Sharfaddeen Sidi Umar" />

Zaben 2019: Aski Ya Zo Gaban Goshi

‘Yan Nijeriya Milyan 84 Da ’Yan Kai Za Su Hallara A Rumfunan Zabe
Masu Kada Kuri’a Sun Karu Da Sama Da Milyan 15 A Bana
Rikita-Rikita Da Salon Yakin Neman Zaben
Ýan Takarar Shugaban Kasa 73 Ke Fafatawa

Babban Zaben Nijeriya na shekarar 2019 wanda al’ummar kasa suka jima suna jira mai cike da tarihi, ya riga ya gabato domin a yanzu a na kasa da awanni 24 ‘yan takara su fara auna tsawonsu a zaben wanda mai girma zai dauki girmansa a mabambantan kujeru.
Baya ga zaben 2015, zaben 2019 shi ne zabe mafi zafi, mafi daukar hankalin al’ummar ciki da wajen kasa haka ma mafi shan kwaram da kwaramniyar siyasa da ‘yan Nijeriya suka shaida tun daga kan yekuwar neman zabe da yadda jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka rika nunin juna da yatsa tare da yi wa juna wankin babban bargo a zazzafar bakar adawa.
A gobe Asabar 16 ga Fabrairu za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya wadanda suka kunshi ‘Yan Majalisar Dattawa da ‘Yan Majalisar Wakilai. A yayin da bayan makwanni biyu a ranar 2 ga Maris za a gudanar da zaben Gwamna da na ‘Yan Majalisar Dokoki na Jiha.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a karkashin shugabancin Farfesa Mahmud Yakubu ta yi alkawalin gudanar da ingantacce, amintacce kuma karbabben zaben da jama’ar kasar nan za su yaba wanda a cewar Hukumar za a gudanar da zaben 2019 cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna ko wane irin bambanci ko bangaranci ba.
Shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari wanda duniya ta zuba wa idanun ganin yadda zai jagoranci gudanar da zaben kasar sa mai cike da rudu da kwamacalar siyasa iri daban-daban, ya bayyana cewar zaben gaskiya da adalci ne tubalin dorewar Dimokuradiyya da zaman lafiya a kowace irin kasa, don haka ya bayar da tabbacin za a rika tunawa da shi wajen gudanar da zaben gaskiya da adalci.
Buhari wanda ya bayyana hakan tun a yayin da yake kaddamar da kwamitin yakin neman zaben sa a Abuja, ya bayyana cewar Hukumar Zabe ta gudanar da zabuka 195 a mazabun kasar nan wanda kuma ya fi sauran zabukan da suka gabata inganci da adalci duk kuwa da cewar ra’ayin jam’iyyar adawa ta PDP ya saba da ra’ayin Shugaban Kasa.
Shugaba Muhammad Buhari na jam’iyyar APC wanda ke neman sake komawa mulki a karo na biyu da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne manyan ‘yan takara; wadanda manyan jam’iyyun Nijeriya biyu suka tsayar takara domin fafatawa a karon battar karfen shugabancin kujera mafi daraja ta daya a kasar nan.
LEADERSHIP A YAU Juma’a ta labarto cewar zaben 2019 shi ne zabe mafi yawaitar wadanda suka fito neman Shugabancin Kasa domin akwai ‘yan takarar shiga Fadar Mulkin Nijeriya har mutum 73 da za su fafata a zaben, wanda har wayau shi ne zabe mafi yawan wadanda za su jefa kuri’a domin kuwa ‘yan Nijeriya miliyan 84, 004, 84 ne suka yi rajistar zabe wadanda za su hallara a rumfunan zabe a gobe. Haka ma daga ciki sama da matasa miliyan 42 ne suka yi rajistar zabe kamar yadda Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana. Bakidaya jam’iyyun siyasa 91 ne za su fafata a zaben wanda za a gudanar a rumfunan zabe miliyan 11, 997, 73.
Ya ce adadin yawan masu zabe ya kama kashi 42 na bakidayan yawan ‘yan Nijeriya miliyan 198 da ake da su a yanzu haka. Haka ma adadin ya karu da miliyan 15.17 sama da mutane miliyan 68, 838, 476 da suka yi zabe a shekarar zabe ta 2015.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a yayin da yake hannunta babban kundin rajistar masu zabe ga jam’iyyun siyasa a Abuja, ya bayyana cewar Yankin Kudu -Maso- Kudu ya na da mutane miliyan 12, 841, 279 da suka yi rajistar zabe wanda hakan ya kama kashi 15.29 na bakidaya yawan wadanda suka yi rajista.
