Khalid Idris Doya" />

Zaben Cike Gurbi: APC Ta Sayi Kuri’un Jama’a Da Naira 200, Inji Kauran Bauchi

Tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Bala Muhammad Kauran Bauchi ya yi zargin cewar an yi magudi wajen gudanar da zaben cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu.

Ya bayyana hakan wannan zargin nasa ne a lokacin da ke zantawa da ‘yan jarida din makadan bayan da ya kada kuri’arsa a mazabar Kofar Gidan Sarki da ke Gundumar Dan/Kungibar a Yelwan Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri.

Kaura wanda a gefe guda kuma dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP ne, ya shaida wa ‘yan jaridan cewar APC ta yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a a kwararo-kwararo da nufin karkatar da zukatan jama’a su zabi Lawan Yahaya Gumau dan takarar jam’iyyar APC a wannan zaben cike gurbin.

Ya ce; “Bayanan da suke zuwa mana, APC tana baiwa masu kada kuri’u naira 200 kacal domin su zabi dan takararsu; wannan shine bayanin da ke zuwa mana daga rumfunan kada kuri’u da daman gaske,” In ji shi

Kaura ya bayyana cewar a sakamakon yunwar da ke jikin al’ummomi musamman a karkara wannan dalilin ne ya sanya suke amsar naira dari biyu kacal don sauya ra’ayinsu don zabin wani da ake son su zaba.

Ya kuma yi bayanin cewar ba a samar ma wasu runfunan kayyakin gudanar da aikin zaben da wuri ba, wanda hakan ya janyo dan cikar ga masu kada kuri’un.

Wakilinmu dai ya shaida mana cewar an samu cinciridun masu kada kuri’a a kananan hukumomin Alkeleri, Kirfi da kuma Toro a lokacin da wakilinmu ya ziyararta, inda ya shaida mana cewar mata sun fi yawan fitowa domin dan gwala wannan kuri’ar na cike gurbin.

Zaben dai kamar yadda wakilinmu ya gano a yankunan suna gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tashin hankali ba, ya zuwa lokacin da ke aiko mana da wannan rahoton.

Exit mobile version