Connect with us

WASIKU

‘Zaben 2019: ‘Yan Siyasa Ku Sani Kan Mage Ya Waye’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muka fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Zuwa yanzu dai kan mutane yana kara wayewa game da sha’anin siyasa. Kadan daga cikin abubuwan da mutane suka fahimta a dan wannan tsakanin sun hada da:

–   Siyasar kasarmu kasuwar bukata ce kawai.

–   kowa ta kansa yake yi ba ta talakawa ba.

–   Babu wani tabbataccen aboki ko kuma abokin gaba, sai dai tabbataccen buri da manufa.

Siyasar bana dai ta ishi dukkan masu hankali a kan daina yin fada ko gaba da junansu a kan ‘yan siyasa, domin gaskiya an ji kunya dayawa.

Da yawan wasu sun yi gaba da juna a kan Kwankwaso da Shekarau, da yawa sun yi batanci ga juna a kan Ebeto Da Talba, Ataka Da Lado, da dai sauran su. Amma yau kowa a cikin su ba shi da wani kwarin gwiwa a kan yin adawa da dan’uwansa a kan kowanne a cikin wadannan mutanen.

A yanzu babu gabar da tafi karfi kamar ta Kwankwasiyya da Gandujiyya, Mai Allah da Dan Fari, Mallam Gambo da Mai Allah (misali ne kawai) to na Rantse da sarkin da ya busa min nunfashi, idan da wata bukatar da za ta tilasta hadewarsu to za su hade domin cikar burinsu. To in haka ne kai talaka da babu abin da za ka mora a cikin lamarin mene ne naka na zurfafawa cikin lamarin? Allah ya kyauta.

Sako daga Hussaini Abubakar Danladi, Neja.

 

  • Shawarwari Ga Matasa Masu Neman Aikin Gwamnati A Nijeriya

Salam, Editan LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ka bani dama na bayyana abin da ya ke ci min tuwo a kwarya. Abun dubawa ne kwarai yadda matasa suke shan wahala wajen neman aikin gwamnati a Nijeriya. Ina yiwa matasan Nijeriya fatan alheri a duk inda suke. Tabbas kowa da hanyar da ya zaba a rayuwa musamman a kan abun da ya shafi aikin yi. Sai dai mafi girman kalubale shi ne rayuwar matashin da ya gama karatu ya dogara da gwamnati ta ba shi aiki. Babu shakka duk wanda ya gama karatu a Nijeriya musamman a garuruwan da ba su da kasuwanci, to babban burinsa ya samu aikin gwamnati. Shi ya sa fiye da kaso sittin na wadannan matasa suna shan wahala a kasuwar aiki wato Labour market da turanci musamman ‘ya’yan talakawa wadanda ko Darakta guda daya ba su da shi a cikin zuri’arsu. Malam bahaushe ya ce “Ba a cizon mu’umini sau biyu a rami daya.” Dole sai ya samarwa da kansa rigakafi in dai yana da hankali. Gwamnati ba za ta iya bawa matasan Nijeriya aiki ba musamman irin tamu da take fama da rikici iri-iri. Shekara da shekaru matasan kasarmu suke fuskantar cikas bayan sun gama karatu, shi ya sa mafi yawancinsu suna cikin fatara da talauci. Kusan komai na wadannan matasa yana zuwa ne a makare. Yana da wahala ka samu mutum a cikin nutsuwa a kasa da shekara Arba’in da biyar saboda yana yi na rashin samun komai a kan lokaci.

Mafita ita ce, ya kamata ko wani matashi ya samawa kansa mafita tun kafin ya gama makaranta. Gaskiya yanzu ya zama tsohon tunani a ce baka da aikin yi. Duk duniya babu wanda ya fika son ci gaban ka. Mene ne amfanin Diploma ko NCE ko degree ko masters ko Ph,D idan ba za ta samar maka da hanyar da za ka rayu ba? Gaskiya a irin kasashenmu ne ake gama karatu kuma a jira gwamnati ta ba da aiki. Misali, wanda ya karanta engineering ko law ko medicine ai ba shi da bukatar ya bata shekara biyar yana jiran aikin gwamnati. Haka zalika ko me ka karanta a makaranta zai iya baka aikin yi sai dai zuciyarka ce take da rauni. Babu maraya sai rago, kuma duk wanda ya dogara da wani a duniya ya shiga uku. Gwara ka kirkirowa kanka abun yi kafin ka yi tunanin wani ya taimake ka. Su wadanda kake sa rai za su baka aiki, wallahi ba za su baka ba saboda dalilan da ba sai na fada ba. Akwai wanda ko direbansa ba zai dauke ba saboda kada ka rabu da shi, wani ma zai so a ce ya rabaka da certificate din don kada ka kamo ‘ya’yansa a lokacin da shi yayi ritaya ko ya mutu. Kowa ya auna wannan maganar tawa, don haka matasa ku yi tunani a kan makomar rayuwarku.

Duk mutumin da ya karanta Mass communication ko English yana da damar kirkirarwa kansa sana’a, kaima haka wanda ka karanta Hausa da sauransu. Kowa ya je ya rufe kansa a daki ya yi tunanin abun da zai iya yi. Mafi saukin abun da za ka fara yi shi ne siyar da iliminka saboda ilimi haja ce da ake siyar da ita. Ka kula ko taimako kake nema a kan hanya an fi taimaka maka idan aka same ka fara tafiya, ba wai ka tsaya kamar bishiya kana sakawa mutane hannu ba. Allah ya sa mu ga alheri.

Sako daga Muhammad Idris, Abuja.

07065279510

 

  • Dimokaradiyya Ba Ta Haifar Wa Da Talakan Nijeriya komi ba

Salam, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, don Allah ku bani dama in fadi irin nawa ra’ayin a kan Dimokaradiyya a Nijeriya. A zaharin gaskiya a Nijeriya Dimokaradiyyar da ake tunani akwai ta, to gaskiyar maganar banza ce. A nawa ra’ayin wallahi mulkin soja ya fi kulawa da rayuwar al’umma fiye da mulkin farin hula. Saboda duk shuwagabannin da muke da su ba su san wahalar da muke ba. Ahalin yanzu a Nijeriya babu tsaro, babu ingantacciyar rayuwa, babu ‘yancin kan da muke ikirarin mun samu, kawai yaudarar mu ake da sunan Dimokradiyya. Muna da al’umma sama da mutum million 200 amma bamu da jami’an tsaron da suka kai yawan mutum million 5 ba ma.

Mafitar mu talakawa mu cire kwadayi, mu sawa junan mu kaunar mu. Mu fito dan dole mu daina korafi kawai mu fada harkar siyasa a dama ta da mu in bahaka ba ba za a daina mana mulkin kama karya ba.

Gwamnonin Nijeriya in suka gama wa’adin mulkinsu sai su dauko yaransu na siyasa su sa a kan kujeran mulki saboda su rufa musu asirin a kan barnar da suka yi wannan kawai shi ne. Da fatan Allah ya ba mu zaman lafiya ya ciyar da kasar mu Nijeriya gaba ya kara mana son junan mu ya bamu shuwagabanni nagari. Shugaban kasa kuma Allah ya kara masa lafiya ya ba shi damar gyara kurakuren da yake cikin gwamnatinsa ya hada shi da mashawarta nagari.

Buhari Imam, Sokkwato.

07064756693
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: