Tun lokacin da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya fara zirga-zirgar zuwa asibiti a birnin Landan, ’yan Nijeriya da dama su ke tunani da hasashen anya kuwa Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a babban za~en kasar na 2019, musamman idan a ka yi la’akari da cewa, shi ba shugaba ne mai nuna zalamar mulki ba?
Da yawa masu nazari na da ra’ayin cewa, idan har shugaban ya fahimci cewa, wasu matsaloli za su iya hana shi cigaba da tafiyar da mulkin kasar yadda ya dace idan ya zarce, to ba zai zama irin shugabannin na Afrika da ke nacewa a kan karagar mulki su ce sai su ka]ai za su iya ba, kuma ba zai zama irin shugabannin da ke tsoron barin mulki ba, don kada a tonu irin badakalar da su ke binnewa ba, domin Buhari ne ka]ai a ke yiwa la}abi da ‘Mai Gaskiya’ a siyasar Nijeriya.
Wannan dalilin ya sanya a na ganin cewa, matukar Buhari ya amince ya tsaya takara, to babu makawa zai iya lashe zaben na 2019, domin ko babu komai har yanzu ba a samu wanda talakan kasar ya fi amincewa da shi, kamar Buharin ba. Wannan ne ya sa a ke ganin cewa, idan har Shugaba Buhari ba zai yi takara ba, to jam’iyyar adawa ta PDP ta fi damar lashe zabe a kan a ce ya na yi din.
Duk da dai cewa, babu wata tartibiyar shaida da ta nuna cewa, Shugaba Buhari ba zai iya tsayawa takara ba, to shin idan a karshe ya yanke shawarar ba zai tsaya ba ]in, wa a ke ganin zai iya gadar shi a cikin ’yan siyasar Nijeriya da ke nuna alamun sha’awar kujerar mulkin kasar? Editanmu NASIR S. GWANGWAZO ya yi nazari da duba a kan wadanda a ke ganin su na da wata dama wacce za ta iya taimaka mu su wajen ganin sun cimma wannan buri. Wallahu a’alamu:
Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa kuma tsohon kwamishinan shari’a na jihar Legas, Farfesa Yemi Osinbajo shi ne wanda dokar kasa ta fi bai wa damar gadon kujerar Buhari ta fuskoki daban-daban. Kundin tsarin mulki ya yi tanadin cewa, mataimakin shugaban kasa ne zai gaji shugaban kasa idan shi shugaban ya yi murabus ko ya kasa aiki kwata-kwata a dalilin rashin lafiya ko kuma idan ta-Allah ta kasance ko a ka tsige shi. Wannan wata dama ce ga Osinbajo, wacce zai iya darewa kagarar mulkin Nijeriya, saboda ganin cewa, shugabansa mai laulayi ne. Baya ga haka kuma Barista Osinbajo ya na zaune lafiya da Shugaba Buhari ta yadda har shi shugaban ya ke iya fitowa bainar jama’a ya yaba wa mataimakin nasa. Hakan ya na nuna cewa, Buhari zai iya goyon bayan Osinbajo, idan hakan ta kama. Wani karin arashin kuma shi ne, jiga-jigan makogwaron APC mai mulkin kasar, irin su tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu su na matukar shiri da shi, baya ga goyon bayan da zai iya samu daga yankinsa na Kudu maso Yamma. Haka nan kuma kawo yanzu ’yan Arewa sun a mutunta shi.
Babbar matsalarsa it ace, idanunsa bai gama budewa da siyasar kasar ba. Don haka ba dole ne ya zamana ya na da abokan alaka na jikinsa, wadanda za su iya yi ma sa aiki na cikin gida ba. Yawancin alakar da ya ke da ita ta wasu ce, ba tasa ba ce kai-tsaye.
Bukola Saraki
Tsohon gwamnan jihar Kwara kuma shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Bukola Saraki ya na daga cikin jiga-jigan siyasar da idan an zube a faifai, zai iya kwashewa. Saraki ya kara da manyan APC, irin su Tinubu, a lokacin da ya ke kokarin zama shugaban Majalisar Dattawa, amma sai da ya yi nasara duk da cewa ba su so kuma shi ba dan takarar Shugaba Buhari ba ne. Bayan ya zama shugaban, an cigaba da cin dunduniyarsa, amma hakan bai sa an iya tsige shi ba. Hakan ya buga da mahaifinsa, Olusola Saraki, a lokacin da ya gwamnan Kwara, amma sai sa day a kayar da ’yar takarar uban, wacce yaya ce a wajensa. Hakan ya nuna yadda Saraki ya ke iya yin gwagwarmaya ya kai labarai. Don haka ba abin mamaki ba ne don ya iya samun tikitin tsayawa takara a 2019, musamman ma ganin yadda ya ke jituwa da bangaren adawa na PDP a kasar; fa’idar da babu wani mai kamar tasa a cikin APC mai mulki.
