Bello Hamza" />

Zaben 2019: Jam’iyyar APC Ta Yi Alwashin Karbe Jihohi Uku A Kudu Maso Gabas

Daga Bello Hamza

Jam’iyyar APC ta ci alwashin karbe mulkin jihohi 3 na Kudu maso Gabas da jam’iyyar PDP ke mulki a zaben 2019 dake tafe.

Jam’iyyar ta kuma kara da cewa, nasarorin da shugaba Muhammad Buhari ya samu tun lokacin da ya dare karagar mulkin shugabancin kasar nan musamman aiyukan ci gaba da gwamnatin ke gudanar wa a yankin Kudu Maso Gabas ya isa ya gamsar da mutanen yankin bukatar zaben jam’iyyar APC cikin sauki.

Wani jami’in jam’iyyar ne ya furta haka a garin Abakalili ranar Asabar wajen a bikin murnar zagayowa shekara 5 da kafa bangaren matasa na jam’iyyar (Youth League, APCYL), ya kara da cewa, jihohin da zasu karbe sun hada da Ebonyi da Abia da kuma Enugu.

Shugaban Matasa Solomon Faeren, ya ce, jam’iyyar za ta cika alkawarita na lashe jihohin yankin baki daya a zaben 2019 domin tabbatar da ikon jam’iyyar APC a yankin.

A nasa jawabin, wani babban jami’in jam’iyyar a jihar Ebonyi, Mista Christian Chukwu, ya ce jam’iyyar su a shirye take su kawar da jam’iyyar PDP daga mulkin yankin gaba daya.

Mista  Chukwu wanda ya gabatar da mukala mai taken “The Role of Nigerian Youths in Nation Building,” ya bukaci matasa su rungumi harkokin siyasa domin kawo chanji.

Ya ce, yin haka zai taimaka wa matasa samun kwarewar daya kamata domin cike gurbin shugabancin kasa a nan gaba, ya kara da cewa, ci gaban kasar nan na a hannun matasa ne saboda haka a kwai bukatar matasa su rungumin tsarin siyasa domin kawo ci gaba.

“Matasa ne jigon ci gaba a kasar nan, ci gaban kasar kuma yana a hannun matasa baki daya, ci gaban ko wanne kasa yana a hannun matasa ne saboda haka a kwai bukatar ku karfafa kan ku domin cike gurbin shugabancin kasar nan a nan gaba” inji Mista Chukwu.

Ya kuma yi korafin cewa, jam’iyyar PDP mai mulkin jihar na yi wa ‘yan jam’iyyar APC barazana, amma duk da irin wadanan barazanan sai sun cimma burin su na karbe mulki.

“Manbobin na fuskantar barazana kalakala amma suna nan daram, matasan jihar Ebonyi ba zasu mika wuya ba”

“In ka lura da irin jajircewar da suke yi, zaka fahinci cewa, a shirye suke su karbi abin daya ke nasu ne na ainihi” inji shi.

Shugaban kungiyar matasan jihar Ebonyi, Mista Emmanuel Nweke, ya ce, kuniyar su a shirye take ta tabbatar da mulki na gari da fadakar da matasa da karfafa su domin su shiga harkokin siyasa da na mulki.

Ya ce, kungiyar matasan ta cika shekara 5, kuma a cikin wadannan shekarun sun wayar da kan matasa musamman na ganin sun shiga harkokin siyasa.

“Burin mu shi ne jagorancin matasa da yin aiyukan ci gaban alumma ba na biyan bukatun mutum daya a kashin kansa ba”

“Bukatar mu shi ne dukkan ‘yan jam’iyya su haba hannu su kuma dunkuke domin kawar da jam’iyyar PDP a jihohin da muke magana”

“Hadin kanmu shi zai tabbatar da ci gaban mu da kuma nasarar da zamu samu a jiharmu” inji Mista Nweke.

A nasa jawabin, wani jami’i a kungiyar matasan, Mista Okenwa Uka, ya ce, a halin yanzu matasa na a shirye domin kawo chanji na alhairi da kasar nan ke bukata baki daya.

Ya ce, jam’iyyar PDP dake jagorancin jihar ta Ebonyi ta kasa samar da jagoranci da tsarin da zai fitar da jama’ar jihar daga kungin talauci da na rashin ci gaba.

“Matasa ne za su iya kawo chanjin da ake bukata, sai dai muna kira ga dattawa da su kawo mana gudunmawar daya kamata domin kai wa ga nasara”

“Mun kudiri aikin kawo chanji a harkar shugabanci a jihar, kuma babu wanda zai iya tsayar damu harmu kai ga nasara”inji Mista Uka.

A nasu jawabin daban-daban jagorgorin jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas, Cif Austine Edeze da Cif Christopher Omo-Isu, sun bukaci matasan dasu tabbatar da sun yi ragistan katin kuri’a domin sai da shi za su iya kada kuri’a a zaben da ke tafe.

Daga karshrn taron an karrama wasu ‘yan jam’iyyar saboda jajircewar su da gudummawar da suke bayar wa ci gaban kungiyar, cikin wadanda aka karrama a kwai, Ministan Kimiyya da Fasaha Dakta Ogbonnaya Onu da tsohon gwamnan jihar Cif Martin Elechi da Ambasadan Nijeriya a kasar Peru da Chile Da kuma Paraguay, Cif Jonah Mkpuruka, da kuma wasu mutane 22.

 

Exit mobile version