Connect with us

SIYASA

Zaben Fid Da Gwani: Fid Da ’Yan Takara Ta Hanyar Kato A Bayan Kato Ne Mafita

Published

on

Duk wasu rikita-rikitar da ka ga ana yi a siyasar Nijeriya an kirkire su ne, hakanan duk wata barnar da ka ga ana yi a cikin al’umma shiryayya ce. Wannan kalaman sun fito ne daga bakin Dakta Shehu Abdulmumini Makarfi, kwararren likita kuma dan siyasa a Jihar Kaduna. Ya yi kalaman ne sa’ilin da ya gayyaci LEADERSHIP A YAU, ofishin sa da ke Kaduna, Dakta Makarfi ya bayyana asalin gayyatar shi ne ya yi kira ga al’umma musamman matasan kasar nan kan su guje wa duk wani nau’in tarzoma da tayar da hankali da sunan bangan siyasa. Sannan kuma ya yi tsokaci kan shawarar da uwar Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta yanke, kan abin da ya shafi hanyar da za a gudanar da zaben fitar da gwani. Sun tattauna ne da wakilinmu, Umar A Hunkuyi. A sha karatu lafiya:

Kira Na Ga ‘Yan Bangan Siyasa

“Alamomin da ke wakana a halin yanzun inda har yanzun wasu matasan ba su fahimci baragurbin ‘yan siyasan da sukan kai su su baro ba, masu zuga su da ingiza su suna tayar da hankali a cikin al’umma duk da sunan bangar siyasa. In a ce wannan wata matsala ce da ta zo hakanan, wannan tana da saukin warwarewa, amma dukkanin barnar da ta sami al’umma, wannan an shiryo ta ne, da gangan aka kitsa ta, to ita ce take da matsalar warwarewa. Amma wacce hakanan ne ta zo, Allah ne Ya saukar da ita, to in an so a yi maganinta wannan abu ne mai sauki, sai ka ga nan da nan an yi maganin ta, amma duk wata tirka-tirkan da kake ganin tana faruwa a siyasar Nijeriya, to ma fi yawanci shirya ta ne aka yi, domin a cimma wasu manufofi na son zuciya, ko kuma domin a rufe wata almundahanar da ta jima tana gudana wacce kuma ba a son a sani.

Abin takaicin kuma shi ne, ma fi yawancin wadanda suke a kan madafun iko a halin yanzun su ne mabarnatan, wannan shi ke kara rikirkita al’amarin, na yi barna, ga kuma wani yana son ya bayyanar da barnar da na yi, ya kuma dakatar da ita, ya kuma saita kasa, to wannan shi yake janyo duk mabarnaci ya tashi tsaye don ganin barnar nan na shi ba ta bayyana ba, ko kuma ba a dakatar ma shi da ita ba. To kuma kila ba shi kadai ba ne mabarnacin, akwai sauran ‘yan’uwansa mabarnatan.

 

‘Yan siyasa masu Canza Sheka

To wannan fa shi ya haifar da yadda ake ta rikice-rikice, ka ga wannan ya tsallaka nan wancan ya tsallaka can a tsakanin Jam’iyyu, saboda kowa dole ne ya nemi abokin burmin sa, watau kwarya ta bi kwarya.

Abubuwa ne da suka jima suna gudana a kasarnan, na almundahana, son zuciya da take hakki. to sai yanzun ne Allah Ya kawo lokacin da aka fara farkar da jama’a su ka fara gane cewa ga abubuwan da suke faruwa. Yanzun ta kai ma, a kasarnan idan ka ce mutum ya saci milyan biyu, ba ma mai tsayawa sauraron ka, yanzun har an fara daina maganan satar milyoyi, an koma sai dai maganan satan bilyoyi, ana ma ambatan satan triliyon!

