Ammar Muhammad" />

Zabe: INEC Ta Samarwa Da Masu Hidimtawa Kasa Katifu

NYSC

A shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da za a gabatar bayan dagewa na mako guda da aka yi, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, a wannan karon ta samarwa da masu hidimtawa kasa wato NYSC wadanda za su yi aikin zaben na wucin gadi da Katifu domin saukaka musu wurin kwana a wuraren da aka kai su domin yin aikin zaben.

Masu hidimtawa kasar wanda za su yi aiki a jihar Adamawa sune suka samu wannan tagomashin, kamar yadda Kodinetan NYSC din na jihar, Malam Abubakar Mohammed, ya bayyanawa manema labarai hakan a yau Juma’a a garin Yola.

 

Abubakar ya ce; wadannan Katifu ma’aikatan NYSC din za su aikawa masu hidimtawa kasar a duk inda aka kai su a fadin jihar. Ya ce; Katifun, an kawo su sakamakon yunkurin da shugaban NYSC din ya yi, wato Manjo Janar Kazaure dangane da walwalar ‘yan NYSC din.

A makon da ya wuce, wanda aka dage zaben, rahotanni sun nuna yadda masu hidimtawa kasar suka rika kwana akan tabarmi da kuma kasa sakamakon rashin inda za a kwana. 

Exit mobile version