Maigari Abdulrahman" />

Zabe: Yadda Mashahuren ‘Yan Siyasa Suka Kasa Lashe Mazabarsu

Bayan bada sanarwar dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da hukumar zabe INEC ta yi a ranar Assabar da misalin karfe biyu na dare, bisa dalilan wasu ‘yan matsaloli da hukumar ta bayar, daga karshe an samu gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Febrairu.
To sai dai, zaben wanda aka gudanar a satin nan ya zo da abubuwan ban mamaki ta yanda manya-manyan ‘yan siyasa suka fadi a runfunar zaben su.
Premium Times ta yi duba da nazari a kan wasu fitattun ‘yan siyasar da suka fadi a runfunan zabensu.

•Atiku Abubakar – PDP
Dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya fadi a runfar zabensa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC ne ya doke sa a runfar.
Atiku Abubakar, wanda ya jefa kuri’arsa a runfar Ajiya PU012 a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa ya samu kuri’a 167, inda APC ta samu 186.
Bacin kujerar shugaban kasa, Atiku bai iya kawo wa PDP kujerar Dan majalisar tarayya da ta wakilai ba a runfar, inda APC ta samu kuri’a 187 a zaben Sanata a kan na PDP mai kuri’a 120. A na dan majalisa, APC ta samu kuri’a 145, inda PDP ta samu 121.

•Yemi Osinbajo – APC
Kamar Atiku, shi ma mataimakin shugaban kasa na jam’iyar APC, Yemi Osinabajo bai iya samun nasara a kan ‘yan adawa ba, inda PDP ta doke sa a runfar zabensa.
Mataimakin shgugaban kasar tare da matarsa, Dolapo, sun jefa kuri’arsu a runfar zabe mai lanba 33, Bicotoria Garden da misalin karfe 10:53 na safe a Legas.
A zaben yan majalisar dattawa da wakilai, PDP ta doshe Mataimakin shugaban kasar a runfar zabensa.
A kujerar shugaban kasa, PDP ta samu kuri’a 384, inda APC ta samu 197. A kujerar Sanata, APC ta samu 228, kasa ga kuri’un PDP 378. Haka a kujerar dan majalisar wakilai ma, PDP ta yi rinjaye a kan APC, inda PDP ta samu 244, yayin da APC take da 167.
A wannan runfar zaben, har wa yau, a nan ne dan takarar jam’iyar ANN, Fela Durotoye ya jefa kuri’arsa.

•Former President Olusegun Obasanjo
Bayan zabar dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar a kan Buhari na APC da ya yi, tsohon shugaban kasar ya fadi a runfar zabensa da rinjaye mai yawa.
Tsohon shugaban kasar ya jefa kuri’arsa a Abeokuta jihar Ogun, da misalin karfe 11:15 na safiyar Assabar din. A nan runfar zaben ta Obasanjo, APC ta doke PDP.
PDP ta samu kuri’a 18 kacal a kujerar shugaban kasa, inda APC ta samu 87.
Haka kuma, jam’iyar ADC, jam’iyar ma wacce take ta Obasanjo ita ma, kuri’a 4 kadai ta iya samu azaben.

•Shehu Sani – PRP
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani na jam’iyar PRP bai iya cin runfar zabensa ba, inda abokin hammayarsa a kujerar Sanata, Uba Sani na jam’iyar APC ya doke sa.
Runfa mai lanba ta 20, Unguwar Seriki, Kaduna ta arewa ce runfar zaben Shehu Sani, a nan runfar, Uba Sani ne ya doke Shehu Sani, inda Uba ya samu kuri’a 236, a yayin da shehu Sani yake da 51.
A sauran sakamakon kuwa, APC ta samu kuri’a 292 a kujerar shugaban kasa, inda PDP ta samu 23. A kujerar yan majalisar wakilai, APC ta samu kuri’a 240, PDP 47, sai kuma PRP 28.
Kingsley Moghalu – YPP
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyar YPP shi ma bai samu nasarar lashe zabe ba a runfar zabensa jihar Anambra.
Mista Moghulu, wanda yake tsohon mataimakin babban bankin Nijeriya CBN, ya fadi a runfar zabensa da ke Uruagu, Nnewi, jihar Anambra.
A runfunan zabe 3 da ke wurin, Mista Moghalu ba inda ya samu nasara; duka PDP ce take da rinjaye a kansa. Moghalu ya samu 137 a runfar farko, 145 a wata runfar, da kuma 127, yayin da PDP ta samu 137, 145, da 256 a jerin runfunan.

•Donald Duke – SDP
Tsohon Gwamann jihar Cross Riber kum dan takarar shugaban kasa na jam’iyar SDP, Donald Duke, ya fadi a zaben shugaban kasa a runfarsa ta zabe.
Tsohon Gwamnan kuri’a 6 kadai ya samu, inda PDP ta samu nasara a runfar da kuri’u 291.
Mista Duke ya jefa kuri’ar tasa ne a runfa mai lanba PU005 a Diamond Hill, Calabar, jihar Cross Riber.

