Zaben 2019: DSS Ta Yi Barazanar Kame Masu Shirin Tayar Da Fitina

Jami’an tsaro na sashen DSS sun sha alwashin dirar wa duk wasu masu aikata laifuka da masu taimaka masu a lokacin zaben da za a fara a wannan Asabar din.
Cikin sanarwar da Kakakin hukumar ta DSS, Mista Peter Afunanya, ya fitar a ranar Litinin, jami’an na DSS sun yi alkawarin mayar da wannan zaben karbabbe ga dukkanin Jam’iyyu da magoya bayansu.
Afunanya ya ce, “Hukumar mu ta sha alwashin ganowa da kama dukkanin masu laifi tare da iyayen gijin su, wadanda ba sa nufin ganin an gudanar da babban zaben lami lafiya a cikin kwanciyar hankali.
“Hakanan kuma, hukumar mu ba za ta amince da yada labaran karya ba, da yin kalaman batunci da nufin harzuka rikicin kabilanci ko na Addini da kalaman son rai irin na siyasa.
“Muna gargadin duk masu nufin karya doka da su guji aikata duk abin da zai iya jawo rashin tsaro da tashin hankali a cikin kasa.
“Hukumar mu ba za ta zura ido tana ganin batagari suna neman tayar da rikici a cikin kasa ba.”
Hukumar ta DSS tana yin roko ga ‘yan siyasa da masu jefa kuri’a, masu sanya ido, jami’an zabe, manema labarai, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran su da su kasance masu bin doka.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar mu ta yi aniyar samar da cikakken tsaro a bakidayan lokacin gudanar da zaben.

Exit mobile version