Yusuf Abdullahi Yakasai" />

Zaben 2019: Limamin Kasar Ghana Ya Roki ‘Yan Nijeriya Su Tabbatar Da Zaman Lafiya

Babban limamin Sheikh Usman Nuhu Sha-rubutu, ya yi wannan rokon ne a wajen babban mauludin da aka saba gudanarwa a kasar Ghana domin murnar zagayowar lokacin da aka haifi Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Ya kara da cewa zaman lafiya shi ne tushen komai a kasa, ya roki ‘Yan Nijeriya da su hada kansu su tabbattar an gudanar da wannan zabe cikin zaman lafiya. Ya kuma yi kira ga musulmin duniya su tabbatar sun hada kansu tare da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da kuma sauran al’umma.
Babban limamin kasar ta Ghana, ya yaba da yadda jama’a suka halarci wannan taro daga sassa daban-daban na cikin wannan kasa da makotanta wadda ya ce Ghana kasa ce mai tarin albarka, kana ya yi addu’ar Allah ya mayar da kowa gida kafiya.
Daga cikin manyan baki da suka halarci wannan mauludin daga kasar ta Ghana akwai mataimakin shugaban kasar da kuma gwamnonin kasar da ministoci da dimbin jakadun kasashen duniya. Daga Nijeriya kuma akwai Alhaji Ali Abubakar Danmajen Agege, Sharu Ismaila, Ustaz Malam Maaza Abdullah, shugaban makarantar Islamiya ta Darul Kur’an da ke Agege, Alhaji Mohammed majidadi Faila, da sarkin samarin Agege Alhaji Iro Tafida.
A cikin jawabinsa a madadin ‘Yan Nijeriya Alhaji Ali abubakar ya yaba da dangantakar Nijeriya da Ghana ganin yadda zumunci kasashen biyu ke tafiya cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
A karshe ya gode wa babban limamin kasar Ghana Sheikh Usman Nuhu Sha-rubutu saboda kokarin da yake wajen hada kan musulmi da son zaman lafiya. Daga cikin kasashen da suka halarci wannan babban mauludin har da tawagar musamman daga kasar Senigal wanda Babban Khalifan Shehu Ibrahim Inyass na duniya, Sheikh Tijjani Inyass ya jagoranta.
Kamar yadda wakilinmu ya gane wa idonsa, an yi wannan taro cikin kwanciyar hakanli kuma abin sha’awa hatta jogororin addinin kirista wato fastoci sun halarci wurin taron, inda wannan ke nuna zaman lafiya a tsakanin bangarorin addinai a kasar ta Ghana.
Mauludin dai ya gudana ne a Unguwar Fadama da ke babban birnin kasar Ghana Accra.

Exit mobile version