Khalid Idris Doya" />

Zaben 2015: Ko Yanzu Zan Sake Saduda Ga Buhari – Jonathan

Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewar bai yi nadamar sallama zaben shugaban kasar Nijeriya na 2015 wa Muhammadu Buhari ba.
Tsohon shugaban ya ce ko a yanzu ma zai kuma iya sake yin hakan muddin yana da damar da za ta bashi zarafin yin hakan.
A bisa fadin Jonathan, sauka daga karagar mulki salum alum bayan shudewar wa’adi, ko bayan cin nasara a zabe wani abu ne dake karawa ‘yan siyasa daraja a idon Duniya, a cewar shi; abun da yayi a shekarar 2015 zai ci gaba da bayar da daman tsara tattauna batun siyasa a wannan yankin na Afirka, wanda a cewarsa ta hakan za a samu ci gaba sosai ta fuskacin siyasa da shugabanci.
Majiyarmu ta nakalto cewar tsohon shugaban kasar ya fadi cewar tafiyar da gwamnati na bukatar sadaukarwar, ya kara da cewa dukkanin wani mutum bai zama cikin shirin sadaukarwa ba, to tabbas bai da alaka da siyasa kuma ba irinsu ne ake da bukata a siyasa ba.
Ya ke cewa: “Bari na fito da batun balo-balo. Muddin na sake samun irin wannan damar da na samu a baya, zan sake yin makamancin abun da na yi,” yana mai fadin haka a waje wani taron tsoffin shugabanin kasashen Afirka ‘constitutional term limits summit’ da ya gudana a Naimey ta kasar Nijar.
Jonathan ya ci gaba da cewa, “A kowani lokaci ina cewa muddin kana son zama shugaba dole ne ka kasance a shirya kake wajen sallamawa da sadaukarwa. Muddin kuma ka zama baka da sadaukarwa domin taimakon jama’a, to tabbas ba ka da wani alaka da siyasa, baka da kusanci da harkar siyasa.
“Abun da ya kamata mu sani kawai shine gina al’umma. Wasu mutane suna mutuwa a kokarinsu na gina al’umma.
“Ni sam ban yi nadama har zuwa wannan lokacin ba, a kowace dama da nake da ita, babu nadama saboda abun da na yi zai ci gaba da bayar da damar tsara tafiyar siyasa yadda ya kamata da jawo wa shugabanni kima ba kawai a Nijeriya ba, a ma yankin Afirka gaba daya.
“Wasu mutanen ba su ji dadin abun da na yi ba, a yayin da muke kokarin ci gaba da kyautata demokradiyya, mutane za su fara duba hanyoyin da suka dace da kuma wadanda ba su dace ba.
“Idan dan karamin gudunmawar da na bayar zai taimaka wajen kyautata demokradiyyarmu a Nijeriya da nahiyar Afirka, tabbas kuwa a shirye nake na kara yin hakan domin ci gaban demokradiyya,” A cewar Jonathan.
Tsohon shugaban Nijeriyar ya kuma ci gaba da cewa, “wasu mutanen da ke kewaye da shugaban kasa suna tayar da batun, ta yaya za a iya tafiyar da su alhali suna da gurguwar fahimta wa shugaban kasa,” A fadinsa.
Kamar yadda Jonathan ke cewa, tilas ne kuma dole ne shugaban kasa ya tashi tsaye ya zama jarumi domin kare kansa daga masu ingizashi zuwa tafarkin bata da za ta kai shi ga rasa nasara.
“Irin wadannan mutanen a kowani lokaci a hakan za su zauna. Don haka dole ne shugaban kasa ya kasance a shirye yake don kauce wa masu ingizashi tafarkin da bai dace ba domin ganin bai fada tarkonsu ba,” A cewa Ebele.
Tsohon shugaban kasar Liberiya da ya kasance shugaba daga 1990 zuwa 1994 ya jinjina wa Jonatan a bisa mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ko fitina ba.
LEADERSHIP A Yau dai ta labarto cewar Jonathan ya amince da mika wa Buhari mulkin Nijeriya ne bayan shan kaye da yayi a zaben 2015 da aka gudanar, inda nan take ya kira Buhari ya tayashi murna da samun nasarar lashe zaben, hakan ya kawo karshen kokarin fadace-fadace da tashin hankali a kasar.
A karshen taron dai na tsawon kwanaki 3 da suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar tsofaffin shugabannin kasashen Afirka, da na kungiyoyin fararen hula sun kudiri aniyar soma tuntubar shugabannin kasashe akan uahimancin mutunta ka’idar wa’adin mulki, dai dai abinda kundin tsarin mulki ya yi tanadi, a ci gaba da neman hanyoyin karfafa demokardiyya a wannan nahiya.
Madam Chantal Nare ta Burkina Faso ta gabatar da sanarwar karshen taron tsofaffin shugabannin kasashen Afirka, bayan shafe kwanaki 3 ana tattauna hanyoyin magance matsalar kwaskware kundin tsarin mulki.
Taron ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka da sauran kungiyoyin kasa da kasa irinsu ECOWAS, da makamantansu dasu dage haikan don ganin an mutunta abubuwan dake rubuce a kundin tsarin mulkin kasa, sannan aka gargadi shugabanni dasu guji kwaskware kundin tsarin mulki ta hanyar amfani da karfi, domin kaucewa barkewar rigingimun da aka saba fuskanta a wannan nafiya.
Tsohon shugaban kasar Nijar Alhaji Mahaman Ousman na kallon wannan yunkuri na cibiyar NDI a matsayin wata hanyar kawo karshen zagon kasar da demokradiyya ke fuskanta a ‘yan shekarun nan a nahiyar Afirka.
Masu rajin kare demokradiyya sun dauki alkawarin kaddamar da zagaye a kasashen da shugabanninsu ke kokarin shirya tazarce ta haramtaciyar hanya irinsu Guniea, da Conacry, da Cote d’iboire, da kuma Cameroun, da nufin tayarda talakawa daga barci domin tilastawa shugabaninsu daraja.

Exit mobile version