Mafitar mu kadai daga cikin irin wannan yanayi shi ne, da farko addu’a, kamar yanda muka saba muna addu’an Allah Ya ba mu jagora  da ma sauran shugabannin sassa nagari, ya kamata mu kara dagewa a kanta. Na biyu, mu cire son zuciya, mu natsu, mu kalli abubuwa da idon basira.

 

‘Yan Siyasan Baka

Duk mutumin da ya zo ya ce maka, bari na ba ka dan wani abu ka zama fitinanne, ko kuma ga kudi domin ku aikata abin da kun san cewa wannan abin ba daidai ne ba, ko zai iya taba mutuncin wani, ko da kuwa ta fuskacin magana ce, domin wai a yau, har akwai wasu da ake kira da ‘yan siyasar baka, wadanda in an biya su za su iya taba mutuncin duk wanda ma ba ka zato, ka ga wannan abin bai dace ba. Ya kamata mu gane kasarnan kasarmu ce, kuma baya gare ta ba inda za mu je.

In kuma a yau ka janyo barna, to fa kai ma ba barinka za ta yi ba, don haka ya kamata mu natsu mu gaya wa kanmu gaskiya mu dawo mu yi abin da ya dace. Matukar mun san mutum mabarnaci ne, to ai muna da katinmu na zabe, ba sai ka yi surutu ko ka ci mutuncin wani ba, sai ka zabi mutanan da ka tabbatar da sun dace domin ci gaba da bin kyakkyawar turban da aka dora kasarnan a kai.

Sak, Ko Zaben mutanan Kirki

Ni a fahimta ta, yanda muka yi zaben inna-rididi a wancan lokacin shi ne ya haifar mana da sakamakon abin da muke cikinsa a halin yanzun, muka kwaso kara da kiyashi mai kyau da marasa kyau, na kware da mugu duk muka tasa su a gaba. Ya kuma zamana mutanan banzan ma su ne suka fi yawa, ta yadda duk wasu tsare-tsare da ma gwamnatin ta yi domin talaka ya ji dadi ya samu ci gaba, sai su rika take su suna murjewa. Don haka ga duk mai hankalin a halin yanzun, maganan a yi Sak din nan ya kamata a duba ta da kyau da kuma idon basira.

Sai dai kamar yanda na fada a baya, mutanan da ke da matsala iri guda sukan kokari su kusanci junansu. Don haka a yanzun tafiyar kusan ta zama kashi biyu, yanzun kamar a ware aka yi, wannan kuma addu’o’i ne suka yi aiki, sai ya kasance duk masu matsala iri guda sun koma wuri guda sun dunkule, wannan kuma Kukan Kurciya ne, mai hankali shi ke ganewa. In kana da hankali da zaran ka ga mutane masu halin banza a wuri guda, to maganan ma ka kula su ba ta taso ba, yanzun sai ka duba a nan cikin gida ka nemi na kirki ka zaba.

 

Zaben Fid Da Gwani

Amma sai dai kuma siyasa tana da wani abu guda, yawanci a wajen zaben fitar da gwani ne ake samun matsala, domin a wajen a dauko mutumin da ya fi cancanta, nan ake samun tangarda. yanzun ka ga uwar Jam’iyyar APC, cewa ta yi in an zo zaben fitar da gwani na mukamai, to duk wani wanda yake dauke da katin Jam’iyya ne ya kamata ya zo ya zabi wanda zai shugabance shi, amma sai ga wasu sun ja da baya sun ce, a’a, su sam ba su yarda da wannan ba. Su wai sai kawai a nada masu wasu wakilai da ake kira, Delegate, kamar yadda aka saba a baya.

Alhalin in har za a ce maka wannan shugabanka ne, to kamata ya yi a bar ka, ka darje da kanka. Don haka, gasikyar magana in dai har za a yi adalci, to kamata ya yi a bar duk wani dan Jam’iyya wanda ke da katin shaida, ya darje ya fitar da wanda yake son ya shugabance shi. Wannan ita ce gaskiyar magana.

