Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a ranar Asabar ta kame mai ba Gwamna Bala Mohammed shawara na musamman a kan Ma’aikatan Gwamnati da Harkokin kodago, Mista Abdon Dalla Gin kan zargin sayen kuri’u.
Wakilinmu ya tattaro cewa, bayan jefa kuri’arsa, ana zargin EFCC ta sami makuden kudade har Naira miliyan 1.5 a motar Dallas. An kama Dallas wanda tsohon shugaban ma’aikata ne a mazabarsa ta “Jin Dadin Jama’a” a Dass a zaben cike gurbi na Mazabar Dass da ke gudana a jihar Bauchi sannan aka mika shi ga Hedikwatar Shiyya ta ’Yan sandan Nijeriya da ke Dass don amsa tambayoyi.
Ko ma dai yaya lamarin ya sance, yayin da yake yi wa manema labarai bayani shugaban karamar hukumar Dass, Honarabul Suleiman Mohammed ya ce, an kama Dallas a yanayin da na daidai ba.
Ya ce: “An gaya min cewa an kama daya daga cikin masu ruwa da tsaki na kuma zo na tausaya masa, wanda yake yi hakan daidai ne. Ko da yake, ban tattauna da shi ba amma na ji jim kadan na ji jawabinsa da ya yi ga wasu ‘yan jaridu bayan an kama shi.
Kudin ba nasa bane, kudin na wakilanmu ne, masu dawo mana da sakamakon zabe ga jamiyyar. ”
Jami’an NIS Na Samun Horo A Kan Amfani Da Dokokin Shige Da Ficen ƙasa
Shirin yaƙi da safarar bil’adama da fasa-ƙwaurin ‘yan gudun hijira...