Connect with us

LABARAI

Zaben Fid Da Gwani: Bayan Gwamnoni Sun Yi Tutsu, APC Ta Sake Lale

Published

on

Babban kwamitin gudanarwa na Jam’iyyar APC ya amince da gudanar da zaben fid da gwani na kai tsaye wajen fitar da dan takarar Shugaban kasan ta, wanda hakan ke nufin daukacin ‘ya’yan Jam’iyyar ne masu katin shaidar Jam’iyyar za su gudanar da zaben a duk fadin kasar nan, a maimakon hanyar baya da ake bi inda wakilai biyar-biyar daga mazabu suke taruwa domin gudanar da zaben, a sa’ilin da Jihohi suna da zabin yanda za su gudanar da na su.

A baya dai karamin kwamitin ya nemi da a gudanar da zaben ne a dukkanin matakai na kasa da kuma na Jihohi. Amma a taron Jam’iyyar na yau Alhamis, Jam’iyyar ta amince wa Jihohin da su gudanar da na su zaben kamar yadda suke ganin ya dace da Jihohin na su.

Sai dai, Jam’iyyar ta bukaci duk Jihar da take son gudanar da zaben fid da gwanin na kowa da kowa da tilas ne ta rubuta wa shalkwatar uwar Jam’iyyar bukatar ta na yin hakan.

Wannan dai shi ne shawarar da babban kwamitin Jam’iyyar mai daraja na biyu ya cimma wa a wajen babban taron da Jam’iyyar ta gabatar ranar Alhamis a Abuja.

Tun da farko, gwamnonin Jam’iyyar shida sun shaida wa uwar Jam’iyyar cewa, su fa ba su amince da gudanar da zaben na kai tsaye ba.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu a ranar Alhamis cewa gwamnaonin shida wandanda ba a bayyana mana sunan su ba, sun yi wani taro da shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole, a kan hakan, inda kuma suka shaida masa rashin amincewar su da hakan.

Majiyar wacce ba ta so mu ambata sunanta ba saboda girman maganar, ta bayyana mana cewa, cikin gwamnonin shida da suka sadu da shugaban Jam’iyyar, biyu sun fito ne daga Jihohin arewa ta tsakiyar kasan nan, daya kuma daga sashen arewa maso yamma, daidaya kuma daga yankunan kudu maso gabas da kuma kudu maso yamma da daya daga kudu maso gabashin kasar nan.

Majiyar tamu wacce jigo ce a cikin Jam’iyyar ta APC, ta shaida mana cewa, “Sun shaida wa Oshiomhole cewa, su ba su amince da gudanar da zaben fid da gwanin ta wannan hanyar ba, inda duk cikansu in baccin gwamnan da ya fito daga arewa maso gabashin kasar nan, cewa suka yi suna da matsaloli da mutanan su, wanda hakan zai iya samar da yiwuwar su da sauran ‘yan takarar da ke bayansu ba za su iya samun tikitin takarar Jam’iyyar ba.

“Sun kuma bayyana tsoron su na cewa, akwai yiwuwar Jam’iyyar ta APC ba za ta iya sake cinye Jihohin na su ba, in har Jam’iyyar ta yi amfani da wannan tsarin a wajen fid da gwanin na ta a Jihohin na su.”

Tun da farko, Shugaba Buhari ya gabatar wa da taron ka’idoji 10 wanda tilas ne duk Jihar da ta amince da gudanar da zaben fid da gwanin na kai tsaye ta yi aiki da su. Inda a ka’ida ta biyar shugaba Buhari ya koka da cewa:

Duk da yunkurin sasantawa da aka yi ta yi na ganin ba a sami wata rarraba a cikin Jam’iyyar ba, akwai wasu ‘ya’yan Jam’iyyar da suka dage wajen ganin sun rusa Jam’iyyar. Sun fice daga Jam’iyyar, suna ta kuma shirya makircin da za su ga sun iya tafiya tare da wasu ‘ya’yan Jam’iyyar. Amma a sakamakon tirjewar da sabbin shugabannin Jam’iyyar tamu suka yi, ficewar na su sai ya kasance bai girgiza mu da komai ba, domin ba su iya kwashe adadin da suka yi zaton za su iya kwasa ba, musamman a cikin Majalisun mu biyu na tarayya. Inda har yanzun dai Jam’iyyar namu ce ke da rinjaye a cikin su, kuma karfin na ta ma karuwa yake yi a kullum, inda nagartattun mutane ke kara shigowa cikinmu.

A ka’ida ta 9 kuma shugaba Buhari cewa yay i:

Sannan kuma tilas ne zaben fid da gwanin namu na kai tsaye da za mu gudanar ya kasance ya dace da dokokin da tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, da kuma dokokin zabe gabadaya kuma da dokokin da tsarin mulkin hamshakiyar Jam’iyyar na mu ta APC, suka tanada.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: