Rabiu Ali Indabawa" />

Zaben Cike Gurbi A Zamfara: Matawalle Ya Gargadi Yari Kan Gayyato Wasu Gwmnoni

Zaben Cike Gurbi

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara a ranar Juma’a ya gargadi wasu gwamnoni biyar da sanatoci bakwai da tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya gayyata gabanin taron da za’a yi Asabar a Zamfara da su kaurace wa jihar.

Matawalle ya fitar da sanarwar ne bayan ya leka dukiyoyin da barayi suka lalata yayin kamfen din karshe na yakin neman zadensa a ranar Alhamis. “Idan tsohon gwamna Yari dan gaskiya ne ga mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kamata ya fada wa mutanensa su kaurace wa zaben ranar Asabar a jihar kuma idan yana da jarumtaka ya kamata ya fuskance ni. Ni kuma zan yi maganisa kwata-kwata, ” kamar yadda ya yi kashedi.

“Yari yana ta kuka kamar jariri kuma yana ofishin IGP yana neman a cire kwamishinan ‘yan sanda na jihar. Ya samu gwamnoni biyar, sanatoci bakwai da ‘yan majalisar tarayya goma ciki har da ministan harkokin ‘yan sanda da su zo Zamfara su taimaka masa ya ci zaben.

“Ya gayyaci ‘yan daba da suka tayar da hankali a kan mutanenmu da suka kashe biyu daga cikinsu tare da lalata gine-ginen kamfen dinmu da wasu kadarori masu yawa na mazauna jihar wadanda basu ji-ba- basu gani ba.

“Yari ya yi wa kansa dariya ta yadda ya zama dan aike wa gwamnoni kuma ina gargadin wadannan gwamnoni cewa Jihar Zamfara daban ce kuma ya kamata su nisanci lamuranmu su bai wa ‘yan yankin damar zabar dan takarar da suke so.

“Na zaci namiji ne in ya isa ya fuskance ni. Ya yi kokari ya zama mai kawo matsala ta hanyar zuga mutane don tashin hankali. Ban taba zuwa yakin neman zabe da kaina ba saboda ina so in ba wa zababbun damar zabar dan majalissar da suke. Me ya sa ba zai zo shi kadai ba zai nemi taimako daga Abuja. Yana tsoron kada mu fallasa shi kuma mu mu yi masa tsirara, ”in ji Matawalle.

Ko ma dai yaya, jam’iyyar APC ta bakin mataimakin shugabanta na shiyya a jihar Alhaji Sani Gwamna Mayanchi ya yi watsi da zargin yana mai cewa jam’iyyar PDP mai mulki ita ma ta kafa kwamitinta.

Ya ce ba su taba kai wa kowa hari ba kuma jami’an tsaro sun kasance shaidu. “Sun kafa kwamitin su kuma sun hada da masu rike da mukamai da tsaffin gwamnoni da ministoci. Ba shi da ‘yancin da zai hana namu. A zahiri, shi ne zai iya karbar bakin namu kamar yadda doka ta tanada saboda gidan gwamnati na jiha ne ba na mutum daya ba, ”in ji Mayanchi.

Exit mobile version