Zaben Gwamnonin Imo, Kogi Da Bayelsa: Hukuncin Kotu Da Rikice-rikice Na Matukar Kawo Mana Cikas A Shirye-shiryenmu —INEC
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Gwamnonin Imo, Kogi Da Bayelsa: Hukuncin Kotu Da Rikice-rikice Na Matukar Kawo Mana Cikas A Shirye-shiryenmu —INEC

byYusuf Shuaibu
2 years ago
kOgi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa hukuncin kotu kan ‘yan takara da rikice-rikicen da ke faruwa a jihohin suna matukar kawo mana cikas game da shirye-shiryen hukumar na gudanar da sahihin zabe a ranar 11 ga Nuwambar 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ya bayyana hakan a wani taro tare da jam’iyyun siyasa wanda ya gudana a Abuja.

  • Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
  • Gwamnatin Tinubu Za Ta Muhimmanta Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Da Talabijin – Minista

Ya nuna matukar damuwarsa game da rikice-rikicen da suke tasowa a wadannan jihohi guda uku a tsakanin magoya bayan jam’iyya da ‘yan takara, ya yi gargadin cewa babu yadda za a yi a iya gudanar da sahihin zabe babu cikakken zaman lafiya.

“Sake buga kayayyaki zabe bisa bin umarnin hukuncin kotu cikin kankanin lokaci ba wai tsada ba ne kawai har ma yana shafar ayyukan hukumar. Ko da yake hukumar ta riga ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar jihohin uku, amma umarnin kotu guda hudu da ya tilasta mana sake duba jerin sunayen.

“Wadannan canje-canjen sun bayyana a cikin sabunta jerin jam’iyyu da ‘yan takara a shafinmu na sada zumunta. Daukar wannan hukuncin ba tare da la’akari da abin da zai janyo ya shafi hukumar da ‘yan takarar ko jam’iyyunsu.

“Yayin da yakin neman zabe ke ci gaba da dagula lamura, hukumar ta sake jaddada damuwarta game da yawaitar tashe-tashen hankula a jihohin uku da suka hada da jam’iyyu da ‘yan takara. Ina so in tunatar da ku a matsayinku na shugabannin jam’iyya cewa zabuka na gaskiya da adalci ba zai yiwu ba sai cikin yanayi na zaman lafiya,” in ji Yakubu.

Shugaban INEC ya ce zaben wani tsari ne da ya kunshi Bil’adama a matsayin masu jefa kuri’a, masu sa ido da kuma kafafen yada labarai wadanda tsaron lafiyarsu ya shafi hukumar.

Yakubu ya ce zabukan a jihohin guda uku yana da matukar rudani a wajen gudanarwa.

Ya kara da cewa a daidai lokacin da ya rage makwanni biyu kacal a gudanar da zaben, INEC na gab da kammala shirye-shiryenta kuma wannan shi ne karo na farko da hukumar za ta gudanar da zabukan gwamnoni guda uku a lokaci guda a yankuna daban-daban.

“Hakan zai yiwu ne a daidai lokacin da masu rike da mukaman suke cika wa’adin mulkisu wanda bai wuce kwanaki 150 ba ko kuma bayan kwanaki 30 kafin cikar wa’adin mulkinsu a gudanar da zabe kamar yadda sashe na 178 (2) na kunkundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 ya tanada,” in ji shi.

Da yake mayar da martani a madadin jam’iyyun siyasar da suka yi rajista, shugaban kungiyar IPAC, Injiniya Yabagi Sani, ya ce domin tabbatar da amincewar ‘yan kasa, dole ne INEC ta ci gaba da nuna rashin son kai da gaskiya da kuma jajircewa wajen gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci.

Ya kuma bukaci INEC da ta yi aiki tukuru tare da hada kai da jami’an tsaro wajen dakile matsalar tsaro da ‘yan siyasa masu daukar siyasa a mutu ko a yi rai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
Tambarin Dimokuradiyya

ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

October 3, 2025
Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar
Tambarin Dimokuradiyya

Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar

October 3, 2025
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan
Tambarin Dimokuradiyya

Lalacewar Tsarin Zabe Babbar Barazana Ce Ga Dorewar Dimokuradiyyar Afirka — Jonathan

September 27, 2025
Next Post
Manyan Ayyukan Da Ke Gaban Sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya

Tsarin Canji Na Bai-daya Hanya Ce Ta Tsaftace Kasuwar Shinku

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version