Babbar matsalarsa ita ce, ba dole ne idan ya samu takara, mutanen Shugaba Buhari su taya shi yakin neman zabe ba, saboda yadda ya bata da mutane da yawa a kokarinsa na hawa kujerar shugaban majalisar dattawa ta kasa!
Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, na daya daga cikin masu neman takarar da a ke kallon ya na da wata dama wacce zai iya yin amfani da ita wajen gadon kujerar Shugaban Buhari. Atiku ya na da yara da yawa, sannan kuma a ka ganin cewa ya na da tarin dukiyar da zai iya bankara jam’iyya ta tsayar da shi takara, matukar ba shugaban kasa ne bai son takararsa ba. To, shi kuwa Shugaba Buhari a na ganin cewa, ba zai yi karfa-karfa ba ya ce dole sai ya yi ’yar nune ba, kamar yadda ta faru a zaben shugabannin majalisar dokoki ta kasa. Bugu da kari, kasancewar ejan-ejan ne su ke yin tsaben fitar da gwani na jam’iyya, hakan zai zame wa tsohon mataimakin shugaban kasar abu mai sauki wajen samun tikitin jam’iyya tunda dai yanzu abin na musayar hannu ne. Don haka Atiku ya na da dama, la’alla a cikin APC ko a PDP!
Babbar matsalarsa ita ce, har yanzu talakan Nijeriya ya kasa yarda das hi a cikin zuciyarsa.
San Nda-Isaiah
Tsohon mataimakin daraktan yada labarai na kamfen din Shugaba Buhari a 2003 kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar APC a 2015, sannan shugaban gungun kamfanin jaridun LEADERSHIP, Mista Sam Nda Isaiah, na daga cikin wadanda su ke da wata dama ta gadar kujerar Shugaba Buhari. Babbar dammar Mista Sam ya ke da ita ita ce, kasancewar sa shi kadai ne Kirista dan Arewa da ke gaba-gaba wajen neman wannan takara. A yanzu siyasar Nijeriya bata nasara ko yiwuwa sai an hada dan Kudu da dan Arewa kuma sai an hada Musulmi da Kirista. Kasancewar Nda Isaiah ya hada wadannan abubuwa biyu, kafin 2019 za a iya samun rikicewar lissafin siyasa a kasar ta yadda za a cewa, babu mafita face a tsayar da Kirista dan Arewa takarar zabe, kamar yadda a lokacin juyin mulki na 1966 da a ka yiwa Janar Aguiyi Ironsi, tilas ta sa a ka nada Janar Yakubu Gowon shugabancin Nijeriya, saboda kasancewar shi Kirista dan Arewa, don a zauna lafiya. A kalla saboda yadda addinin Kirista ya fi rinjaye a Kudu, amma kuma ’yan Arewa sun fi yawa a kasar, zai iya kasancewa Kirista dan Arewa ta ya fi samun karbuwa a ko’ina a kasar, idan lamurra su ka hautsine, yayin da Buhari dan Arewa Musulmi ya ce ya ce ba zai tsaya takara ba, su kuma ’yan Kudu su ka ji tsoron kada dan Arewa Musulmi ya hau mulki ya ce sai ya yi shekara takwas. A kalla Sam zai iya zama raba-gardama!
Babbar matsalarsa ita ce, a na ganin cewa, idan banda Shekarau, dukkan ’yan takara sun fi shi kudi, sannan kuma jaridarsa ta jima ta na yiwa wasu manya tonon silili. Don haka wasu su na hakon shi!
Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan tsaro, sannan sanata a yanzu, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya na cikin matasan ’yan siyasa masu karsashi a Arewa, kuma tun ya na gwamna ya nuna sha’awarsa ta zama shugaban kasa, inda ya kafsa da Shugaba Buhari a zaben fitar da gwani na jam’iyya mai mulki ta APC. Wannan ya nuna cewa, ya fara jimawa ya na shirin amsar mulkin kasar kenan. Baya ga haka kuma ya na goyon bayan irinsu tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wanda zai iya yin tasiri wajen sama ma sa goyon bayan masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na Nijeriya.