Ya ce Shiyar Arewa- Ta Tsakiya na da adadin mutane miliyan 13, 366, 070 da suka yi rajistar zabe wanda hakan ke wakiltar kashi 15.91. Kudu- Maso- Gabas kuwa na da wadanda suka yi rajista mutum miliyan 10, 057, 130 tare da wakiltar kashi 11.91, sai kuma Kudu- Maso- Yamma da ke da mutane miliyan 16, 292, 212 da suka yi rajista tare da samun kaso 19.39 na bakidaya yawan wadanda suka yi rajista.
Kamar yadda Hukumar Zabe ta bayyana, Yankin Arewa- Maso- Gabas na da jimillar mutane miliyan 11, 289, 293 da suka yi rajistar zabe tare da wakiltar kashi 13.44, sai kuma Yankin Arewa- Maso- Yamma wanda shi ne ya fi kowane yankin kasar nan yawan wadanda suka yi rajistar zabe ta hanyar samun tsabar mutane miliyan 20, 158 tare da wakiltar kashi 24 na bakidaya adadin wadanda suka yi rajistar zabe a Nijeriya.
Wakilinmu ya labarto cewar a bisa ga dimbin al’ummar yankin ne dalilin da ya sa duk wani mai neman takarar shugabancin kasar nan ke baiwa shiyar Arewa- Maso- Yamma matukar muhimmanci, saboda baya ga kima da tasirin yankin a siyasar Nijeriya haka ma ana gani da kallon duk wani wanda yankin ya mara wa baya to zai samu nasarar lashe zabe kamar yadda tarihi ya gabata a zabukanbaya.
A kan sanin wace jam’iyya ce ta fi dacewa da shugabancin kasar nan, Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole a mabambantan lokuta a wajen yakin neman zabe ya na bayyana cewar Nijeriya da al’ummarta na bukatar ci-gaba da kasancewa a karkashin mulkin Gwamnatin APC wadda ta taka rawar gani wajen dawowa da kima da martabar kasar nan tare da inganta al’amurran da suka yi bahaguwar tabarbarewa a shekaru 16 na mulkin PDP, don haka a cewarsa Muhammadu Buhari ne mafi dacewar ci-gaba da jagorancin kasar nan.
To amma ita kuwa jam’iyyar PDP daga Arewa zuwa Kudu wajen gangamin yakin neman zabe, ba ta taba yin kasa a guiwa ba wajen bayyana wa al’umma cewar jam’iyyar APC ta gaza kwarai ainun wajen sauke nauyin da al’umma suka dora mata na samar da kyakkayawan shugabanci da share hawayen al’umma.
A cewar Shugaban Jam’iyyar, Uche Secondus Gwamnatin APC a karkashin Muhammadu Buhari ba ta haifarwa ‘yan Nijeriya komai ba face koma bayan tabarbarewar al’amurra, karuwar tabarbarewar sha’anin tsaro da cin hanci da rashawa tare da karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa.Babban Zaben Nijeriya na shekarar 2019 wanda al’ummar kasa suka jima suna jira mai cike da tarihi, ya riga ya gabato domin a yanzu a na kasa da awanni 24 ‘yan takara su fara auna tsawonsu a zaben wanda mai girma zai dauki girmansa a mabambantan kujeru.
Baya ga zaben 2015, zaben 2019 shi ne zabe mafi zafi, mafi daukar hankalin al’ummar ciki da wajen kasa haka ma mafi shan kwaram da kwaramniyar siyasa da ‘yan Nijeriya suka shaida tun daga kan yekuwar neman zabe da yadda jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka rika nunin juna da yatsa tare da yi wa juna wankin babban bargo a zazzafar bakar adawa.
A gobe Asabar 16 ga Fabrairu za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya wadanda suka kunshi ‘Yan Majalisar Dattawa da ‘Yan Majalisar Wakilai. A yayin da bayan makwanni biyu a ranar 2 ga Maris za a gudanar da zaben Gwamna da na ‘Yan Majalisar Dokoki na Jiha.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a karkashin shugabancin Farfesa Mahmud Yakubu ta yi alkawalin gudanar da ingantacce, amintacce kuma karbabben zaben da jama’ar kasar nan za su yaba wanda a cewar Hukumar za a gudanar da zaben 2019 cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna ko wane irin bambanci ko bangaranci ba.
Shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari wanda duniya ta zuba wa idanun ganin yadda zai jagoranci gudanar da zaben kasar sa mai cike da rudu da kwamacalar siyasa iri daban-daban, ya bayyana cewar zaben gaskiya da adalci ne tubalin dorewar Dimokuradiyya da zaman lafiya a kowace irin kasa, don haka ya bayar da tabbacin za a rika tunawa da shi wajen gudanar da zaben gaskiya da adalci.
Buhari wanda ya bayyana hakan tun a yayin da yake kaddamar da kwamitin yakin neman zaben sa a Abuja, ya bayyana cewar Hukumar Zabe ta gudanar da zabuka 195 a mazabun kasar nan wanda kuma ya fi sauran zabukan da suka gabata inganci da adalci duk kuwa da cewar ra’ayin jam’iyyar adawa ta PDP ya saba da ra’ayin Shugaban Kasa.
