Zaben Cike Gurbi: INEC Ta Tura Jami’ai 1,111 Jihar Jigawa

Zaben Dan Majalisa

Daga Maigari Abdulrahman

Hukumar zabe ta kasa ta ce ta tura maáikatanta 1,111 da jami’ai 854 a zabin cike gurbi na dan majalisar tarayya da za a gudanar ranar Asabar a Gwaram, jihar Jigawa.

Mista Festus Okoye, kwamishinan zabe na kasa ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Dutse  gabanin shirye-shiryen zaben da za a gudanar.

Kwamishinan ya ce sun karbo kayan zabe daga babban bankin najeriya a Dutse, wanda duka bangarorin jamíyun siyasa, jamián tsaro da hukumar zabe su ka tantance tare da amincewa akai.

Kwamishinan ya ce za a wuce da kayan zaben zuwa ofishin hukumar zabe da ke karamara hukumar Gwaram bisa rakiyar jamián tsaro

Zaben cike gurbin dai na zuwa ne biyo bayan mutuwar dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar yankin, marigayi honarabul Hassan Kila

Exit mobile version