Bello Hamza" />

Zaben Fidda Gwanin APC: Cikin Wasu Gwamnonin Arewa Ya Duri Ruwa

Ya zuwa yanzu cikin wasu gwamnonin jam’iyyar APc ya duri ruwa, musamman ma a arewacin Nijeriya. Sakamakon matsayar da kwamitin zartaswar jam’iyyar APC ya cimma dangane da zaben ‘yar tinke ko akasinsa.

Kwamitiin Zartaswar na jami’iyyar APC ya amince da gudanar da zaben fid da gwani a ranar Asabar 29 ga watan Satumba a jihohi 36 na kuma yankin babban birnin tarayya Abuja FCT.

Shugabannin jam’iyyar sun kuma haramta wa shugabanin jam’iyyar na jihar Adamawa dada kasancewa masu gudanarwa ko masu lura da gudanar da zaben fid da gwani na jihar saboda zargin son kai da suka nuna tun da farko.

Wannan bayani yana kumshe ne a cikin sanarwa da jami’in watsa labaran jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ya bayar wanbda hakan kuma ya kawo karshen rade radin da ake yin a tsarin da za a bi wajen gudanar da zabe fid da gwanin, da kuma hanyoyin da za a yi amfani da shi a zaben da za a gudanar a karshen makon nan.

Cikkaken bayanan tsarin yadda za a gudanar da zaben a dukkan jihohin kasar nan 36 da yankin Abuja ya nuna cewa,  Jihar Abia – ‘yar tinke, Adamawa – ‘yar tinkeAkwa Ibom – Wakilan jam’iyya, Anambra-Wakilan jam’iyya, Bauchi –Wakilan jam’iyya, Bayelsa-Wakilan jam’iyya, Benue – ‘yar tinke, Borno – Wakilan jam’iyya, Kross Ribas – ‘yar tinke, Delta- ‘yar tinke, Ebonyi- Wakilan jam’iyya, Inugu – ‘yar tinke, takardar sanarwa ya kuma nuna cewa, a jihar Edo- ‘yar tinke, Ekiti – ‘yar tinke, Gombe – Wakilan jam’iyya, Imo –Wakilan jam’iyya, Jigawa – ‘yar tinke, Kaduna – Wakilan jam’iyya, Kano – Kato ayan kato, Katsina- Wakilan jam’iyya, Kebbi –Wakilan jam’iyya, Kogi- Wakilan jam’iyya, Kwara- Wakilan jam’iyya, Lagos- Wakilan jam’iyya, Nasarawa – ‘yar tinke, Nija –’yar tinke, Ogun –Wwakilan jam’iyya, Ondo – Wakilan jam’iyya. Bayanan ya kuma nuna cewa, sauran jihohin za su yi amfani da tsari kamar haka, Osun – wakilan jam’iyya, Oyo – wakilan jam’iyya, Filato – wakilan jam’iyya, Ribas – Wakilan jam’iyya, Sokoto – wakilan jam’iya, Taraba – ‘yar tinke, Yobe- wakilan jam’iyya, jihar Zamfara kuma – ‘yar tinke, sai kuma yankin Abuja da za su yi amfani da ‘yar tinkewajen gudanar da zaben fid da gwanin da za a gudanar a yankin gaba daya.

 

 

Exit mobile version