•Ntufam Hilliard Etta – APC
Mataimakin shugaban jam’iyar APC yankin kudu-maso-kudu, Ntufam hilliard Etta, shi ma ya fadi a runfar da Mista Duke ya fadi, inda PDP ta lashe kujerar ‘yan majalisar wakilai da ta dattawa a runfar, baya ga ta shugaban kasa.
PDP ta samu kuri’a 207 a kujerar Sanata, inda APC ta samu 193. A kujerar wakilai ta kasa, PDP ta samu nasara da kuri’a 215 a kan APC mai kuri’a 140.

•Babajide Sanwo-Olu – APC
Dan takarar Gwamna na jam’iyarAPC a jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, shi ma bai iya kawo wa jam’iyar APC runfar zabensa ba.
Ya fadi ne a runfar tasa ta Femi Okunnu, Lateef Jakande, Ikoyi jihar Legas. Dan takarar PDP Atku Abubakar ne ya samu nasara a runfar, inda ya samu kuri’a 52 a kan Buhari na APC da kuri’a 48.

•Jimi Agbale – PDP
Kamar Mista Sanwo-Olu, haka ita ma jam’iyar PDP ta fadi a runfar zaben da dan takarar Gwamananta, Jimi Agbaje ya jefa kuri’arsa.
A runfar zabe mai lanba PU004, hanyar Hinderera, shiyar Liberpool, Apapa Legas, APC ce ta samu nasarar kujerar Shugabn kasa da kuri’a 83 a kan PDP mai kuri’a 80.
A kujerar Sanata, APC ta samu kuri’a 88, inda jam’iyar PDP ta samu 79.
Andy Ubah – APC
Sanata mai wakailatar Anambra ta arewa a karkashin jam’iyar APC, Andy Ubah shi ma ya fadi a runfar zabensa.
Sanatan, wanda ya jefa kuri’arsa a runfar Salbattion Army, yankin Uba, ya fadi da gagarumin rinjaye, inda PDP ta samu kuri’a 115 yayin da yake da kuri’a 4 kacal.

•Buba Galadima
Kakakin yakin neman zaben Atiku, Buba Galadima ya sha gagarumin kaye a runfar zabensa.
Buba Galadima, wanda yake babban abokin Buhari a da, kwatsam daga baya ya koma dan adawarsa, kuri’a 2 kadai ya iya samu, inda APC ta samu kuri’u 750.

•Bode George – PDP
Wani jigo a jam’iyar PDP, Bode George, wanda ya jefa kuri’arsa a runfar zabe da ke yanki na 2, POU01, Oko-Faji, Legas bai kawo runfarsa wa PDP ba.
Buhari na jam’iyar APC shi ne ya lashe zabe a runfar da kuri’a 84, inda abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu 40.
Ko a shekarar 2015 ma, Mista George bai ci runfar zabensa ba.

•Ibrahim Dankwambo – PDP
Jam’iyar PDP ta fadi a runfar zaben Gwamnan jihar Gwambe mai barin gado, Ibarahim Dankwambo.
Buhari na jam’iyar APC ne ya samu nasarar lashe zaben, inda ya samu kuri’a 453, a yayin da Atiku ya samu kuri’a 80. Gwamnan ya kada kuri’arsa ne a runfar Hassan Manzo da ke Harwagana karamaar hukumar mulki ta Gwambe.
To sai dai, Dankwambo wanda yake dan takarar kujerar Sanata a jam’iyar PDP, ya doke dan takarar APC da Ahmaa Alkali, inda ya samu kuri’a 325, yayin da Ahmad din yake da 212.

•Dapo Abiodun – APC
Dan takarar Gwamna a jihar Ogun karkashin jam’iyar APC, Dapo Abiodun, shi ma ya fadi a runfar zabenbsa, PDP ce ta samu nasara a runfar.
Mista Abiodun ya jefa kuri’arsa ne a runfar Ita Osanyi da ke Iperu, karamar hukuma Ikenne da ke jihar ta Ogun.
Atiku Abubakar na jam’iyar PDP ne ya samu nasara a runfar, inda ya samu kuri’a 124, yayin da Buhari ya samu 118.
The Ogun State APC gobernorship candidate, Dapo Abiodun, also lost his polling unit to the opposition party.
Mista Abiodun ya jefa kuri’arsa ne a runfar zabe da ke Ita Osanyi a Ipewru, Ikenne karamar hukumar mulki ta Ogun.
Atiku Abubakar na jma’iyar PDP ne ya samu nasara a runfar, inda ya samu kuri’a 124, yayin da Buhari yake da 118.

Exit mobile version