Amma a ce a zabi wasu mutane kalilan da za a lullube su a daki ana sanya masu farashi daban-daban, kamar yanda aka saba yi a baya, to wannan tamkar an kashe maciji ne amma ba a sare kan ba. Domin kenan matsalar dai tana nan, domin karshe farashi za a sanya masu, su kuma su bijiro da wanda bai dace ba. Wanda kuma in sun yi hakan, ita uwar Jam’iyya ba abin da za ta iya yi, hakanan za ta dauko shi da karfin tsiya ta dankara wa mutane. Amma kuwa in da ace tun farko zabin al’umma ne, to mawuyaci ne ka ga an fitar da na banza, sai dai ka ga ana tafawa. Domin an fitar da mutumin kirki wanda kuma ba zai yi wuyan tallatawa da kuma saidawa ba, wanda kuma ya san ga hanyar da aka bi aka zabe shi, ba kudin shi ne suka kai shi wannan mukamin ba,  don haka ba zai yi wasa ba.

 

Kan Shawarar  Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna

To duk da ban san ko me ita uwar Jam’iyya, ko kuma in ce gwamnatin Jihar Kaduna ta kalla ya sanya ta ce ba za ta bi wannan hanyar ba, wacce tabbas mu muna ganin ita ce ta fi dacewa. Amma dai ko ma mene ne, kowa ya san gaskiya a duk inda take. Amma mu dai ‘ya’yan Jam’iyya muna ganin a bar dukkanin ‘ya’yan Jam’iyya su fito su zabi wadanda suke ganin su suka dace, wannan shi ne gaskiya. Amma idan aka ce za a yi cushe, tabbas akwai matsala babba kuwa. Irin wannan rufa-rufan kuwa shi ke sanyawa a sami matsala a cikin Jam’iyya, gaskiya dai guda daya ce, kuma ba ta neman ado, in har ka san kana da al’umma sun kuma amince da kai, kuma su ne za su yi zaben nan, to a bar su, su zo su zaba mana.

Muna fatan kuma uwar Jam’iyya ta canza tunani a kan wannan shawarar na ta, domin har yanzun lokaci bai kure mata ba.

PDP Ta Sake Nada Walid Jibrin A Matsayin Shugaban Amintattunta

Jami’yyar PDP ta sake nada Walid Jibrin a a matsayin shugaan kwamitin amintattunta har na tsawin shekara 5. Alhaji Jibrin ya fito ne daga jihar Nasarawa, an kuma nada shi ne a karon farko a cikin shekarar 2013.

Sanarwa wannan nadin ta fito ne ta hanjun shugaban da kan sa a ranar Litinin din nan. An kuma sake tabbatar wa tsohon shugaban majalisar dattijai, Adolphus Wabara, matsayin Sakataren Kwamitin amintatatun na tsawon shekara 5.

Alhamtis ne kwamiti ta yanke wanna shawarar don a samu cikakken ci gaba a cikin jam’iyar.

Ya tabbatar da cewa, an sake nada shi a matsayin shugaban kwamtimin amintatatu na tsawon shekara 5 a taron da aka gudanar.

Ya ce, tarron ya bayar da shawarar cewa, ya kamata dukkan ‘yan kwamiin su tabbatar da mutumcin su tare da kasancewa ‘yan ba ruwanmu a yayin gudanar da harkokin ‘yan jam’iyyar, musanmman a wanna lokacin da ake shirin shiga babban taron jam’iyyar inda a za a fid da ‘yan takara da asu daga tutar jam’iyar a zabe mai zuwa.

Shugaban kwamitin amintattun ya kuma gargadi ‘yan PDP a kan su yi taka tsantsan wajen tafi da harkokin masu canza sheka zuwa jam’iyyar, su kuma lura da gudummawar da tsaffin ‘yan jam’iyyar suka bayar tun kafuwar jam’iyyar.
Advertisement

labarai