Umar A Hunkuyi" />

Zabe: An Ci Gaba Da Hada-hada A Maiduguri

An ci gaba da gudanar da hada-hada kamar yanda aka saba a garin Maiduguri, bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar Asabar.
Majiyarmu ta ruwaito cewa, harkokin kasuwanci sun ci gaba, an kuma bude shagunan da aka rufe su a ranar ta Asabar, domin zaben, duk an bude su a jiya.
Motoci da masu baburan haya masu taya uku duk sun ci gaba da karakaina bayan dage dokar hana zirga-zirgan.
A kasuwar Gomboru, harkokin kasuwanci sun ci gaba kamar yanda aka saba, ‘yan kasuwa sun bude shagunan na su, masu saye kuma sun cika kasuwan.
Yusuf Hassan, mai siyar da abin wuya na mata cewa yayi, yana sa ran samun ciniki mai yawa duba da yanda kasuwan ta cika da masu ciniki.
Hassan ya yi nuni da cewa, yanda aka gudanar da zaben lami lafiya musamman a Jihar ne ya ba su daman bude kasuwan na su ba tare da wata fargaba ba.
Lydia Audu, mazaunar garin ta ce, ta tafi kasuwan ne domin siyan kayan miya da ganyayyakin da za ta dafa ma iyalanta abinci.

Exit mobile version