Zabe : Rundunar ‘Yan Sanda Sun Shirya Tsaf, inji DIG Baraya

Mataimakin shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa mai wakiltar yankin arewa maso yammacin wannan kasa DIG Aminchi Sama’ila Baraya ya sha alwashin ladabtarda duk wani dansanda da aka samu yana yunkurin tallafawa magudi ko almundahana a ya yin zabe mai zuwa.
DIG Baraya ya yi wannan furuci ne a jiya lokacin da ya kawo ziyarar ganawa da jami’an ‘yansanda da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin zabe a jihar wadda aka gabatar a hedkwatar ‘yansanda dake birnin Dutse.
Shugaban ‘yansanda ya kuma ayyana lambobin waya har guda biyar wadanda ya ce a kirashi dasu matukar aka ga wani na yunkurin aikata ba daidai ba musamman ma akan jami’an nasa na ‘yansanda da sauran al’umma masu yunkurin tada zaune tsaye.
Haka kuma ya umarci masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasar da su ja kunnen al’ummarsu bisa tada zaune-tsaye musamman kafin zabe, bayan zabe da kuma bayan kammala zaben na bana.
Shi kuwa da yake nasa jawabin a yayin taron, kwamishinan ‘yansanda na jihar CP Bala Zama senchi yace, jihar Jigawa jihace wadda Allah ya albarkace ta da zaman lafiya don haka ba zasu zuba ido wasu maras kishi su tarwatsa wannan zaman lafiya akan san zuciyarsu.
Don haka ya umarci jami’an nasu dasu kara daura damararsu domin tinkarar wannan zabe tareda tabbatar da gaskiya da adalci yayin gudanarda ayyukansu domin dorewar dimokradiyya da cigaban kasa baki daya.
Daga karshe ya yabawa duk wadanda suka sami damar halartar taron gamida bada tabbacin cewa rundunar tasu ta shirya tsaf domin tinkarar zaben mai zuwa.

Exit mobile version