Connect with us

SIYASA

Zaben 2019: Mun Gamsu Da Shirye-Shiryen Hukumar Zabe -Alhaji Umaru Birnin Kebbi

Published

on

ALHAJI UMARU BIRNIN KEBBI, shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Labour, na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yammacin kasarnan, wanda ya kunshi, Kaduna, Kano, Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Jigawa. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu, UMAR A HUNKUYI, a Ofishinsa da ke Kaduna, ya yi bayani ne kan shirin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi na gudanar da babban zabe na kasa a 2019, da kuma irin shirin da ita na su Jam’iyyar ta Labour ta yi, gami da manufofinta, sannan kuma ya yi magana a kan sabon tsarin albashin ma’aikatan kasar nan, inda aka kwana da kuma matsayin da Jam’iyyar na su take a kai, a karshe ya gabatar da kiran da yake yi na musamman ga al’umman kasar nan a kan zaben.
A sha karatu lafiya:
Kun gamsu da shirye-shiryen wannan zaben ta fuskacin hukumar zabe ta kasa, kuna ganin ta shirya kamar yadda hukumar take fada?
Kwarai kuwa, mu mun gamsu da shirin gudanar da wannan zaben kamar yadda muka gani, muka kuma ji na irin abin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta shaida wa duniya ta yi, na shirin gudanar da wannan zaben. Dalili kenan da ya sanya duk dan takaranmu da ya zo mukan tantance shi mu kuma gabatar da shi, mu kuma amshi takardun shiga takara daga hukumar zaben mu ba shi ya cike su.
Amma akwai masu kokawa da kuma nu na dari-dari kan gudanar da zaben shi kansa, wasu kuma tababan gudanar da zaben suke yi a turbar gaskiya, har sukan bayar da misali da Jihar Ekiti, suna nu na an yi amfani da jami’an tsaro domin su mara wa wata Jam’iyya?
Daman haka abin yake, a duk lokacin da za a yi zabe za ka sami kowa da irin na shi ra’ayin. Ai an yi zabe a Nijeriya na gaskiya kowa kuma ya gani, a lokacin da aka zabi Buhari, ai kowa ya san an yi zabe ne na gaskiya, hukumar kuma da ta yi wancan zaben ai ita ce za ta sake gudanar da wannan zaben, don haka ban ga dalilin da zai sanya har mutane za su rika zargin ta ba. Hatta shi kanshi zaben na Jihar Ekiti, ai kowa ya ga abin da aka yi, da aka yi zabe na gaskiya ai gaskiyan ta fito ko? Don haka ni ina ganin sam bai ma kamata mu rika yin irin wadannan surutan ba, mu muna da tabbacin hukumar zabe za ta yi gaskiya da adalcin da ta yi a baya, kuma za ta yi abin da ya kamata. Wanda duk ya san ba zai ci zabe ba, to kar ma ya bata ma kansa lokaci da neman fakewa da irin wadannan surutan marasa asali. Duk wanda ya san shi na kwarai ne kuma ya yi abin kwarai yana kuma da jama’a to ya fito kawai, jama’an za su zabe shi.
To ku a Jam’iyyar Labour wadanne irin manufofi ne kuke ganin kuna da su kyawawa, wadanda kuke ganin har za ku tallata wa al’umman kasa su domin su zabe ku?
Mu abin da muka fi dogara da shi a matsayinmu na Jam’iyyar Ma’aikata shi ne, hanyoyin raya tattalin arzikin kasa, domin in kasa tana da arziki, to tana iya biyan ma al’ummanta bukatun su. Mu in har Allah Ya kaddarci muka kafa gwamnati, lallai za a sami ayyukan yi, dukkanin kamfanonin da suka ruguje za mu tabbatar da duk mun tayar da su, za mu kuma kafa sabbi, za mu kuma karfafi mutane ta yadda kowa zai sami sana’ar yi, ba tare da ya dogara da wani ba. Muna da tabbacin in an yi hakan Nijeriya za ta ci gaba, don matukar kowa yana da aiki ko sana’ar da yake yi, ba yadda za a sami wani kace-nace a cikin kasa.
