amarin haka ne, wato yadda takun nasu.”
Mataimakin akan harkokin siyasar ya kara bayyana cewar su mazauna Bictoria garden city, sun fada ma shi mataimakin Shugaban kasar kukun sun a yadda ake samu ambaliyar ruwa , lokacin da suke tarurrukan nasu,amma kuma sai kasa share masu hawaye, da kuma gina masu filin wasa. Shi yasa suma suka saka mashi da yadda ya yi masu.
Tsohon dan majalisar dattawan ya kara bayyana cewar wasu daga cikin mutanen, sun ce wadanda suka shigo da kaya, sun shiga cikin wani hali saboda yadda gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hana shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
Ya kara bayanin cewar wasu daga cikin su har ma bakar magana suka fada ma shi mataimakin Shugaban kasar suka yi, amma sai ya nuna shi bai damu ba, maimakon haka ma sai kawai ya ci gaba da yakin neman zaben shi.
Ojudub ya ci gaba da bayanin cewar da akwai “ Akwai ma wasu lokuttan d wasu wadanda aka taron da su, abin yak an dame su, saboda koda yaushe hakanan yake zuwa babu ko wwani alkhairin da ayake yi masu. Dama ai an ce duniya susar Jaki ce, ka Sosa mani nawa jikin nima in sosa maka naka.
“Wannan kuma ya kamata ace taro ne na masu hali, koda naji hakan, abin ya bani mamaki, saboda kuwa wasu sunce tun daga lokacin da aka zabe shi, sun sa ran zai yi masu wani dan karamin filin wasa, yayin da wasu kuma sun sa ran zai taimaka masu dangane da matsalar malalar ruwa. Wani ya yi maganar cewar shi da Buhari ya kamata aga laifin su, saboda ta haka ne yayi asarar dan shi na farko,wanda ya mutu lokacin da matar shi mai ciki ta tafi wurin da ruwa ya malala a cikinn gidan sh.
“ Wani ya nuna rashin jin dadin shi saboda wasu mutane wadanda suke ajiye motocinsu a bayan gidamn shi, sai kuma wani wanda shi cewa ya yi, karya ce aka yi ma shi akan gadar Neja ta biyu, wadda aka fara yin aikin nata tuni. Duk wani kokarin da aka yi domin a samu ganawa da shi, saboda su, amma sai ga shi hakan bata samu ba, haka aka yita yi, har ma wani lokaci ma ana ganin ai watakila ya canza al’amarin.”
Har ila yau Ojudu ya kara jaddada cewar shi mataimakiin Shugaban kasar dan asalin jihar Ogun ne, amma kuma duk rayuwar shi ya zauna Legas ne, ya dace ace ya canza rumfar zaben shi, amma kuma shi ya fi son ya ci gaba da yin zaben a Bictoria Garden City.
Ya kara yin bayanin cewar Osinbajo ya dace ace ya yi rajista ne da kuma jefa kuri’a Somolu, Legas inda ya yi makaranta, inda kuma har yanzu mahaifiyar shi take zama, amma kuma sai ya ga yafi dacewa da ya jefa kuri’ar ta shi BGC saboda shi yana ganin su wadanda suke zama a wurin za su jefa ma shi kuri’a.
Tsohon dan majalisar ya rubuta cewar “ Gaskiya ne Osinbanjo ya fadi zaben shi a bawai mazabar shi bace, wannan kuma haka ne, yana iya zuwa ya sa kuri’a Ikenne, saboda can garin sun a asali, can ne kuma jama’ar shi suke son shi.
“ Ya kamata a ce ya shiga layi ya samu yin zabe a Somolu wanda wani wuri ne a Legas inda aka haife shi, ya kuma girma a can.inda kuma mahaifiyar shi take zama, ana kuma matukar son shi. Ko kuma yana iya yanke shawara ya jefa kuri’ar ita Akoka garin da yake kusa da jami’ar Legas, inda can ne ya koyar shekaru masu yawa, saboda ana sa ran a can ma zai fi samun farin jinin mutane mazauna wurin, saboda ko shakka babu zai samu babban rinjaye saboda mutumin sune sun kuma san shi. Amma shi kuma Osinbanjo mutum ne wanda yake kaucewa matsala ta haka zai iya dan zama a wurin har sai ya kai ga samun ko kuma ganin abinda bai dace ba.

Exit mobile version