Zaben 2019: Ba Mu Da ‘Yan Takara Sai Buhari Da Masari — Jam’iyyar APC

Daga  El-Zaharadeen Umar, Katsina

Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta bayyana cewaa zabe mai zuwa na shekarar 2019 ba su da dan takarar shugaba kasar da ya wuce Shugaba Muhammadu Buhar, a Katsina kuma gwamna Aminu Bello Masari dan takararsu.

Shugaban Jam’iyyar Shitu S. Shitu ya bayyana haka jim kadan bayan kammala wani da taro da jam’iyar ta kira a Katsina inda ta ce sun yanke wannan hukunci ne bayan sun lura da irin cigaban da wadannan shuwagabani suka kawo al’umma tun daga hawansu zuwa yanzu.

Ya kuma kara da cewa abubuwan da yawa sun fara a wannan tafiya inda har a ka samu wasu bara gurbi suke neman kawo cikas a wannan tafiya karkashin shugaban Muhamamdu Buhari har a ka samu nasarar cin zabe a shekarar2015 tun daga shugaban kasa zuwa ‘yan majalisa.

Ya ce wannan ya kara ba su kwarin gwiwa  inda suka tattauna da masu ruwa da tsarki a matakin jihar da kuma kananan humumomi daga karshe suka fito da wannan matsaya guda daya.

Shugaban na jam’iyya ya ce sun fadawa duniya suna da kyakkawar manufa sannan suna zaune tare da sauran bangarori lafiya, kowane bangare tana kowa hakkinsa wanda shari;a ta tanada.

Acewarsa bayan doguwar tattaunawa da aka yi da shuwagabanin jam’iyya da suka hada da shuwagabanin kananan humumomi da sakatarori inda suka tattauna abubuwa masu mahimmaci, a karshe bisa shugabanci da suke samu na adalci daga shugaban kasa zuwa jaha, jam’iyyar ta yi ittifaki cewa bata da dan takarar shugaban kasa a 2019 sai Muhammadun Buhar a jihar Katsina kuma gwamna Aminu Bello Masari.

Kazalika jam’iyya ta ki yi karin haske game da wasu matsaloli da ta ke fuskunta musamman a cikin gidanta inda ko a kwanakin baya sai da jam’iyara ta tsaida matakin shugaban jam’iyar na Katsina ta tsakiya.

Sannan har yanzu ba su bada wani gamsashen bayyani ba game da dakatarwa, inda ake ganin ya kamata ta fara dinke wannan baraka kafin daukar wannan matakin na tsayar ‘a yan takara a zabe mai zuwa.

Bayan haka kwanan na wata matsalar ta sake kunno kai inda wasu da suke ganin ba a kyautata masu ba gwamnatance suka ware da sunan APC Akida wanda ita ma ana ganinta a matsayin wata babar barazana a wannan tafiya ta APC Masariya.

Exit mobile version