Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Ina Tsoron Karfin ’Yan Adawa, in ji Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da karfin mulkin da yake da  shi yana tsoron kare gwamnatinsa musammam a gurin ‘yan adawa.

Buhari ya ce gwamnatinsa na fama da makarkashiya ta kowane bangare daga ‘yan adawa, wadanda kuma hana su kulla irin wannan makarkashiya abu ne mai wahalar gaske.

Ya fadi hakan ne a fadarsa da ke Aso Rock Billa a Abuja  jiya Juma’a lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar yada manufar Buhari ta kafar sadarwar zamani wato Buhari Media Organisation.

Haka kuma shugabn kasar ya ci gaba da cewa, abu ne mai wahalar gaske  masoyansa su iya kare gwamnatinsa musamman a wurin ‘yan adawa..

Ya jinjinawa kokarin mambobin kungiyar na bayyana manufar gwamnatin ta sa duk da matsananciyar wahalar da suke sha musamman a wajen ‘yan adawa.

“Na san kuna yin matukar kokari wajen gudanar da ayyukanku, kasancewar abin da kuka sa a gaba abu ne mai wahala. Domin ba abu ne mai sauki ba, a yi kokarin fahimtar da jama’a kan inda wannan gwamnati ta sa gaba musamman ma lokacin da kuke kokarin kare ni.

“Na san wannan gagarumin aiki da kuke yi babu wanda ya isa ya biya ku, aiki ne na sadaukarwa, sakamakonsa na gurin Allah. Domin aiki ne da kuke yi da karfinku da kudinku da kuma tunaninku.

“Duk da cewa, ‘yan adawa na ci gaba da yi wa wannan gwamnati zagon kasa, ba zai sa mu fasa abin da muke yi ba,” .

Shugaban kasa Muhammadu Buhai, tare da sakataren gwamnatin tarayya Mista, Boss Mustapher (na 6 daga dama) da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari lokacin da mambobin kungiyar Buhari Media Organisation karkashin jagorancin Mista Austin Buraimoh ( na 5 daga dama) a state House da ke Abuja.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: