Zaben Gwarzon Littafi Na Shekarar 2018

Kamar yadda ya zama sunnar rayuwarmu a karshen kowacce shekara. ‘yan jaridu kan yi waiwayen baya don yin bita da fashin baki kan abubuwan da suka faru a cikin shekarar masu dadi da ma maras dadin nasu.

Kamfanoni da bankuna kuma su hau kididdigar abubuwan da suka shiga da wadanda suka fita don tantance ribar da aka samu a shekarar ko akasin haka. Haka kungiyoyi da hukumomi kuma ke bayar da kambun girmamawa ga zakwakuran mutane da suka bayar da wata muhimmiyar gudummawa ko suka yi wani babban abun a yaba wanda tarihi ba zai manta da shi ba. Yayin da kuma za a ga masu ta’ammali da kafafan sadarwa na zamani suna ta yin rubuce-rubuce, a ciki suna fadin gwarzayensu na wannan shekarar da kuma dalilan da ya sa suka zabe su.

To, hakan ta sa wannan jaridar taku mai farin jini da tarin albarka wato LEADERSHIP A YAU LAHADI ita ma ta ba ku dama domin fadar ra’ayoyinku na gwarzon littafi a wannan shekara ta 2018 da kwana Daya da yini Daya ne suka yi mana saura mu yi sallama da ita. Ga dai sakonnin ra’ayoyin naku wanda wakilinmu Adamu Yusuf Indabo ya tattara mana.

 

Salam. Ina cikin matsananciyar farin ciki a lokacin da zan gaya maku ni Hajara na mikawa littafin ‘A Mafarkina’ Kuri’ata na 2018, wanda Fatima Dan Borno ta rubuta. Littafin ya fadakar ya ilmantar babban abun burgewa a labarin ya nuna mahimmancin hakuri da kuma yarda da kaddara. Duk da Khairat ta tsinci kanta a cikin matsala ta rashin dangi, da kuma rayuwar daji haka baisa ta sabawa Mahaliccinta wajen butulce masa ba. Nagode

Daga Zaidu Ibrahim Barmo (MrZaid) Jibia, Katsina, Nigeria 08033002473. Littafin Gwanin Na Iya Na Maimuna Idris Sani Beli shine ya kamata ya zama Gwarzon shekarar 2018. Dalilaina kuwa su ne; Yadda littafin ya fadakar tare da hannunka mai sanda akan wasu azzaluman jama’a. Sannan ya nuna mana muhimmancin jajircewa akan abinda kake so kamar yadda Gwani yayi. Sannan ya ceto Khadija daga fadawa halaka ta hanyar auren kishin wuta. Hakurin Asma’u abin koyi ne ga Mata da ma Maza baki daya, yadda tayi hakuri da sadaukarwa har ta samu Gwani. Da sauran abubuwa da yawa da littafin ya kunso.

 

Amincin Allah ya tabbata a gareku leadership Hausa. Muna jin dadin shirye-shiryenku suna kayatar da mu sosai, mun kuma ji dadin wannan sabon shirin da kuka kawo na zaban gwarzon littafi. A gaskiya naso da ni wata me kudi ce da Fatima Dan Borno zan ba award na karramawa. Na zabi littafin ‘A Mafarkina’ a matsayin gwarzon shekara. Dalilina da yasa nace A mafarkina saboda littafin ya fadakar da mu ya nishadantar ya kuma ilmantar. Ina mika sakon jinjina agun marubuciyar yar mutan Borno.

 

Fulani Hafsat, Potiskum Jihar Yobe

Littafin A Mafarkina na Fatima Danbarno, shi na zaba gwarzon wannan shekara ta 2018. Hujjata ta zabar sa shi ne, littafin ya kayatar da ni, ya wa’azantar kuma ya nishadantar. Hakika Fatima Danbarno ta yi kokari wajen tsara labarin.

Halima Muhammad Hassan, CH 19A Maccido Dalhatu Road S/Gari Sutun Wada Kaduna. Ni littafin Keta Haddi na Asma’u Lamido ne gwarzon shekarata, saboda littafi ne mai matukar ma’ana musamman a cikin rayuwar da muke ciki a yau. Kodayake ba abun mamaki ba ne in mu kai duba ga yadda ta fi karkata gun tunatar da mu a kan abun da ya shafe mu a yau. Kuma wannan littafin zai iya tafiya daidai da kowanne zamani saboda abun da ta karantar a ciki. Da fatan Allah ya kara mata basira da hazaka ta kawo mana wadanda suka fi wannan.

 

Na zabi littafin A Mafarkina na Marubuciya Fatima Danborno a matsayin gwarzon shekarana. Tayi amfani da hikima da ilmi wajen rubuta shi wanda yake matukar ilmantar da mata akan illan zuwa gidan bokaye.

 

Salam. Barkanku da war haka ma’aikatan wan nan jarida mai farinjini. A rayina gaskiya littafin da yafi cancanta ya dau gwarzon shekara shi ne littafin Hajiya Habiba Abubakar Imam,saboda a gaskiya littafin yana dauke da darussa da yawa acikinsa,littafin MUSABBABI,yana nuni da yadda mutanen yau suka sakaki wurin dogaro ga Allah Wanda ta dalilin rashin dogaro ga Allah ke jawo wa mutum tsalle daya mai jefa mutum rijiya,musabbabin rashin dogaro ga Allah ya sanya Musadik fadawa tarkon da  aka dora masa laifin kisan uwar dakinsa, inda saida kyar ya sha da taimakon Allah ya fita halin wan nan tarko,haka matar ubansa Hajiya Kilishi, ita kuma akan abin duniya ta yassarar da imaninta ta shiga ta hita ta wulakanta rayuwar Musadik, wanda duk idan muka yi duba da littafin yana magane ne a kan yanda mutanen wannan zamanin su ka zama shiyasa masifu sukayi mana yawa acikin duniyar nan tamu, rashin dogaro ga Allah ka ce dole sai ka lalata ma wani rayuwa saboda abinduniya, wannan sune manyan hujjojin da littafin ya kunsa duk da ba iyakarsu kenan ba amma dai duk wanda zai duba littafin to zai fahimci wadannan hujjojin. Mun gode Allah ya kara ma wannan jarida farin jini da daukaka.

 

Gwarzon littafina a 2018 shine GWANIN NA IYA Wanda Maimuna Idris Sani Beli ta wallafa. Na zabi littafin ne saboda dalilai kamar haka:

1-Labarin yana da jigon dake rike mai karatu daga farko har karshe ta yanda ba zaka so rasa ko kalma daya daga labarin ba.

2:marubuciyar ta yi kokarin yin bincike kafin tayi rubutun,bata gina labarinta a doron zato ba.

3: Hausar da aka yi amfani da ita a littafin abar birgewace.

4: Marubuciyar bata yi karyar kudi,mota,ko gidaje kamar yanda aka saba gani a litattafan wannan zaman,wannan tasa mai karatu zai ji abin tamkar akanshi ko a kusa dashi yake faruwa.

5: An kula da ka’idodin rubutu kuma aikin littafin ya inganta daidai gwargwado.

 

Salam LEADERSHIP A YAU LAHADI. Na ga shafinku yana tambayar gwarzuwar shekara, ni ma na dauki lambarku ne in gaya maku ni Fatima Ibrahim Garba Dan Borno ce gwarzuwata a cikin littafinta na ‘A Mafarkina’.Littafin ya fadakar ya kuma sake sa mun rauni a zuciyata har na ji ba zan iya yin halin Fauza ba, babu Wanda ya zaci ita zata iya aikata haka. Daga karshe a aika min jinjinta a gare ta don muna kukan rashin samunta a waya. Na gode.

 

Na zabi littafin A mafarkina a matsayin Gwarzon shekara. Wanda gwarzuwar marubuciyar nan ta yi Fatima Ibrahim Garba (Dan Borno) Saboda yadda littafin ya fadakar da mu illar cin amana, haka kuma salon rubutun ya bambanta da sauran littafai. Ana so idan za a karanta littafi a dinga ji kaman ana kallo ne a gaske, haka marubuciyar ta yi amfani da salonta a wajen rubuta A Mafarkina.

 

Na zabi A Mafarkina na Fatima Dan Borno a matsayin gwarzon shekarata, don bana wuce karanta littafanta. Dalilaina saboda littafin idan ka karanta sai ka tausayawa halin tashin hankalin da Khairat ta tsinci kanta. Fauza kuwa ta nuna halin butulci ta yi mana bazata. Har kullum mu na kara jinjinawa kaifin alkalami irin na FATIMA Dan Borno, ta nuna mana illar cin amana da a yanzu shi ya fi komai yawa a duniyar nan.

 

Salam LEADERSHIP A YAU LAHADI. Ni Bahijja Lukman na zabi littafin Keta Haddi na Asma’u Lamido a matsayin gwarzon littafi na wannan shekara, saboda littafi da ya zo da salo mai daukar hankali, kuma ya tabo wata babbar matsala da ta addabi al’umma, wanda lungu da sako birni da kauye kowa yana kuka da wannan babbar matsala ta fyade ga kananun yara.

 

Na zabi littafin ‘A Mafarkina’ na Fatima Dan Borno a matsayin gwarzona. Littafin ya nishadantar ya nuna mana karfin zumunci da kuma Amana. Na dauki halin Khairat a labarin na watsar da halin Fauza da Sauda.

 

Maimunatu Yusuf Tijjana, Jihar Kano

Salam LEADERSHIP A YAU LAHADI. Gaskiya mun ji dadin wannan dama da kuka ba mu na fadar ra’ayinmu na Gwarzon Littafin Shekara 2018. To ni dai ‘Gwanin na iya’ na takwarata Maimuna Idris Sani Beli ne zabina. Saboda da ma can takwarata gwanar azancin zance ce da kuma tarin hikimomi. Sannan kyawawan halayen Gwani abun burgewa ne wadanda kaddarar rayuwa take son sakaye su da karfin tsiya. Kuma ga shi mai tsananin kulawa da son iyalinsa, domin Gwani ya hakura da duk wani farin ciki da jin dadinsa don tabbatar da martaba da farin cikin yalinsa.

 

Aisha Humaira Daga Unguwar Dosa  Kaduna

Na zabi littafin ‘A Mafarkina’ a matsayin gwarzon shekara. Dalilina littafin ya fita daban a cikin irin littafan da muka saba karantawa. Littafin yana kara jadadda mana abincin wani gubar wani. Ba Lalle abinda ya burge ka ya burge waninka ba. Littafin ya nuna mana illar saurin rantsuwa ko kuma ka nunawa duniya kai ka isa bayan ka mance duk isarka Allah ya fika zai kuma iya juya maka tunaninka. Na kasance mace me yawan rantsuwa a dalilin littafin nan ya sa na ji ni ma ina son canza hali irin na Adam me hani da saurin rantsuwa. Nagode. Littafin Fatima Dan Borno ta rubuta, a kuma roke ta ta dinga barin waya a kunne kuma ta dinga dagawa dan muna kaunarta.

 

Hafsat Maman Ilham Daga Kaduna

Na Zabi littafin A Mafarkina na Fatima Dan Borno a matsayin gwarzon ankara. Dalilaina saboda cin amanar da akayi wa Khairat don kawai saboda son zuciya a cilla ta daji ga tsohon ciki. Wannan rashin imani ya yi yawa. Marubuciyar ta yi amfani da salo irin wanda har aka gama littafin ba mu so muka ajiye ba. Jinjina ga Fatima Dan Borno.

 

Mu tara a sati mai zuwa don jin ragowar ra’ayoyin naku da kuma fitar da sakamako.

 

Exit mobile version