Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Zabe: Mun Yi Aiki Bisa Tanadin Doka – Rundunar Sojin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya  ta bayyana cewa ayyukan da suka gudanar a zaben da aka kammala na shugaban kasa da yan majalisu sun kasance cikin ka’idar da doka ta tanada, rundunaar ta bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin da yake magana akan zargin da ake yi na hada kai da ‘yan siyasa, tursasawa da kuma harbi masu jefa kuri’a a wasu yankuna a fadin kasar a lokacin zaben, ya ce sojoji da aka tura gudanar da tsaro a harkokin zabe sun yi aiki cikin kwarewa.
A cewar kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, ya bayyana cewa; mun yi aiki bisa ka’ida, doka, ka’idojin aiwatarwa da aiki, akwai zarge-zarge da dama game da hada kai da yan siyasa, cin zarafin masu zaben da hada kai da jama’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a lokacin zabe.Ma’aikatan INEC a wasu jihohin, ciki har da Rivers, Legas da Delta, sun zargi sojojin da  tsoma baki a harkokin zaben. Sojoji sun yi harbe-harben da suka haifar da mutuwar mutane da dama, da kuma wasu ayyukan rashin adalci da ake zargin an yi a wasu jihohi a lokacin zaben.
Amma, Musa ya shaidawa manema labarai cewa sojojin sun nuna matsayar su kafin zaben, a lokacin zaben da kuma bayan zaben. Ya kara da cewa masu lura da zabe sun yaba wa sojojin dangane da irin rawar da suka taka, yayin da ake gudanar da zaben
Exit mobile version