Zaben Fidda Gwani: ’Yan Takara A Bauchi Sun Nemi APC Ta Dawo Musu Da Kudadensu Na Fom

Wasu ‘yan takarar da suka nemi jam’iyyar APC ta tsaida su neman kujerun ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi da suka hada kansu a karkashin kungiya mai suna ‘Bauchi State Assembly Aspirants Forum’ wadanda suka fadi a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta yi, sun bukaci uwar jam’iyyar APC a matakin kasa da ta soke zaben fitar da gwani na majalisar jihar Bauchi ko kuma su dawo musu da kudadensu na fom din nuna sha’awar takara da suka biya.

Da take magana da ‘yan jarida, Kakakin kungiyar ‘yan takarar da suka sha kayen, Honourable Aishatu Haruna wacce aka fi sani da ‘Gimbiya’ ‘yar takarar da ta nemi shiga majalisar don wakiltar mazabar Zungur/Galambi ta shaida cewar babu wani zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar ta Bauchi, inda ta yi zargin kawai jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen wadanda za su tsaya takara hadi da mika wa hukumar zabe ta INEC.

Ta ce, “Mun sayi foms a wajenku, kun yi mana gwaji na tantance har Allah ya sa muka samu sahalewa ba tare da wani matsalar da kuka ce kun samu daga gare mu ba. mun zaci za ku guduanar da adalci a tsakanin kowani dan takara a lokacin gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar. A zahirin gaskiya babu wani wajen da aka gudanar da zaben fitar da gwani na ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi, abu daya da muka gani kawai shi ne jam’iyyar ta fitar da jerin sunaye, nadi kenan aka yi,” Inji ta

“Muna kira ga shugaban jam’iyyar APC na kasa da uwar jam’iyyar ta kasa, hadi da shugaban kasa Muhammadu Buhari da su shigo cikin lamarin domin wanzar da adalci. Abun da muke bukata shi ne a fara soke zaben da aka ce an yi, ko kuma jam’iyyar ta dawo mana da kudadenmu da ta amsa a hanunmu,” Inji ta

‘Yar takarar ta shaida cewar hatta zaman tattauna da gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce zai yi da ‘yan takarar don ganin yadda za a dan sauko da matsalolin carar da wadanda suka fadin ke ta yi, da cewar har yanzu babu wani zama da gwamna ya kirasu kawo yanzu, inda ta shaida cewar gwamnan ya bayyana cewar zai yi kokarin shawo kan matsalar da ke akwai amma shiru.

Idan dai ba ku mance ba, a makon jiya ne muka kawo muku labarin da ke cewa su wadannan ‘yan takarar da suka sha kayen sun baiwa uwar jam’iyyar wa’adin kwanaki hudu da ta soke zaben fitar da gwanin majalisar jihar Bauchi, inda ma suka nemi cewar muddin aka ki yi musu hakan da iyuwar su dauki matakin ficewa daga cikin jam’iyyar.

Kawo yanzu dai sun nemi a dawo musu da kudadensu da suka biya na sayen fom din nuna sha’awar tsayawa takarar majalisar jihar a karkashin jam’iyyar APC, ‘yan takarar da suke wannan korafin sun ayyana kansu da cewar za su haura 110 zuwa 120 wadanda dukkaninsu suka nemi kujerun majalisar jihar Bauchi daga sassa daban-daban na jihar ta Bauchi.

Exit mobile version