Muna kuma yi wa al’umman kasan nan alkawarin cewa, tabbas za a sami ingantaccen ilimi, za a sami kuma ayyukan yi kamar yadda na fada a baya, za kuma mu tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasan nan ya karu a saman abin da ita gwamnati mai ci yanzun take yi. Za mu kuma mayar da hankalinmu ka-in-da-na-in, a kan harkar noma, domin duk kasar da ba ta iya ciyar da kanta, to ba ta da ‘yanci. Domin kamar yadda aka yi a zamanin su Sardauna, Tafawa |alewa, Azikwe, Owolowo da sauran su, ai da noma ne a wancan zamanin tattalin arzikin kasar nan ya dogara. Mukan noma gyada, koko, auduga da makamantan su, mu sayar mu sami kudaden da za a yi mana ayyuka da su, mun kuma ga ayyukan da aka yi mana, wadanda ga su nan har gobe muna cin gajiyar su. Da wadannan kudaden ne aka gina mana manyan makarantu, kamfanoni, manyan tituna, asibitoci da makamantan su, wadanda har gobe duk muna amfana da su. To muna tare da irin wadannan tsare-tsaren wadanda har in Allah Ya ba mu gwamnati za mu ci gaba da karfafa harkar noma, raya tattalin arzikin kasa, samar wa da mutane ayyukan yi, da bayar da nagartaccen ilimi da kiwon lafiya.
Wannan yana nu ni ne da cewa ba ku gamsu da yanda wannan gwamnatin ta APC ke gudanar da na ta ayyukan ba, ko kuwa dai?
Ba cewa muke ba mu gamsu ba, za mu dora ne a kan abin da su ma suke yi, mun san Jam’iyyar APC tana da tsari, to mu ma muna ganin namu tsarin ya fi wanda ita take da shi, to shi ne muke son mu dora a kan abin da ita take yi, domin a sami kyakkyawan zaman lafiya da ci gaban kasa. Domin duk mutumin da yake neman shugabanci, to bai kamata ya soki wanda yake a kan shugabancin ba, don in ya yi hakan, to shi ma in ta shi ta zo haka za a yi ma shi. Sai dai ya yi azaman in shi ma ya samu to zai kara ne a bisa abin da wadancan suke yi, to in ya yi hakan sai ya sami yabo daga wajen mutane.
To har yanzun dai babu tabbacin fara yin aiki da sabon tsarin albashi na ma’aikatan kasan nan, kamar yadda a baya can gwamnatin ta alkawarta. To ku a matsayin ku na Jam’iyyar ma’aikatan kasar nan, ya kuke ganin yanda lamarin ke tafiya?
Duk wanda ka ji yana nu na tababan tabbatan hakan, to kila dan adawa ne. ai an kafa kwamiti ne, wanda kwamitin nan kuma mu a matsayinmu na kungiyar kwadago muna cikin sa, sannan kuma kwamitin ya tara mutane ne masu hankali da lura a cikin sa. To amma abin da mutane ba su gane ba shi ne, wannan fa sabon tsarin albashin da ake magana, duk inda ta kai, ta komo, tilas ne sai Majalisar kasa ta tabbatar da shi. To amma a yanzun haka, kuma a wannan irin hali da ake ciki mai matukar mahimmanci, su ‘yan majalisun sun kulle majalisun sun ta fi hutu. Don haka ka ga duk wani abin da za a yi, tilas ne a saurara sai sun dawo, an san bisa ga hakki suna da daman tafiya hutu, to amma ina amfanin hutu in kasa na cikin halin kakanikayi! Don haka duk dan kasa mai hankali wanda kuma ya san abin da ya kamata, ya san wannan tafiya hutun na su har tsawon watanni biyu bai cancanta ba, domin ya kashe abubuwa masu yawa.
Don haka batun sabon tsarin albashi na kasa, tabbas za a yi shi, kuma cikin dan lokaci kankani ma’aikata za su ji dadin shi, amma muna masu kara ba su hakuri, saboda tangardan da aka samu a tsakanin majalisa da sashen shugaban kasa, muna fatan dai ya kamata ne a hada kai a yi wa mutane aiki. Amma maganan sabon tsarin albashi kusan an kammala, gabatarwa ne kawai muke jira.
A karshe, a dunkunle, wane kira kake da shi ga al’umman kasar nan?
Kira na ga al’umman kasa shi ne, a jajirce a yi siyasa a tsakani da Allah, a zabi mutanan kirki masu amana wadanda za su rike kasar nan, in kasa ta rayu, kowa zai rayu.
Cewa ka yi a zabi mutanan kirki, ba ka ce a yi Sak ba, ko kai ma ba ka da ra’ayin a yi Sak din ne?
A’a, mutanan kirki na ce a zaba, saboda ai muna da Jam’iyyoyi kusan 91 ne, don haka mutumin kirki ya kamata a zaba, wanda zai bauta wa kasa, wanda ya yarda da akidan talakan kasar nan ya rayu ya ji dadi, shi ya kamata a duba a zaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: