Maigari Abdulrahman" />

Zaben 2019: Za A Hukunta Masu Laifi Daidai Da Doka – Shugaban INEC

Shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce, a hukunta wadanda aka kama da laifi a yayin zabe daidai da doka kamar yanda ta tanadar.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki a dakin taron kasa da kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wannan dai ya sabawa kalaman Buhari da ya yi a kan barayin kwatunan zabe yayin wani zaman jam’iyar APC a Abuja, inda Buharin ya ce, duk wanda ya saci akwatin zabe, ‘a bakin rayuwarsa’.
A nasa bangaren, Farfesa Yakubu cewa ya yi, ‘Matsayar hukumar zabe kan wadanda aka sama da aikata laifin zabe shi ne, a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada.’
Da yake magana kan rahotannin da ke yawo ka cewa jami’an tsaro na farin kaya sun kama wasu ma’aikaatn zabe, ya bayyana cewar, ‘Ba wani Kwamishina da hukumar farin kaya ta DSS ta kama. Sannan ba wani gidan Kwamishina da shi ma aka zagaye. Kwamishinonin da ake rada cewar an kama, yanzu haka (yau Talata) su na ofishinmu a nan Abuja suna aiki.’
Da yake magana kan dage zabe, Shugaban hukumar ya kara nuna damuwar hukumar da sake bada hakuri kan dage zaben da hukumar ta yi. Ya kuma bada tabbacin cewa, dukkanin matsalolin da aka fuskanta a makon da ya gabata da suka janyo dage zaben an magance su.
‘Dukkanin kayan zabe sun isa a jihohi 36 da ke fadin Nijeriya tare da babban birnin tarayya yanzu hakan nan. Ma’aikatnmu a jihohi sun fara aikin gayyato wakilian jam’iyu zuwa babban bankin kasa da ke jihohi domi tanatance kayan zaben.’ Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, ‘aikin isar da kaayn zabe a jihohi zai kasance a ranar Laraba da Alhamis 20 ga wata. Ofisoshin zabe da tantancewa kuwa za su kasance a bude a ranar Jumu’a da misalign karfe 9 na safe.’
Da yake bayani kan isar jami’an tsaro da kayan zabe a ofisoshin zabe a daren jumu’a, Farfesa ya bayyna cewa, kara horas da ma’aikatan zabe na wucin gadi kuwa zai kasance ranar jumu’a a ofisoshin hukumar da ke garuruwa.

Exit mobile version