Daga Abubakar Abba, Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da goyon bayan mafi yawancin gwamnonin jam’iyyar (APC) da kuma ministoci kan ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
El-Rufai ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa jim kaban da kammala ganawar da ya yi da shugaba Buhari a fadar ta shugaban kasa.
Ya ce, “in dai akan takarar shugaba Buhari ce a shekarar 2019, a nawa ra’ayin, shugaban ya samu cikakkiyar lafiyar da zai iya kara tsayawa takarar, kuma burina da addu’a sune ya tsaya takarar.”
Sai dai gwamnan ya karyata labaran kanzon kuregen da ake yadawa akanshi da ke cewa ana renonsa ne don ya gaji shugaba Buhari a kakar zaben shekarar 2019.
Gwamna Nasiru El-rufa’i ya cigaba da cewa, “A matsayina na dan gani kashenin shugaba Buhari. Bani da wani burin neman kujerar shugaban basa kamar yadda ake ta yamibibi dani akan hakan, tun lokacin da nake rike da mukamin ministan Abuja da kuma bayan na bar aiki na Ministan a shekarar 2017 ake ta irin wannan yamibibin.”
Gwamnan ya ce, “Abin da nake son in sanar da duniya shi ne, ban taba zama dan takarar shugaban basa ba, haka nan ban taba zama dan takarar gwamna ba. Na zama gwamna ne a bisa ikon Allah kuma don shugaba Buhari ya ce in fita in tsaya takarar.”
Da aka nemi jin ra’ayinsa akan furucin kwanan baya da ministan mata da walwalar jama’a Aisha Alhasan tayi na cewa ba za ta goyi bayan Shugaba Buhari a zaben 2019 ba, idan har ya tsaya takara. El-Rufa’i ya ce, furucin nata ba wani abin mamaki bane.
Ya ce, “ Ban yi mamakin hakan ba, domin a matsayinta ‘yar Najeriya kuma mutum, tana da damar ta fadi albarkacin bakinta sannan ta kuma goyi bayan wanda take so.”