Zaben 2019: INEC Ta Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta kawo mata dauki a dai-dai lokacin da ta ke shiye-shiryen zabe a shekara mai zuwa. Farfesa Yakubu ya mika wannan bukata ne yayin da kwamitin majalisar Dinkin Duniya mai lura da bukatar da ake da shi na zaben 2019 ta kawo masa ziyara.

Shugaban INEC ya ce Hukumarsa na bukatar taimako a bangaren horas da ma’aikata da fadakarwa da ilimantar da masu zabe da kuma tsarin dokokin zaben. Ya kuma nemi taimako a bangaren ilimantar da jam’iyyun siyasa da warware rikice-rikice da kuma yadda za a samu shigowar mata da matasa da mutane masu nakasa a fagen harkokin siyasar kasar nan. Ya kuma lura da cewa, UN ta dade ta na taimaka wa hukumar INEC wajen samun tsarin zabe karbabbe a Nijeriya.

Farfesa Yakubu ya ce Hukumarsa a shirye ta ke ta dora akan abin da wanda ta gada ya yi na gudanar da zabe ba tare da magudi ba kuma zuwa yanzu hukumar ta yi wa wadanda suka cancanci yin zabe Miliyan 74 ragista. Ya ce, a kwai rufar zabe 119,973 da mazaba 8,809 da yankunan zabe 1,553 da za a gudanar da zabe a shekara mai zuwa.

Shugaban Hukumar ya kuma kara bayyana cewa, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015 da 2015 zuwa 2019 hukumar ta samar da canje-canje a fannoni daban-daban na harkar zabe a Nijeriya wanda ya hada da yadda a ke kada kuri’a da yadda katin zaben ya ke da kuma yadda takardar sakamakon zabe ya ke kasance wa haka kuma “Mun samar da canji a wajen tattabar da kwarewar ma’aikatanmu da kuma kawo tsarin kimiyya da fasaha wajen gudanar da harkar zaben, abin da ya hada da “Card Reader” da kuma amfani da na’ura wajen lura da zirga-zirgan kayan zabe.

 

Exit mobile version