Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Babbar Daraktar Mata a Majalisar Dinkin Duniya, Phumzile Mlambo-Ngcuka ta bayyana cewa akwai bukatar a karfafi mu’amalar mata a lamurran siyasar Nijeriya.
Daraktar Matan ta bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da ta yi da wakilin Nijeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Banded a mataimakin wakili, Samson Itegboje.
Misis Mlambo-Ngcuka ta ziyarci Nijeriya ne, tare da rakiyar Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammad domin kawo karshen irin matsalolin da ’ya ’ya mata ke fuskanta a fadin kasar.
Misis Mlambo-Ngcuka ta shelanta goyon bayan majalisar dinkin duniya, inda ta kare matakin da cewa maza sun mamaye komi a siyasa, sun hana matan sakat.
“Don haka zamu yi aiki da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, don cimma wannan muradi.” In ji ta.
A ta bakinta, gaba daya abubuwan da ta yi a Nijeriya, za ta koma ta mika rahoto. Wanda cikin makasudin ziyarar har da irin ayyukan da mata ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya suke yi a Nijeriya, da kuma irin ci gaba da ake samu a Nijeriya a lokacin ziyarar.
“Sannan Za mu tabbatar da mun bayar da tallafi ga ‘yan matan da aka sace – wanda kuma zamu fi mayar da hankali akan ‘yan matan Chibok. Haka kuma mun cimma nasarar bibiyan halin da matan da ke sansanin ‘yan gudun hijira ke ciki a wurare mabambanta.” In ji ta
Ta yabawa Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo bisa yadda ya ya iya rike Nijeriya a lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke Landan domin jinya.
Ta ce: “Lokacin da muka je Nijeriya mun tarad da Mataimakin Shugaban Kasa ne a matsayin mukaddashi, wanda kuma ya taimaka mana matuka wurin wannan shiri namu.
“Taimakon da ya bamu ne ma muka iya kaddamar da kamfen din marawa mata baya wanda aka yiwa take da ‘HeForShe’. Yanzun kuma da shugaba Muhammadu Buhari ya dawo, za mu sake dawowa domin mu kara kaddamarwa a karo na biyu.” In ji ta.