Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Zabe: El-Rufai Ya Kada Kuri’ar Sa Bayan Shafe Sa’o’i Akan Layi

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya shafe wasu awanni yana bin layi kafin ya samu ya kada kuri’ar da a zaben shugaban kada da ‘yan majalisu da ake gabatar was a yau Asabar.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kada kuri’ar sa ya ce ‘lokacin da na isa filin zaben, na’urar tantancewar bata aiki, saboda haka sai da muka yi jiran awa biyu kafin a gwara ta fara aiki.
Gwamnan ya bayyana jinjina wa al’ummar jihar bisa hakurin da suka yi, suka fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri’ar su duk da dage zaben da akayi a satin da ya gabata, jama’ar wurin nan sunyi hakuri, sun jira duk da na’urar tantancewar ta sami matsala, sai ma wash da su dinga karuwa, El-Rufai ya roki hukumar zabe ta kara lokacin zabe sakamakon tsaikon da aka fuskanta.
Exit mobile version