Munkaila Abdullah" />

Zaben Gwamna: Gwamna Badaru Ya Kada Kuri’arsa A Makare

Gwamnan mai ci a jihar Jigawa kuma dan takarar gwamna karkashin tutar jam’iyyar APC, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya jefa kuri’arsa ta zaben gwamna domin sake neman darewa kan karagar mulkin jihar a karo na biyu, amma a makare.

‎Gwamna Badaru ya yi zaben ne da misalin karfe 10:36 maimakon karfe 8:00 kamar yadda a ka yi zato tu da fari a akwatin zabensa mai lamba 003 da ke mazabar Babura Arewa firamare a garin na Babura da ke jihar ta Jigawa.

Haka kuma gwamna ya bayyana gamsuwarsa da yadda a ke gudanar da zaben cikin tsari lafiya da kwanciyar hankali.

Da ya ke bayani kan yanayin fitowar al’umma a zaben kuwa, gwamnan ya ce ba zai iya sanin wannan ba “tunda iyaka mazaba ta kawai na je kuma Alhamdulillah”.

Daga karshe ya yi‎ kira ga al’umma da su fita kwansu da kwarkwata domin jefawa jam’iyyar APC kuri’unsu domin dorewar cigaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Exit mobile version