Muhammad Maitela" />

Zaben Gwamnoni: Yadda A Ka Samu Karancin Fitowa A Borno Da Yobe

An samu karancin fitowar jama’a domin jefa kuri’a a zaben gwamnoni da yan majalisar dokoki a jihohin Borno da Yobe, a binciken da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta gudanar a wasu rumfunan zabe a Maiduguri da Damaturu, musamman idan an kwatamta da zaben shugaban kasa wanda ya gabata; makonni biyu da su ka gabata.
A tattaunawar da wakilinmu da wasu masu jefa kuri’a, a wasu rumfunan zabe a unguwannin Maisandari, Bama Road, Gwange, Bolori tare da Shehuri, duk a cikin birnin Maiduguri, sun bayar da tabbacin hakan tare da bayyana dalilai mabambanta dangane da karancin fitar jama’a zuwa zaben.
Sauran rumfunan zaben, su ne ‘Water Board’, Bindigari, Mairi, Maisandari, Kofar Fada a babban birnin jihar Yobe, Damaturu, inda babu jama’a, kamar yadda wata jami’ar hukumar INEC; Hafsat Sale Umar ta tabbatar.
“Mu na nan tun kimanin karfe 6:00 na safe, amma mutane kadan mu ka tarar, kuma kamar yadda ku ke gani, babu jama’a sosai. Duk da ban san dalilin da ya hana jama’a yin tururuwar fitowa ba, amma dai a bangaren mu, babu wata matsalar da mu ke fuskanta.”
Wanda Abdullahi Musa a mazabar unguwar Gwange, da ke Maiduguri, ya bayyana cewa, “mafi yawan masu zabe sun fi damuwa da zaben shugaban kasa- ta dalilin Buhari; kawai saboda Buhari ya kayar da Atiku,” in ji Abdullahi.
Yayin da shi kuma Bukar Hassan, wanda ya jefa kuri’arsa a mazabar Maisandari a birnin Maiduguri ya ce, “ni a nawa tunani shi ne an samu karancin fitar jama’a ne; sabanin na shugaban kasa, a jihar Borno, a zaben gwamnoni shi ne saboda yadda kowa ya sani kan cewa aikin gama ya gama, “wa ka ke ganin zai iya kara wa da Farfesa Zulum (APC)?”
Yayin da shi kuma Malam Sabo Isa, dan gudun hijira a sansanin Mogolis ya bayyana cewa, “ta ya ya ba za a fuskanci karancin fitar masu jefa kuri’a ba, alhalin kusan duk manyan PDP sun riga sun kaura zuwa APC; yan kwanaki kafin zaben? Wanda kusan duk yan takarar PDPn da a ke sa ran a zaba duk suma sun zubar da makaman su, to wa za a zaba?”
Wanda dangane da hakan ne, kwamishinan hukumar INEC a jihar Yobe, Alhaji Ahmad Makama, a lokacin da ya ke rangadin gani da ido kan yadda zaben ke gudana, ya bayyana wa manema labarai kan cewa, ba za a yi gaggawar yanke hukunci kan yanayin karancin fitowar masu jefa kuri’ar ba- ganin cewa har yanzu safiya ce.
Alhaji Makama ya ce, “wanda a halin da ake ciki yanzu, bai wuce awa guda da fara gudanar da zaben ba, ba za iya yanke hukunci kan karabcin fitowar jama’a ba ko a’a. Amma dai ko ba komai, mu abinda ya dame mu shi ne, zaben zai ci gaba da gudana har zuwa karfe 2:00 na yamma,” in ji shi.
Haka kuma, Makama ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda zaben ke gudana, a cikin tsari da tsanaki, tare da cewa, “wanda babu wani korafin tangardar da muka samu, kuma zaben ya na gudana a cikin tsanaki a dukan rahotanin da ma’aikatan mu suka aiko mana a fadin jihar Yobe”.
Wanda a hannu guda, wakilin (agent) na PDP a wata daya daga rumfar zabe a Damaturu, ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda zaben ke gudana a cikin tsanaki, babu wata hatsaniya- a halin da a ke ciki yanzu.
Haka zalika kuma, har a lokacin kammala wannan rahoton, zabukan sun gudana ba tare da labarin kai wani hari ba a jihohin.

Exit mobile version