Zaben 2019: ’Yan Sanda Za Su Kewaye Dukkanin Gidajen Da Ake Kan Aikin Gininsu

Daga Umar A Hunkuyi

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas, Imohimi Edgal, ya ce, rundunar su za ta kewaye dukkanin wuraren da ake zubar da shara da kuma gidajen da ake kan aikin ginin su da ake kyautata zaton maboyar batagari ce, a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen rundunar na tunkarar babban zaben 2019.

Kwamishinan, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa za su yi hakan ne domin hana aikata duk wasu laifuka kafin babban zaben da ke tafe.

A cewar sa, batagari da yawa suna amfani da ire-iren wadannan wuraren a matsayin mafakan su da kuma wuraren ajiye makaman su a Jihar.

“Ba mukan kula da ire-iren wadannan wuraren ba, amma bayanan sirri sun tabbatar mana da cewa batagarin sukan boye makaman su a irin wadannan wuraren.

“Lokacin da muka kai farmaki wajen zubar da shara na Olusosun kwanan nan, mun kama sama da batagari 100 a wajen. Mun kuma samu bindigogi da albarusai da tabar Wiwi a wajen. Wajen zubar da sharar babba ne da ya kai fadin hekta 50.

“Mun yanke shawarar karbe tsaron iren wadannan wuraren ne a Legas, domin ganin an gudanar da zabe lami lafiya a 2019.

“Kan hakan mun ta shirya taruka da jami’an hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, INEC. Muna kuma ta yin nazarin wasu rahotannin abubuwan da suka faru a lokacin zabukan baya a nan Legas, domin mu gano dukkanin wuraren da suke da hadari a lokacin zaben.

“Mun kuma shawarci masu iren wadannan gine-ginen a nan cikin garin Legas da su tabbatar da batagarin ba su yin amfani da wuraren. Mun kuma yi kira ga al’umma da su tseguntawa ‘yan sanda dukkanin ire-iren wadannan gidajen da babu kowa a cikin su, wadanda batagarin ne ke zama a cikin su suna shirya yadda za su aiwatar da mugayen ayyukan su,” in ji Kwamishinan.

 

Exit mobile version