Zaben 2019: Kuri’arka ’Yanci Ka!

 

Y

ana da kyau mutane su sani su kuma fahimta cewar kowanne mutum a Nijeriya kuri’a daya gareshi, kuma wannan kuri’ar ita ce ‘yancinka  idan har mun mallake ta. Ina samun kaina cikin matukar mamaki idan naga mutum mai ilimi ko wani wanda ya san me yake yi yana fadin shi ya dena zabe, ko shi ba zai yanki katin zabe ba.

A yanzu da abubuwa suka bayyana a zahiri, bai kamata ace ana samun masu irin wannan gurguntaccen tunani ba. Ya kamata mu sani, batun katin zaben nan fa yana da alaka da rayuwarmu da ta ‘ya ‘yanmu da jikokinmu, domin da wannan katin zabe ne zamu zabi Shugabanni, su kuma Shugabannin nan, su ne mas’uliyyar gudanar da al’amuranmu yake a wuyansu.

Na san da dama wasu za su yi zargin cewar ai mun gwada a baya mun gani, abinda muka zaba ba shi ne abinda ake bamu ba. Wannan ba zai iya zama dalili daga cikin dalilai da za su hana mutumyankar katin zabe da kuma yin zabe ba. Lallai a halin da muke ciki yana iya zama wajibi a garemu kowanne baligi da ya yanki katin zabe kuma ya tabbatar yayi zabe inda yana da lafiya a lokacin zabe.

Yana da kyau mu kara sani cewar, da kuri’ata da taka da tasu za’a a hada a kirga ace daya biyu har zuwa miliyan.Ta hanyar zabe ne da kuma wayar da kai kadai zamu iya samun Shugabannin da muke so da za su gudanar da al’amuranmu. A cikin miliyoyin mutanen da suke wannan kasar, mutum guda ne kadai zai iya zama Shugabanmu, kuma ta hanyar zabe zamu zabe shi.

A wannan lokaci da muke fama da magauta da ‘yan bora da kuma makiya na kusa da na nesa. To mu sani duk yawan da muke alfahari da shi, matukar bamu yanki katin zabe kuma mun fita mun yi zabe ba, to yawan ya tashi a banza, kuma mun zama taron tsintsiya babu shara.

Ya zama wajibi a garemu, mu sani yawanmu a zahiri shi ne yawan kuri’unmu. Ina amfanin muna ikirarin yawan al’umma a wannan bangaren namu, amma anje wajen zabe an mana fintinkau? Yawan ya zama yawan da bai mana amfani ba tunda an sha gabanmu.

Mu sani magautanmu, kullum hudubarsu shi ne su yanki katin zabe kuma su fita su yi zabe, domin su kamo yawan kuri’unmu, sabida sun fahimci tunaninmu na rashin son yankar kain zabe. Lallai ne muma mu sani duk wani matashi da ya kai matsayin zabe to lallai ya fita ya yanki katin zabe, kuma ya tabbatar yafita yayi zabe lokacin zabe.

Zarge zargen da muke yi a lokacin zabe, na hanamu abinda muka zaba, ko sace mana zabe, ko kawo yamutsi a lokacin zabe, galibi duk suna faruwa ne sakamakon rashin yankar katin zabe da mutane masu ilimi da tarbiyya da dama da basu yi ba, wannan ce takan baiwa batagari daga cikinmu sukan ci karensu babu babbaka a lokacin zabe, suma kuma sabida basu san kansu bane, basa tunanin makomarsu da ta ‘ya ‘yansu shekaru 30 ko 50 nan gaba.

Duk wani mai hankali kuma mai tunani, da yake kallon kasarnan, idan har bamu dage mun tashi tsaye ba akan batun zabe da kuma zabar mutane na gari. To wallahi za’a cigaba da rayuwa ne kashin dankali a kasarnan, domin kuwa masu arziki za su yi ta samun arziki su da ‘ya ‘yansu, talakawa kuwa za su yi ta shan wahala su da ‘ya ‘yansu, kusan yanzu alamu suna nuna cewar, indai kai talaka ne to ‘ya ‘yanka da jikokinka duk talakawa za su kasance, haka in kai ami ilimi ne ko wani mai arziki haka zuri’arka za su kasance.

Sauya wancan tsari na gadar talauci ko arziki yana da alaka da tsayawarmu da kuma jajircewarmu wajen ganin mun gayawa kanmu gaskiya kuma mun yiwa kanmu kiyamul laili mun yanki katin zabe mun kuma tabbatar mun yi zabe. Wannan batun zaben ko mu sani ko kada mu sani yana damfare da rayuwarmu da ta ‘ya  ‘yanmu. Jama’a mu fita mu yanki katin zabe, sannan mu zabi mutanan kirki lokacin zabe. Kuri’arka ‘yancinka.

Dole ne mu yi kira ga jama’a su zabi mutanen kirki nagari a ko ina suke, indai kai mai zabe ne ba dan jam’iyya ba, to kada wani ya rudeka da wata jam’iyya kwaya daya cewar ita ce ta mutanan kirki, in ka tafi a haka ka yaudari kanka, kuma kai ne zaka yi da-na sani kai da iyalanka, domin kune zaku shiga halin ha’ula’i idan kuka rasa abinda zaku ci ko abinda zaku biyawa yara makaranta.

Mutane su zama masu bincike da sanin ainihin mutanen da ya kamata su zaba, ba kawai bin inna rududu ba, a tsaya a duba ko ina ana samun mutane nagari da kuma batagari, tunda a cikinmu babu Umar Bin Khaddab ko Usman Bin Affan ko Aliyu Bin ABi-Talib, dan haka za’a iya samun nagari da na banza a cikinmu, a kuma ko ina.

Muna gani yadda ‘yan siyasarnan suke canza sheka daga wannan zuwa waccan, to muma haka ya kamata mu zauna mu tankade mu rairaye muga su waye wadan da suka dace da Shugabantaramu. Bin irin yadda muka yi a baya na inna rududu ba zai taba haifar mana da da mai ido ba, domin munyi kuma bamu ga wani alfanu da hakan ya haifar mana ba.

Lallai dukkan wanda ya kai lokacin zabe wato 18 to ya hanzarta ya yanki katin zabe, domin da shi ne ya cika dan kasa tabbatacce wanda zai bayar da gudunmawa wajen zabarwa da kasarnan Shugabannin da za su jagoranci tafiyar da al’amuransa, da suka shafi Ilimi, Lafiya, Noma da Kiwa, da sauransu.

Kowacce karamar hukuma akwai inda aka tanada domin yankar katin zabe, dan haka aduk wanda ba shi da katin zabe, ya bincika a karamar hukumarsa ina ne ake yankar katin zabe yaje ayi masa. Idan mun ji mun bi kanmu, idan munki bi wataran zamu yi dana sanin yadda lamura suke tafiya ba daidai ba kasarnan. Allah ya datar da mu.

 

Exit mobile version