Rabiu Ali Indabawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Zaben Cike Gurbi A Zamfara: Matawalle Ya Gargadi Yari Kan Gayyato Wasu Gwmnoni

by Rabiu Ali Indabawa
December 5, 2020
in LABARAI
2 min read
Zaben Cike Gurbi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara a ranar Juma’a ya gargadi wasu gwamnoni biyar da sanatoci bakwai da tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya gayyata gabanin taron da za’a yi Asabar a Zamfara da su kaurace wa jihar.

Matawalle ya fitar da sanarwar ne bayan ya leka dukiyoyin da barayi suka lalata yayin kamfen din karshe na yakin neman zadensa a ranar Alhamis. “Idan tsohon gwamna Yari dan gaskiya ne ga mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kamata ya fada wa mutanensa su kaurace wa zaben ranar Asabar a jihar kuma idan yana da jarumtaka ya kamata ya fuskance ni. Ni kuma zan yi maganisa kwata-kwata, ” kamar yadda ya yi kashedi.

samndaads

“Yari yana ta kuka kamar jariri kuma yana ofishin IGP yana neman a cire kwamishinan ‘yan sanda na jihar. Ya samu gwamnoni biyar, sanatoci bakwai da ‘yan majalisar tarayya goma ciki har da ministan harkokin ‘yan sanda da su zo Zamfara su taimaka masa ya ci zaben.

“Ya gayyaci ‘yan daba da suka tayar da hankali a kan mutanenmu da suka kashe biyu daga cikinsu tare da lalata gine-ginen kamfen dinmu da wasu kadarori masu yawa na mazauna jihar wadanda basu ji-ba- basu gani ba.

“Na zaci namiji ne in ya isa ya fuskance ni. Ya yi kokari ya zama mai kawo matsala ta hanyar zuga mutane don tashin hankali. Ban taba zuwa yakin neman zabe da kaina ba saboda ina so in ba wa zababbun damar zabar dan majalissar da suke. Me ya sa ba zai zo shi kadai ba zai nemi taimako daga Abuja. Yana tsoron kada mu fallasa shi kuma mu mu yi masa tsirara, ”in ji Matawalle.

Ko ma dai yaya, jam’iyyar APC ta bakin mataimakin shugabanta na shiyya a jihar Alhaji Sani Gwamna Mayanchi ya yi watsi da zargin yana mai cewa jam’iyyar PDP mai mulki ita ma ta kafa kwamitinta.

Ya ce ba su taba kai wa kowa hari ba kuma jami’an tsaro sun kasance shaidu. “Sun kafa kwamitin su kuma sun hada da masu rike da mukamai da tsaffin gwamnoni da ministoci. Ba shi da ‘yancin da zai hana namu. A zahiri, shi ne zai iya karbar bakin namu kamar yadda doka ta tanada saboda gidan gwamnati na jiha ne ba na mutum daya ba, ”in ji Mayanchi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban Sojin Sama Ya Jaddada Kudurinsa Na Tabbatar Da Tsaro Da Lafiyar ‘Yan Nijeriya

Next Post

Kyakkyawan Zato Ya Sa Abokan Takarata Yanke Shawarar Dafawa Takarata -Barista

RelatedPosts

Ministan Cikin Gida

Ministan Cikin Gida Ya Yaba Da Aikin Ginin Gidan Gyaran Hali Irin Na Zamani Da Ake Yi A Kano

by Rabiu Ali Indabawa
15 seconds ago
0

Ministan harkin cikin gida na Tarayyar Nijeriya Abdurra'uf Arebeosola ya...

Ranar 'Yan Mazan Jiya

Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Gwamnan Gombe Ya Jinjina Wa Dakarun Soji Kan Kare Nijeriya

by Rabiu Ali Indabawa
5 mins ago
0

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranci bikin...

Sanata Yar’adua

Sanata Yar’adua Ya Gina Wa Kungiyar Izala Makaranta Kyauta A Katsina

by Rabiu Ali Indabawa
10 mins ago
0

Tsohon Sanata wanda ya taba wakiltar Katsina ta tsakiya, Sanata...

Next Post
Barista

Kyakkyawan Zato Ya Sa Abokan Takarata Yanke Shawarar Dafawa Takarata -Barista

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version