Idris Aliyu Daudawa" />

Zaben 2019: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Kiyaye Yada Labaran Karya

Yayin da ake shirin gabatar da zabubukan gwamnoni da kuma ‘yan majalisun jihohi ranar 9 ga watan Mariis, 2019 kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, wani malamin jami’a Farfesa Ebans Osabuohien, ya yi kira da ‘yan jarida cewar su kiyaye bayyana labarun da bana gaskiya ba.
Osabuohien shi Farfesa ne na sashen tattalin arziki a jami’ar Cobenant dake a jihar Ogun shine wanda ya yi wannan bayanin lokacin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Abuja ranar Talata.
Ya yi bayani cewar su labaran da bana gaskiya ba, ba wai kawai suna da wata dama bace ta sa a samu tashe- tashen hankula bane, kafin ko kuma lokacin zabe, da kuma bayan zaben, amma kuma suna sa a rasa amincewa da yarda da sakamakon zabubbukan suka kasance. Saboda kuwa ai mutane ba za su amince da hakan bane.
”Shi amfani kafafen watsa labarai lokaci zabubbuka shine sun ilmantar da al’umma, saboda kuwa su wata mahada ce, tsakanin Shugabanni wadanda suke mulka.
”Don haka su bangren watsa labarai suna da rawar da suke takawa wajen bayyana gaskiya, su kasance su ba ruwan su da kowa, su bayyana gaskiya lokacin da ake wayar da kan al’umma.”
Kamar dai yadda ya malamin ya kara bayyanawa su ‘yan jarida ya kamata su rika aiki da kungiyoyi masu zaman kansu, domin a rika bayyana gaskiya, abin da zai taimaka wajen ilmantar da ‘yan Nijeriya fiye da ko wanne lokaci.
Ya yi kira da masu zabe da su fito kwansu da kwarkwatar su, su zabi wadanda suke so lokacin zaben, amma kuma ya kamata su yi amfani da hankali da kuma tunanin su, ba sai an matsa masu ba, dangane da wadanda za su zaba.
Daga karshe ya yi kira da mutane masu zabe da su bukaci bayanan ayyukan da ake yi masu daga Shugabannin su, tun daga matakan gwanatocin tarayya, jihohi, da kuma kananan Hukumomi.

Exit mobile version