Umar A Hunkuyi" />

Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kaduna: Gaskiyan Abin Da Ya Faru A Kajuru –Stingo Minista

Danlami Stingo Usman, shine dan takarar neman shugabancin Karamar hukumar Kajuru a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, ya yi wa wakilinmu bayanin hakikanin abin da su suka ga ya faru a karamar hukumar na su dangane da zaben kananan hukumomin da ya gudana ranar 12 ga watan Mayu 2018,  a dukkanin fadin Jihar ta Kaduna. Ya yi wadannan bayanan ne washegarin ranar da hukumar zabe mai zaman kanta ta shelanta cewa, ta rushe zaben da aka yi a karamar hukumar ta Kajuru tare da wasu kananan hukumomin hudu, inda kuma ta sanar da cewa, za a sake zaben a ranar 2 ga watan Yuni 2018. Ga abin da Stingo, ke cewa kan yadda suka ga zaben ya gudana:

Karamar Hukumar Kajuru tana da mazabu guda 10, cikin kuma mazabu goman nan akwai akwatuna 15. A wannan rana ta 12 ga watan Mayu, an yi zabe a Kajuru, a wadannan akwatunan guda 153, sai dai kadan wadanda na’urar zaben ba ta yi aiki ba. amma dai gabakidaya za mu ce an yi zabe lami lafiya, ba fada ba rigima a dukkanin akwatunan nan guda 153, domin ko bayan zabe da muka tattauna da babban Jami’in ‘Yan Sanda na Karamar Hukumar ta Kajuru, ya nu na mana jin dadin sa, yana mai cewa ya ji dadin yadda zaben ya gudana, domin a duk wuraren da aka gudanar da zaben nan ba inda aka kawo masa rahoton an yi wata rigima ko kuma an sami cikas ba a gudanar da zaben ba.

Ma’aikatan zabe kuma duk sun bayar da hadin kai a akwatuna, don ba mu sami inda aka ce an hana wani ko wasu kada kuri’arsu ba bayan kuma duk sun cika ka’idodjin kada kuri’ar na su. Ba mu kuma ji abokanan hamayyar mu su ma sun koka a kan hakan ba. wannan alama ne da ya nu na an yi zabe an kuma gama lami lafiya. Kila sai dai abin da ba a kan rasa ba bayan an gama zabe.

Sai dai mu a karamar hukumar Kajuru mun sami damuwa matuka, domin da rana wasu suna cikin zabuka, wasu ma sun kammala za su dauki akwatuna su kai rahoton zaben a mazabu, sai ga wani Jami’in gwamnatin Jiha ya zo ya shiga Ofishin zabe na karamar hukuma ya yi taro tare da shi Jami’in zabe na karamar hukumar da Kantoma na karamar hukumar gami da wani daga cikin shugabannin Jami’an tsaron yankin. To bayan wannan taron ne da suka yi, aka sami matsala a karamar hukumar Kajuru, aka gayyaci wasu jami’an zaben na mazabu wajen, inda daga nan ne wasun su tunda suka tafi ba su sake dawowa ba. jama’a kuma tun da an fara kawo rahotannin sakamakon zaben sai suka tsaya a wajen ba su sake barin wajen ba.

A ranar zabe an karbi sakamakon zabe na mazabu shida, da suka hada da mazaba ta Maru, Idom, Kufana, Rimau, Kasuwar magani, da Kajuru. Ranar litinin kuma aka karbi rahoton sakamakon zaben mazabar Kalla. Inda shi jami’in hukumar zaben na wannan mazabar bayan ya fara bayar da sakamakon zaben, sai ya fita kamar zai je ya yi fitsari, daganan sai ya sullube ba a kara ganin shi ba. Da jami’an tsaro da wadanda suka gudanar da zaben a akwatunan da ita kanta Jami’ar da ta yi aikin zagayawa tana duba yanda zaben ke gudana, duk sun zauna sun kwana a wajen sun ma wuni washegarin ranar Lahadi a wajen, ba su ta fi ko’ina ba. Dan Majalisarmu a Majalisar Jihar Kaduna,  Honorabul Dika Sambo, daga wannan mazabar ta Kalla ya fito, nan duk suka kwana har ranar Litinin. Sai a ranar Litinin din ne babban Jami’in ‘Yan Sanda ya shirya aka je aka sanya ita mai duba zaben na wannan mazabar aka ba ta dama sannan ta fadi sakamakon zaben na wannan mazabar ta Kalla.

