Mukaddashin sufeto-janar na ‘yan sanda Nijeriya, Muhammad Adamu; ya ce rundunar ta na nan yadda aka santa, wato wacce bata goyon bayan ko wace jam’iyyar siyasa, kuma ba zata goyi bayan wata jam’iyya ba a zabukkan da ake shirin fara gudanarwa daga gobe Asabar.
Sufeton ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da tawagar masu sanya idanu akan zabukka ta duniya ta ziyarci shi a ofishin shi dake hedikwatar ‘yan sanda dake birnin Abuja, a yau Juma’a, tawagar ta kunshi wasu kungiyoyi biyu, “National Democratic Institute” (NDI) da kuma “International Republican Institute” (IRI).
Babban sufeton ya tabbatar da cewa rundunar su ta gama shiryawa tsaf don tabbatar da tsaro a lokacin zabe da ma bayan zaben, musamman ma dai a runfunan zabe, sannan rundunar za ta hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da samun nasarar tabbatar da tsaro a lokutan zaben.
Sannan ya bayyana cewa rundunar ba zata kyale wani yayi aikin sanya ido a rumfar zabe ba, muddin bashi da katin shaidar sanya idanun, inda ya ce duk wanda aka samu bashi da katin shaidar sanya idanu za a hukunta shi a matsayin wanda yazo tayar da hankula a rumfar zaben.
Adamu ya bayyana cewa jami’ansu sun samu horaswa ta musamman, wacce za ta taimaka musu wajen gudanar da ayyukan samar da tsaro a lokutan zaben, cikin ayyukan da jami’an zasu yi harda samar da tsaro ga malaman zabe, da masu sanya idanu da ma masu kada kuri’a.