Khalid Idris Doya" />

Zaben Gwamnoni: APC Na Fuskantar Barazanar Rasa Kujerar Gwamnan Bauci

apc

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Bauchi ta bayyana sakamakon zaben Gwamnan jihar Bauchi da aka fafata a ranar Asabar, inda hukumar ta bayyana cewar jam’iyyar PDP ta darar wa jam’iyyar APC da ke mulkin jihar da kuri’u 4,059 kacal, sai dai ba ta bayyana wanda ya samu nasara ba a sakamakon wasu matsaloli da suka faru na soke zaben wasu mazabu.

Da yake bayyana sakamakon zaben a qakar daren Lahadin nan, wajajen karfe 12:30am, babban jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi, Farfesa Kyari Muhammad mukaddashin shugaban jami’ar Futi da ke Yola, ya bayyana cewar a bisa sakamakon zaben da ya tattara a kananan hukumomi 19 na jihar ta Bauchi jam’iyyar PDP ce ke kan gaba wacce ta samu nasara da kuri’u dubu 469,512, inda yake mai shaida cewar jam’iyyar da ke mulki a jihar ta Bauchi APC kuma ta samu kuri’u 465,453.

Ya ce, sauran jam’iyyun da suka fafata GPN ta samu 2,143 da kuma jam’iyyar PRP mai kuri’u 45,735 kana jam’iyyar NNPP ta samu 31,057, da sauran kananun jam’iyyun da suka fafara.

Farfesa Kyari ya shaida cewar dukkanin kuri’un da aka kada dai sun kai Miliyan 1,048,220, inda ya ce an soke kuri’u dubu 45,312 a bisa dalilai daban-daban, kana ya kuma bayyana cewa kuri’un da aka kada marasa kyau kuma dubu 21,419 ne a fadin jihar.

Farfesa Kyari Muhammad ya bayar da umurnin cewar za a sake gudanar da zaben gwamnan jihar a rumdunar zaben da aka samu korafe-korafen sahihancin zaben kamar kamarar hukumar Tafawa Balewa da sauran wasu ‘yan yankuna kalilan. Ya bayar da mako uku, kwanaki 21 da a sake gudanar da zaben a wadannan rumfunar.

Farfesan ya shaida cewar tazarar da ke gaban jam’iyyar PDP da kuma APC Dubu 4,059 ne

 

Exit mobile version