Ranar 12 ga watan na Mayu da aka gudanar da zaben an sami matsala a mazabu guda uku, mazaba ta Tanta Two, jami’in zaben gabadaya bai ma leka mazabar ba, an je an gama zabe a akwatuna an dawo an hadu duka, amma ba wanda zai karbi sakamakon zabe. a mazabar Buda, shi jam’in hukumar zaben yana cikin harhada sakamakon zaben kwatsam, sai ga Sojoji a mota suka fara harbin Iska, suka kwashi shi kan shi jami’in hukumar zaben da takardunsa gabadaya, wannan bayan ya gama karban sakamakon zaben ne duka yana shigar da su ne a cikin takardun bayanan da aka tanada. Aka kwashe shi gabadaya da takardun aka wuce da shi Kajuru, nan fa jama’an da suka kada kuri’un suka bi shi, aka je can amma ba a saurare su ba. hakanan ma ya kasance a mazabar Afogo, tamkar dai abin da ya faru da na mazabar Tanta.

Wannan shi ne dalilin da ya sanya ba a sami sanar da sakamakon zabe a wadannan mazabun guda uku ba. amma mu a Jam’iyyance, tun da an rigaya an kammala zaben a wadannan mazabun duka an kuma baiwa kowane wakilin Jam’iyya da wakilan jami’an tsaro kwafi-kwafi na sakamakon zaben, to sune muka mora muka harhada muka samu tabbacin mun ci zabe a mazabu guda tara, domin muna da Kansiloli guda tara wadanda PDP ta ci a wannan karamar hukuma ta Kajuru, guda daya ne na Kajuru, wanda muka san PDP ba ta samu ba.

To daga baya abin da yake bamu mamaki shi ne, aka je karamar hukuma domin a tattara sakamakon nan bakidayansa a bayar da sanarwa, sai aka taras babu jami’in zaben hukumar zaben na karamar hukuma. Ba a gan shi ba, hatta Kantoman karamar hukumar, Alhaji Aminu Rabi’u Zangon Aya, wanda ya baiwa kowa mamaki kasantuwar a ce dattijo kamar shi, amma ana zama sai ya shiga motar shi ya yi tafiyar sa ya bar Jama’a. Da ba a gansu ba gabadaya, nan jama’a suka yini a ranarAsabar nan aka wayi gari ana jiran sa ya zo ya karbi rahoton sakamakon zabe ba a gan shi ba. Haka dai al’ummar Kajuru da suka kada kuri’a suka yini nan suka kwana suka wayi gari suka sake yini suka sake kwana, haka ya zama Litinin, Talata, Laraba, haka ya zama Alhamis, sai a ranar Alhamis da dare ne muka sami labarin cewa wai ita shugabar hukumar zaben na Jiha, Dakta Saratu Dikko, ta sanar da cewa, zaben Kajuru, ba a sami sakamako ba, don ba a sanar ba, don haka za a sake yin zaben ranar 2 ga watan Yuni.

To mu a matsayinmu na masu son zaman lafiya, sanin kowa ne cewa a ‘yan watannin baya an sami wani tashin hankalin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi, don haka muna gujewa duk wani abin da zai sake tayar da jijiyan wuya ya kawo wani rudamin. Sai muka fahimci cewa, ita hukumar zaben ne da kanta take neman ta haddasa mana fitina a karamar hukumar Kajuru. Don a sake zubar da jini a ce ba ma son zaman lafiya ne. In kuwa ba hakan ba, ta ya za a ce an kammala zabe an kuma bayar da sakamako a mazabu bakwai har jami’an zaben mazabun bakwai sun baiwa Kansiloli bakwai takardun shaidar cin zaben su, sai kuma a ce ba a turo mana wanda zai zo ya karbi sakamakon zaben nan na karshe a shalkwatar karamar hukuma ba, sai mu ji kawai wai an soke zabe za a kuma yin wani zaben.

Ba tsoron zaben muke yi ba, domin muna da tabbacin ko da za a sake yin zaben sau goma, kowa ya san karamar hukumar Kajuru, gida ne na Jam’iyyar PDP. Amma domin a haddasa mana fitina, hukumar zabe tana neman ta kawo mana matsala da kanta.

Idan har hukumar zaben ba ta zo ta kirga kuri’u ta bayyana sakamakon zaben ba, ta kafe da cewar za ta sake gudanar da zaben ne, to ina kira ga jama’a da ka da su gajiya su fito kamar yadda suka fito a baya ko da kuwa sau nawa ne, domin an ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya.

Exit mobile version