Connect with us

RAHOTANNI

Zaben 2019: Bokola Saraki Ya Aiyyana Takarar Shugabancin Nijeriya

Published

on

A ranar Alhamis ne shugaban majalisar Dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki CON, Waziri na Ilorin ya aiyyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kaaar nan a karkashin jamiyyar PDP. Dakta Saraki ya aiyyana wannan kuduri masa ne a wani taron masu ruwa da tsaki, musamman matasa dake da kudurin tsayawa takarar mukaman siyasa daban daban a fadin kasar nan, an dai gudanar da taron ne a oral din Sheraton dake babban birnin tarayayyar kasar nan Abuja, ranar 30 ga watan Agusta 2018.
A jawabinsa Sanata Saraki ya fara ne da nuna farin cikinsa a kan yadda masata suka nuna shaukinsu na shiga harkokin siyasa da nufin suma a dama dasu a fagen gudanar da mulkin kasar nan. Ya kuma ci gaba cewa, Cudanyar dana yi daku dama wasu matasa a fadin kasar nan ya tabbaar mani da cewa, Allah Ya albarkace mu da jajirtattun matasa dake da kudurin ceto kasar nan. Ya kuma mika godiyarsa na samun daman tattauna da matasan a kan matsalolin da Nijeriya ke fuskanta da kuma tattauna hanyoyin fitar da hanyoyin warware matsalolin musamman ganin kakar zaben shekarar 2019 na dada karasowa.
Daga nan ya nuna mahimmancin matasa a dukkan harkar ci gaban kasar nan saboda matasa ne kusan kashi 70 na alummar Nijeriya. “Wannan wani abu ne da dukkan kasashen duniya za su yi fatan samu.
Amma abin takaicin shi ne duk da dimbin arzikin da Allah Ya hore mana, yan Nijeriya da dama na a cikin mumman hali, yan Nijeriya da dama na cikin yunwa, yara kanana da mata da sauran jama’a na mutuwa saboda cututtakar da za a iya yin maganinsu cikin sauki, rayuwar jama’a da dama na cikin matsanancin talauci, kusan mutum Miliyan 87 a kasar nan na a cikin talauci wannan ya sa a halin yanzu Nijeriya ke a kan gaba a tsakanin kasashen duniya a fagen talauci. Matasanmu basu da wani fata a rayuwarsu, abubuwan daya kamata a samar a makarantu don ilimantar da matasanmu ya karanta, an kuma kasa fito da aiyyukan yi ga matanmu, hakan ya garkamesu ya kuma hana su bayar da gudummawarsu a harkar bunkasa Nijeriya baki daya.
Wadannan matsaloli na tsananin talauci da yunuwa da kuma rashen tsaro a fadin kasa ya ingiza da yawa daga cikin matasanmu fadawa aiyyukan aikata laifufuka, har ma fadawa harkokin taaddanci. Garuruwa da dama na zaune ne cikin tsoro saboda aukuwar rikice rikice da fashi da makami da garkuwa da mutane.
Sanata Saraki ya kuma tabo bangaren tattalin arzikkin kasa kuma, shugaban majalisa dattijai Bukola Saraki ya bijiro da bukatar gaggauta farfado da komatsar tattalin arzikin kasa don asamu Nijeriya ta fara tafiya yadda ya kamata, don kuwa a halin yanzu, yawan marasa aikin yi ya karun fiye da duk wani lokaci a tarihin kasae nan,a kullum sai wani dan Nijeriya ya rasa aikinsa.
Ya kuma ci gaba da cewa, ‘A halin yanzu kasar nan ta rabu fiye da duk wan lokaci, jama’ar kasar anan sun rabu ta bangaren yankunan da suka fito da bangaren addini da kuma kabilanci, an kuma a rabu a bangaren talakawa mara sa karfi da kuma bangaren masu hanu da shuni, gaba daya kasar ta rabu gida gida fiye da duk wani lokaci, a kwai bukatar yin wani abu don kawo karshen wannan halin a cikin gaggawa.
Kasancewar wadannan matsalolinna cikin zuciya tad a kuma bukatar amsa kiran dimbin matasan Nijeriya ya sa zan ayyana kudurina na ke kuma sanar da shiri na na shiga takarar kujerar shugabancin tarayya Nijeriya a zaben gama gari dake tafe a shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, ina yin haka ne tare da tabbacin cewa, ina da duk abin da ake bukata na kai Nijeriya da ‘yan Nijeriya tudun mun tsira”.
Daga nan sai shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya shiga bayyana shirin da yake da shi ga ‘yan Nijeriya in har ya samu kaiwa ga zama shugaban tarayya Nijeriya, da farko dai ya ce, zai tabbatar da an gudanar da tsarin gwamnatin da dukkan dan Nijeriya zai san a nan harkar gwamnati don kuwa da kowa za a tafi don a tsira tare.
“Zan tabbtar da an gudanar da gwamnatin da matasa za su bayar da gudumnmawar daya kamata, gaba daya zan gudanar da gwamnati ne da zai zama na masu jini a jika, gaba daya za mu gudanar da gwamnati na matasa masu basira da kirkire kirkire, ta hanyar samar wa da matasa jari don su gudanar da dukkan sana’o’insu da kuma bayyana basirar da Allah boye a cikinn zukatansu.
Ina da shirin sake fasalin hukumomin tsaron kasar nan da kuma samar musu da dukkan kayan aiyyukan da suke bukata na samun nasarar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya.
Na yi shirin kare dukkan ‘yan Nijeriya tare da kare dukan hakkokinsu dake a cikin kundin tsarin mulkin kasa nan, zan kuma tabbatar da ana gudanar da komai a karkashin doka da oda.
A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuma, ba zamu yi shi ta hanyar zabe ba da kuma yin bita da kulli da abokan adawar siyasa, amma lallai ina sane da cewa, yaki da cin hanci da rashawa shi nne kashin bayan bunkasar tattalin arzikin kowanne kasa a fadin duniyar nan.
Ina da yakinin cewa, Nijeriya na bukatar shugabanni da za su yi alfahari dasu, inda za sun iya daga kai a fadinn duniya su buga kirji a matsayinsu na ‘yan Nijeriya, irin wannna tsarin shugabancin zan kawo a Nijeriya in na kai ga darewa karagar mulkin kasar nan.
Wannan kuma a cikin sauki zan iya samar da irin wannan shugabanci, a matsayi na na gwamna jihar har na shekara 8, kuma a halin yanzu ia shugabancin majalisar dattijai na tarayyar Nijeriya. Wadanna mukamai sun sa zan iya gudanar da aiyyukan ofishin shugaban kasa ba tare da wani matsala ba.
Ina kara tabbatar muku da cewa, za a samu sauyi mai ma’ana in har na zama shugaban kasa, don kuwa zan yi mulki ne tare da kuduri kawo ci gaba a kasar nan, na kuma yi alkawarin cika dukkan alkawuran da muka yo ba tare da barin ko daya ba.
Na zabi kasancewa tare da ku a wannan lokaci ne saboda kune abokan tafiyata, domin kuwa matasa su ne abin alfaharin wannan kasa, gudummawarku ne zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan baki daya, a saboda haka nike kira gareku da ku hada hannun ku mika mani ragamar tafiyar da wannan kasa tamu Nijeriya, Allah Ya taimake mu gaba daya.
Da wannan jawabin ne Dakta Abubakar Bukola Saraki da dora harshashin yakin neman zabensa na zama shugaban kasar Nijeriya, a zaben da za a gudanar a shekarar 2019.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: