Idris Aliyu Daudawa" />

Zaben Da Aka Yi Ya Tabbatar Da Adamawa A Matsayin Jihar Zaman Lafiya -Ribadu

Kafin Hukumar zabe mai zaman kanta ta kai ga bayyana sakamakon zabe wanda yake da sahihanci, tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewar yadda aka tafiyar da zaben jihar Adamawa, an yi shi cikin zaman lafiya da kuma kanciyar hankali.
Saboda haka ne shi Ribadu ya yi kira da wadanda za su yi nasara da kuma masu faduwa,. a zaben da aka gabatar ranar Asabar, da cewar su yi hakuri da duk irin sakamakon da suka samu, wajenn gudunmawar da suka bada wajen harkar zaben.
Shi Darekatan al’amura na sake zabn Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar yana da yakinin cewar shine wanda zai samu nasara daga karshen, saboda za’a sake zaben shi.
“ Duk wadanda suka kasance cikin zaben da aka ranar Asabar waddab ta gabarta, ko wanne daga cikin su, ko shakka babu ya taka muhimmiyar rawa, wajen zabubbukan , don haka, sai ya yi hakuri akan duk abinda ya samu dangane da sakamako.
“ Wannan zabe ne kuma al’amarin daya shafi damukuradiyya ne, dole ne a samu wadanda suka yi nasara , da kuma wadanda za su fadi, amma kuma babbar wadda zata yi nasara ita ce kasarmu Nijeriya. Saboda haka ya fi muhimmanci mu ci gaba da kasancewa hakan, wadanda suka samu nasarar, su dauki cewar lokacin sune ya yi, ba wata maganar girman kai wanda za su dauka.
“ Wadanda kuma basu samu nasara ba, ya kamata suma su gane cewar sunnbayaer cda tasu gudunmawar, a ci gaban mulkin damukuradiyya, sais u yi alfahari da irin gudunmawar da suka bayar dangane da haka abin da kuma har ta kai mu winda muke zuwa yanzu.
“ Sai su karbi abin da suka samu, bugu da kari kuma su yi tunanin ita rayua bata tsaya ba, da yin zabe sau daya tak, saboda ai ita rayuwa ai b a anan, saboda kuwa ai ko ma b ayi nasara akai darasin da akan koya.

Exit mobile version