Zaben Cike Gurbi: Kujerar Dan Majalisar Jihar Kaduna Ta Sabon Gari Ta PDP – Ali Baba

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko, Zariya

 

An bayyna zaben cika gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta a mazabar Sabon gari a jihar Kaduna da cewar, babu ko tantama jam’iyyar PDP ce za ta sami nasara, in har aka gudanar da zaben bisa dokokin da hukumar zabe mai zaman kanta ta tsara.

Wanda jam’iyyar PDP  ta tsayar domin ya fafata da sauran jam’iyyu da suka tsayar da ‘yan takara domin tunkarar zaben cike gurbi da aka samu bayan majalisar jihar Kaduna ta daga wa tsohon shugaban majalisar Alhaji Aminu Abdullahi Shagali ya yi nukusanin zuwa majalisar kamar yadda dokar zama a majalisar ta tanada, Alhaji Ali Usman Baba ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu kan zaben cika gurbin da za a yi a ranar 19 ga watan Yunin da mu ke ciki.

Alhaji Ali Baba ya ci gaba da cewar, babu shakka, al’ummar karamar hukumar Sabon gari, musamman mazabar Sabon gari da za a fafata domin cike gurbin babu wani dalili da al’ummomin wannan mazaba za su zabi wata jam’iyya ba jam’iyyar PDP ba, domin, a cewarsa, sun san abubuwanda jam’iyyar PDP ta yi ma su daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2015.

Da kuma yak e tsokaci kan matsalolin da al’ummar mazabar Sabon gari da karamar hukumar ke fuskanta, kamar yadda ya ce, ya san matsalolin kama daga matsalolin hanyoyi da kuma yadda dakunan shan magani su ke ciki da kuma yadda ake whaladda al’umma da suke ayyukan gwamnati da kuma wadanda ke sana’o’I kamar kasuwanci da sauran matsaloli ma su yawan gaske da suke addabar al’umma a wannan mazaba.

Alhaji Ali Baba ya tabbatar da cewar, a matsayinsa na cikakken dan jam’iyyar PDP, ya fara rike mukami a gunduma ya zuwa karamar hukumar Sabon gari da aka zabe shi kansila, al’ummar karamar hukumar Sabon gari, sun san abubuwan ci gaba al’umma da aka samar, a dalilin motsinsa, sboda haka, a cewarsa, tunkarar matsalolin da ske addabar al’ummar Sabon gari, abu ne mai sauki, in har al’umma suka raka shi da addu’o’I, bayan nasarar day a ke sa ran samu.

Domin warware matsalolin da suke addabar al’umma kuwa, Alhaji Ali Baba ya ce a matsayinsa na dan majalisar da matsayinsa shi ne yin dokoki, zai tsaya, kuma tsayuwa irin na mai daka, na ganin duk wani aikin da ya shafi gwamnati, ya ce sa ido na ganin gwamnati ta yi aikin ba tare da bata wani lokaci ba, ta yadda al’ummar da suka zabe shi za su ce gwammma da suka zabe shi ya wakilce su a majalisar Kaduna.

Da kuma ya ke tsokaci kan yadda ya kasance wanda zai tsaya wa jam’iyyar PDP takarar cike gurbin, Alhaji Ali Usman hya tabbatar da cewar, dole ya jinjina wa wadanda suka nuna bukatar tsaya wa takarar, amma saboda wasu dalilai da suka gani gareshi, suka janye ma sa, domin yin takara da wadanda za su fito daga wasu jam’iyyu, sai ya ce, ya na shirye ya yi wakilcinsa da al’ummar gundumar Sabon gari da kuma karamar hukumar Sabon gari baki daya.

Exit mobile version