Shugaba Muhammad Buhari na jam’iyyar APC wanda ke neman sake komawa mulki a karo na biyu da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne manyan ‘yan takara; wadanda manyan jam’iyyun Nijeriya biyu suka tsayar takara domin fafatawa a karon battar karfen shugabancin kujera mafi daraja ta daya a kasar nan.
LEADERSHIP A YAU Juma’a ta labarto cewar zaben 2019 shi ne zabe mafi yawaitar wadanda suka fito neman Shugabancin Kasa domin akwai ‘yan takarar shiga Fadar Mulkin Nijeriya har mutum 73 da za su fafata a zaben, wanda har wayau shi ne zabe mafi yawan wadanda za su jefa kuri’a domin kuwa ‘yan Nijeriya miliyan 84, 004, 84 ne suka yi rajistar zabe wadanda za su hallara a rumfunan zabe a gobe. Haka ma daga ciki sama da matasa miliyan 42 ne suka yi rajistar zabe kamar yadda Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana. Bakidaya jam’iyyun siyasa 91 ne za su fafata a zaben wanda za a gudanar a rumfunan zabe miliyan 11, 997, 73.
Ya ce adadin yawan masu zabe ya kama kashi 42 na bakidayan yawan ‘yan Nijeriya miliyan 198 da ake da su a yanzu haka. Haka ma adadin ya karu da miliyan 15.17 sama da mutane miliyan 68, 838, 476 da suka yi zabe a shekarar zabe ta 2015.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a yayin da yake hannunta babban kundin rajistar masu zabe ga jam’iyyun siyasa a Abuja, ya bayyana cewar Yankin Kudu -Maso- Kudu ya na da mutane miliyan 12, 841, 279 da suka yi rajistar zabe wanda hakan ya kama kashi 15.29 na bakidaya yawan wadanda suka yi rajista.
Ya ce Shiyar Arewa- Ta Tsakiya na da adadin mutane miliyan 13, 366, 070 da suka yi rajistar zabe wanda hakan ke wakiltar kashi 15.91. Kudu- Maso- Gabas kuwa na da wadanda suka yi rajista mutum miliyan 10, 057, 130 tare da wakiltar kashi 11.91, sai kuma Kudu- Maso- Yamma da ke da mutane miliyan 16, 292, 212 da suka yi rajista tare da samun kaso 19.39 na bakidaya yawan wadanda suka yi rajista.
Kamar yadda Hukumar Zabe ta bayyana, Yankin Arewa- Maso- Gabas na da jimillar mutane miliyan 11, 289, 293 da suka yi rajistar zabe tare da wakiltar kashi 13.44, sai kuma Yankin Arewa- Maso- Yamma wanda shi ne ya fi kowane yankin kasar nan yawan wadanda suka yi rajistar zabe ta hanyar samun tsabar mutane miliyan 20, 158 tare da wakiltar kashi 24 na bakidaya adadin wadanda suka yi rajistar zabe a Nijeriya.
Wakilinmu ya labarto cewar a bisa ga dimbin al’ummar yankin ne dalilin da ya sa duk wani mai neman takarar shugabancin kasar nan ke baiwa shiyar Arewa- Maso- Yamma matukar muhimmanci, saboda baya ga kima da tasirin yankin a siyasar Nijeriya haka ma ana gani da kallon duk wani wanda yankin ya mara wa baya to zai samu nasarar lashe zabe kamar yadda tarihi ya gabata a zabukanbaya.
A kan sanin wace jam’iyya ce ta fi dacewa da shugabancin kasar nan, Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole a mabambantan lokuta a wajen yakin neman zabe ya na bayyana cewar Nijeriya da al’ummarta na bukatar ci-gaba da kasancewa a karkashin mulkin Gwamnatin APC wadda ta taka rawar gani wajen dawowa da kima da martabar kasar nan tare da inganta al’amurran da suka yi bahaguwar tabarbarewa a shekaru 16 na mulkin PDP, don haka a cewarsa Muhammadu Buhari ne mafi dacewar ci-gaba da jagorancin kasar nan.
To amma ita kuwa jam’iyyar PDP daga Arewa zuwa Kudu wajen gangamin yakin neman zabe, ba ta taba yin kasa a guiwa ba wajen bayyana wa al’umma cewar jam’iyyar APC ta gaza kwarai ainun wajen sauke nauyin da al’umma suka dora mata na samar da kyakkayawan shugabanci da share hawayen al’umma.
A cewar Shugaban Jam’iyyar, Uche Secondus Gwamnatin APC a karkashin Muhammadu Buhari ba ta haifarwa ‘yan Nijeriya komai ba face koma bayan tabarbarewar al’amurra, karuwar tabarbarewar sha’anin tsaro da cin hanci da rashawa tare da karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa.

Exit mobile version