Ibrahim Muhammad" />

Zaben 2019: An Nemi ‘Yan PDP Su Hada Kai A Kano

Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare wani jigo ne a jam’iyyar PDP a jihar Kano, inda kuma ya yi kira ga ‘yan PDP, musamman a jihar su zo a hada kai a kauda Gwamnatin Ganduje, wanda ya yi zargin ya maida lalitar jihar kamar ta gado.

Ya yi wannan kira ne a zantawarsa da wakilinmu a kwanakin baya, inda ya nuna takaicinsa bisa zargin da ake yi na yadda wasau daga cikin jama’an gwamnati ke  karbar kudi daga hannaun  ‘yan kwangila, saboda haka, sai su yi aikin da aka ba su yadda suka ga dama, kuma za ka ga ana ayyuka ba inganci a jihar.

Ya kawo misali da cewa in an ce za a gina gadar sama, sai a gina kududdufi, dan kwangila in zai yi aiki a Naira miliyan 100  ya kawo Naira miliyan 30 ya bayar, duk aikin da zai yi mara karko ba za a iya ce masa don me ba.

Ya kara da cewa “ga wanda  ya san harkar kasuwanci irina, zan iya masana’antar da zan dau matasa aiki da suka gama karatun digiri guda 1000, wanda albashinsu ba zai gaza Naira 60,000  duk wata ba, kuma in ci riba, amma mutum daya   kadai ana zarginsa da kwashewa”

Don haka Dayyabu Ahmad ya ce cikin yardar Allah za su kada APC a jihar Kano da kasa, domin ba mai kishin sake zaben Ganduje haka Buhari, domin da an gan shi cewa ake yunwa-yunwa.

Ya ci gaba da korafin cewa an kashe kasuwanci a Arewa, an hana noma an hana kiwo. Don haka ya ce “ya zama wajibi a kammu mu karya wannan Gwamnati mu watsar da ita mu kafa PDP a kowane mataki don ci gaban al’ummar kasar nan.”

Exit mobile version