Kuma alamu sun nuna cewa, idan har APC za ta iya ba shi takara, to akwai yiwuwar zai iya lashe zaben. Babbar matsalarsa ita ce ta samun ejan-ejan a lokacin zaben fitar da gwani, kasancewar hatta a jiharsa ba ya shiri da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ballantana ya sa rai da zai iya samun tikiti.
Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan Kano na farko da ya taba yin tazarce a gadon mulkin jihar kuma tsohon ministan ilimi, Malam Ibrahim Shekarau ya na daga cikin manyan ’yan siyasar da a ke ganin za su iya yin tasiri wajen samun tikitin takara na jam’iyya, kasancewar sa a cikin jam’iyyar adawa ta PDP. Ganin yadda shugabancin PDP na kasa ya yi ammanar cewa, ba domin Shekarau a cikin jam’iyyar ba, watakila da yanzu an daina maganar ta a jihar Kano, wanda hakan ba karamin nakasu ba ne, saboda tasirin Kano a siyasar Arewa, don haka jam’iyyar za ta iya bas hi tikiti a kokarin da ta ke yi na ganin ta dawo da mutuncinta, wanda ya zube warwas a yankin. Bugu da kari, mukamin da ya rike na ministan ilimi a karshen gwamnatin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya sanya malaman jami’a da dama sun yarda da shi a matsayin wanda zai iya jagorantar kasar zuwa tundun-mun-tsira, saboda yadda ya kawo karshen yajin aikin sai-baba-ta-gani da kyawawan manufofinsa.
Babbar matsalarsa ita ce kimarsa ta a idanun ’yan Arewa da dama ta fa]i, saboda ficewa da ya yi daga APC ya koma PDP a lokacin a ke fama da hare-haren Boko Haram.
Sule Lamido
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin dasashen waje, Alhaji Sule Lamido ya riga ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a 2019 cikin jam’iyyarsa ta PDP. Ganin irin jajircewarsa a siyasance da kuma dimbin aikin da ya yi a Jigawa lokacin da ya ke gwamna duk da cewa jihar ta na cikin matalautan jihohi a Nijeriya, hakan ya ba shi dammar yiwuwar ya karbu, idan har jam’iyyarsa ta tsayar das hi takara. Rigingimun da ya yi da tsohuwar gwamnatin PDP a lokacin Jonathan, wani dalili day a sanya har yanzu talakan Nijeriya na kallon Lamido a matsayin daya daga cikin ’yan siyasar da za su iya kawo ma sa mafita. Haka nan kuma alakarsa da Obasanjo za ta taimaka wa tafiyar tasa a yunkurin neman tikitin PDP.
Babbar matsalarsa it ace cigaba da zama da ya yi a PDP gabanin zaben 2015 da ya gabata.
Ibrahim Hassan Dankwambo
Gwamna jihar Gombe kuma tsohon babban akuwa na tarayyar Nijeriya, Gwamna Ibrahim Hassan Dankambo ya na da damar samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP, saboda kasancewarsa gwamna mai a babbar jam’iyyar adawa ta kasa, PDP. Hakan zai iya ba shi damar a tsayar das hi takarar, domin al’adar jam’iyyar ya nuna yadda gwamnonin cikinta ke iya sarrafa ta, kamar yadda a 2007 su ka tsayar da gwamnan jihar Katsina na lokacin, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, wanda a karshe shi ne ya lashe zaben. Ganin yadda Dankwambo ya ke takar sa’a a tsayar da shi kuma ya lashe zaben kamar yadda mu ka gani a 2011 da kuma yadda ya iya kai bantensa a 2015 ya zarce da mulki a jihar Gombe, duk da cewa jam’iyyarsa ta yi bakin jinni a yankin Arewa maso Gabas da Arewan gabadaya saboda rikicin Boko Haram, to za a iya cewa, idan har PDP ta tsayar da shi takara kuma Buhari bai tsaya ba.
Babbar matsalarsa ita ce, har yanzu mutuncin PDP bai gama dawowa a idanun ’yan Arewa ba kuma shi bai da karfin farin jinin da mafi yawan talakawa ke la’akari da shi, duk da cewa, a na ganin ya na cikin gwamnonin das u ka tabuka abin arziki a fadin tarayyar Nijeriya.
Nasiru El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya na da cikakkiyar damar zama shugaban Nijeriya saboda baya ga kasancewar sa gwamna mai ci, kuma a na ganin kamar ya fi kowa kusa da Shugaba Buhari a cikin jam’iyyarsu ta APC da kuma gwamnonin kasar bakidaya. Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa, hankalin Buhari ya yi matukar kwantawa da El-Rufai ta yadda ya na iya jin maganarsa kuma yarda da dukkan abinda ya aikata. A na ganin cewa, ko da Buhari bai da niyyar yin abu ko kuma bai fahimci abu ba har yak e kin shi, to gwamnan na Kaduna zai iya sanya way a sauya ra’ayi a kan abin. Abin nufi a na shi ne, da alama Buhari ya yarda da amanar El-Rufai da tunaninsa kamar yadda ya yarda da shugaban hukumar kwastam, Kanar Hamid Ali mai ritaya, wanda shi ba dan siyasa ba ne; tsohon soja ne kawai. Bugu da kari kuma, kwazon aikin da El-Rufai ya yi a lokacin da da ya ke rike da mukamin ministan Abuja ya ba shi damar zama mai farin jini a idanun mafi yawan talakawan da ba su zauna a babban birnin kasar ba lokacin da ya ke rike da shi. Haka nan kuma mutanen da ke wajen jihar Kaduna su na kallon a matsayin wanda ya ke aiki tukuru a jihar.
Babbar matsalarsa ita ce, ya tara makiya da yawa, saboda alakarsa da Shugaba Buhari. Don haka za su yi duk mai yiwuwa su ga cewa, bai iya gadon shugaba mai ci ba. Masu irin wannan fushi na kallon irin su El-Rufai a matsayin butulu ko kuma kaska rabi mai ji, saboda yadda ya taba kwayewa ubangidansa na farko, Atiku Abubakar, baya ya koma gindin Obasanjo a lokacin da su ka raba gari. A yanzu haka su na ganin cewa, ya na cikin masu zuga Shugaba Buhari kan wasu al’amuran siyasa a kasar!
Rochas Okorocha
Gwamnan jihar Imo kuma tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Gwamna Rochas Okorocha a yanzu shi ne kadai dan siyasar day a fito daga yankin Kudu maso Gabas na kabilar Ibo da a ke ganin ya na da tagomashi a Arewa, saboda ayyuka da shirye-shiryen gina al’umma da ya dade ya na aiwatarwa a dukkan fadin kasar, ba sai yankin day a fito kadai ba. Ikirarin da ya ke yin a cewa, shi ne cikakken dan Nijeriya ya na tasirin a zukatan mutane, saboda yadda a ke ganin a fili ya na yin abubuwa na raya kowanne yanki da dukiyarsa, kamar bide makarantu da sauransu. Idan dai za a iya tunawa Rochas ya taba yin ikirarin cewa, wasu daga kakanninsa sun fito daga Arewa ne. Baya ga haka kuma shi ne kadai gwamnan da ya lashe zabe a tutar jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas a fadin Nijeriya, sannan kuma ya ke da kyakkywara alaka da mutenan yanki, baya ga cewa ya jin babban yaren Arewa, wato Hausa.
Babbar matsalar Gwamna Rochas ita ce, zai yi wahala a zabe na 2019 a mika ragamar mulkin Nijeriya ga yankin day a fito, saboda Arewa ta na ganin ba ta gama nata zango biyun ba, sannan kuma Kudu maso Yamma, yankin Yarabawa, za su ga cewa, ai su ne su ka fi bada gudunmawa wajen kafuwar wannan gwamnati, bayan yankin Arewa.
Wadannan na daga cikin nazarin mu ka kawo mu ku. Shin ku a naku tunanin da ra’ayin wane ne ku ke ganin zai iya kai bantensa, idan Buhari bai tsaya takara ba? Za ku iya turo ra’ayinku ta wannan adireshin leadershipayaulahadi@yahoo.com ko sakon Watsapp ta wannan lamba 08039382831. Za mu ware shafi sukutum wanda za mu wallafa ra’ayoyinku a kan wannan batu mako mai zuwa in sha Allahu. Sai mun ji daga gare ku.